← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 106

Sashe 32

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare Ibrahim ya zo wajen Jidda bayan ta fita sun gaisa suna ɗan tattaunawa tana zaune kan wani dakali da yake daga can ƙofar gidan shi kuma yana tsaye ta jingina da jikin motarsa, hira suke cikin natsuwa da kwanciyar hankali, tsaftatacciyar hira ba irin hirar da wasu ƴanmata da samarin zamani suke yi ba wacce hira ce da ta saɓawa addini da kuma al'ada, wanda yawanci wasu samari da ƴanmatan sun ɗauki hakan a matsayin wayewa, bayan ba wayewa ba ce jahilci ne da rashin tsoron Allah da kuma tuna makoma.

Hira da taɓa jikin juna, ko hirar marar kyaun sauraro, gabaɗaya ya saɓa addini sannan daga ke har shi ba za ku yi daraja a idanun junanku ba sannan ko da Allah ya yi kun yi aure za kuke zama da zargi!.

Cikin hirar tasu ne Ibrahim ya ce

"Jiddanah!" Murmushi ta yi ta É—ago tana kallonsa ