← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 106

Sashe 42

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu muryoyi ta ji sun sallama a gadarance, muryar É—aya ta so ta san mai ita sai dai bata gama tantancewa ba, sai kawai ta jiyo muryar Nasir yana faÉ—in

"Haba ku da gidanku, sai wani rafka sallama kuke yi kamar baƙi"

Wata murya ta jiyo ta ce

"Gaskiya dai ai gidanta ne kuma gidan yayanta abu ne ya haÉ—e mata biyu" Duk wannan maganar da suke kafin su shigo tsakar gidan ne wato daga zauren gidan, kafin ta gama dawowa daga shan ruwan mamakin maganganunsu ta yi saurin amsa sallamar tana fitowa daga falon nata.

Hakan ya yi daidai da shigowarsu tsakar gidan suka yi ido huɗu da Sadiya wacce shigar da ta yi ta ɗauki hankalinsu ganinta tsaf tamkar ita ce amaryar ta yi ƙiba abinta kamar bata da wata damuwa, don dama ita damuwa sai idan mutum ya buɗe cikinsa ake sanin yana da ita duk da a lokuta da dama tana iya bayyana kanta a gangar jikin mutum.

Ba ma wannan ne ya ɗan taɓa musu zuciya ba, yadda cikin jikinta ya mata cif-cif shi ne abin da ya ɓatawa Meenal rai, a take ta ji wani kishi ya baibaye mata zuciya tana jin tamkar ta maƙure Sadiyar ita bata ma san tana son Nasir haka ba sai da ta ji kishin Sadiya ya tokare mata maƙoshi ya ƙi gaba kuma ya ƙi baya!. Basu kaɗai lamarin Sadiya ya tafi da su ba hatta Nasir ta shammace shi, saboda kayan jikinta bai taɓa ganinta dansu ba sabbi ne, da ta saya wajen maman afrah don tana siyar da set ɗin plazzo na yara da manya sannan tana siyar da iya wandon plazzo ɗin. Ba wai don bata yin kwalliya ba sai dai don ɗinkin ya fita ne yadda wandon ya baje sosai ya ƙara mata kyau rigar kuma cif kamar don ita kaɗai aka ƙirƙire ta.
Sadiya ganin su Meenal ya taɓa mata zuciya a nata ganin ba ƙaramin cin fuska ba ne namiji ya shigowa da mace matarsa da zai aura, kuma bai sanar da ita ba sai dai kawai ta gansu sun shigo, duk da cewar Babarsa da Babar Meenal ƙawaye ne amma ai ya kamata a ce an sanar da ita, kai ita gaba ɗaya ma bata ga alfanun hkan ba domin mai suke ci na baka na zuba ai in dai gida ne kamar yau ne za ta shigo shi, tun da yanzu biki bai fi sati uku ba kuma an kammala mata komai na ɓangarenta. Sadiya bata so su ga lagwanta daga su har Nasir ɗin don haka sai ta ƙirƙiri bariki kamar yadda su ma suka mata bariki cikin wani salon murya ta ce

"Oyoyo baby sannunka da zuwa, kenan dama ba sai an yi sallar magribar za ku zo ba, ka ce mini sai an yi sallar magriba za ka kawo su?" Ta faɗa tana wani rausaya kai gefe tare da yin fari da ido, mamaki al'ajabi ne ya kama kowane ɗayansu, musamman Nasir da hakan ya fi kasancewa baƙon abu a wajensa hakan ya sa ya saki baki galala yana bin ta da kallo. Meenal kuwa wani takaici ne ya turnuƙe ta tana jin tamkar ta kurma ihu tana ganin Sadiya bata isa ba bare ta kai har Nasir ya yi wata magana da ita musamman yadda ƙannensa suke sanar mata ita ba komai ba ce a cikin gidan, amma yanzu gashi ta ga akain haka, don bata taɓa tunanin Nasir zai sanar da Sadiyar zuwanta ba, ta so a ce Sadiyar bata san da zuwanta ba domin ta ƙona mata rai sai gashi sun samu saɓanin abin da suke zato, wato ma yadda ta so ta ɓatawa Sadiya rai na zuwanta gidan sai gashi ta ga ko a jikin Sadiyar wai an tsikari kakkausa.
Maganar Sadiya ce ta katse su da faÉ—in
"Sannunku da zuwa amarya bakya laifi" Wani irin haɗe rai Meenal ta yi ita kuma ƙawarta ta ɗauke kai tamkar ta ga kashi tun da sun gama shiryo yadda za su ƙular da Sadiya ta yadda abin zai tsaye mata a rai har ya hanata sukuni. Shi kuma Nasir sai ya tsinci kansa da faɗin
"Eh dama yanzu ne za su zo" Shi kansa vai san dalilinsa na faÉ—in hakan ba tun da ya san basu yi maganar da Sadiyar ba. Murmushi Sadiya ta yi ta ce
"To ai ita da gidanta ma za ta iya zuwa koyaushe duk da dai ba a kawo ta ba" Kallon kallo aka shiga tsakanin Meenal da ƙawarta Meenal a zuciyarta tana rayawa a ranta cewa dole idan ta shigo gidan nan Sadiya ta faɗawa aya zaƙinta.
A hankali ta fara wani taku tana jijjiga jiki yadda za ta ɗauki hankalin Naair ɗin ta yadda zai shagala da kallonta har Sadiya abin ya bata haushi sai dai aka samu akasi shi kawai sai ya ji kamar wanda aka jarabce shi da kallon Sadiya kawai ji ya yi tamkar an sanya maganaɗisu a tsakaninsu wani abu yake ji yana fusgashi dangane da ita. Ƙawar Meenal ta ja wani gajeran tsaki ta kama hanyar ɓangaren Meenal ɗin kamar yadda ta ga Meenal ta yi sallamar wani yaro ya katsewa kowa hanzari inda ya ce a bashi farin mai na dubu biyu da ɗari biyu, kasancewar a ƙulle suke a wajen sannan kuma gashi kuɗin nasa ba canji banne dubu biyun ce da ɗari biyun sai Sadiya ta ce

"Ɗan yi haƙuri ka ji ka zo a daidai lokacin da zan nunawa ƙanwata ɗakinta, bari in zo in baka" Shi kuma Ibrahim jin wannan furucin sai ya ce
"Bari in bashi" Ya faɗa yana nufar wajen zai ɗakko masa man, shi ya yi hakan nr don ya birge su Meenal su ga kamar dai ba ya wulaƙanta matarsa saboda ya san an ce wasu matan sun tsani namiji mai wulakanta matarsa ya gida, saboda suna ganin su ma wataran idan sun shigo gidan zai musu hakan. Da to ta amsa masa ta fara bin bayansu don lokacin Meenal har ta murɗa ƙofar za ta buɗe, zuwan Sadiya ya sa ta dakata da abin da take a ƙufule ta ce

"Ba ma buƙatar taimakon ki" Sadiya sai ta saki murmushi ta ce
"Ayya!. Dama don an ce baƙon ka annabinka amma tun da haka ne babu damuwa s fito lafiya" Nuna rashin damuwa a kan lamarin abin da ta faɗawa Sadiya ya sa ta ƙara jin zafi a ranta, ita kuma Sadiya ta juya ta koma lokacin har Nasir ya ɗakko man yana nuna mata cewa wannan ne? Su dama tsabar ma ransu da ya ɓaci suna shiga suka fito na farko dai yanayin yadda suka samu akasin yadda suka yi zato daga matar gidan da kuma yanayin ginin da aka yi sai ta ji bai wani kwanta mata ba tun da lamarinta akwai ƙarya a ciki, haka ya sa suka fito buguzum-buguzum Sadiya kuma da ta bashi amsa da shi ne man sai ta je za ta karɓa ta tsaya dab da shi wani ƙamshin turarenta ya buge shi, bai san lokacin da ya yi murmushi ba ita kanta Sadiyar abin ya bata mamaki sai dai sakin murmushin da ya yi a kan idanun Meenal wacce ta ƙara cin karo da haɗuwar hannayen Sadiya da Nasir a daidai lokacin da zai bata man, ko kallo basu ishi su Meenal ba sannan ta yi da na sanin zuwanta gidan, don tana ganin cin fuska Nasir ya mata da gangan. Hanyar waje suka nufa, Nasir ya shiga kiransu amma ko waiwaye babu wacce ta yi a cikinsu.

Bao bi ta kan Sadiya ba wacce ta karɓi man ta ba yaron a take ya takewa su Meenal baya yana faman rafka musu kira, yaron ma fita ya yi Sadiya a fili ta ce

"Ku kuka sani ku ƙare ƙalaw" Ta faɗa tana mai shigewa ɗaki hannunta riƙe da kuɗi.
Su Meenal ko kallon inda motar Nasi take basu yi ba, haka suka fara tafiya kamar za su tashi sama, Meenal ta ce

"Wai ni Nasir zai yi wa barikanci,saboda na ce zan je in ga ɗakina saboda tsare -tsaren kayan da za a saka a ciki shi ne har zai ke kula matarsa da ya san yana son ta uban wa ya ce ya ce zai aure ni?" Ta faɗa tana yin ƙwafa tare da raya cewa zai san ya yi da ƴar halak. Ƙawarta Huzaifa ta ce

"Wai baki ga har wani yauƙi take ba, yanzu wannan matar ce za a ce tana fuskantar wulaƙancin ɗa namiji anya ba rufarki aka yi ba?" Ran Meenal ne ya ƙara ɓaci tana cin wani alwashi a kan komai kamar ta yi kuka ta ce

"Abin ya zo da rainin wayo, wai ni ba ma wannan ba sana'a take yi fa da alama kina gani ana sayen mai, ni da babu uwar da nake siyarwa kuma wallahi ba zan siyar ba amma zan É—auki mataki bari na shiga gidan, ai duk wanda ya iya allonsa wankewa yake yi" Huzaifa ta shiga zuga ta tana ta jin kanta dole ta yi wani abu duba da yadda shi ma Nasir ta ga yana yi wa Sadiya wani kallo tamkar bai san da su ba a wajen.

Nasir tun da ya fito ya hangi sun kama hanya sun tafi, daga haka ya gane akwai gagarumar matsala, hakan ya sa ya fara sauri ya take musu baya, yana tunanin abin da ya musu don shi kansa ya sha'afa da yadda ya mu'amalanci Sadiya a gabansu. Yana binsu yana magaiyar su tsaya amma basu saurare shi ba suka ba banza ajiyarsa. Yana dab da ƙarasowa da yake sauri suke kamar su tashi sama, kawai sai gani ya yi sun tsare mai napep, sun shiga da ɗan gudunsa ya taho sai dai kafin ya zo mai napep ɗin ya tada sun tafi, ya san kuwa hakan ba ya rasa nasa ba cewa umarni su Meenal ɗin suka baiwa mai napep ɗin.
Chapter 42 · 0% Book details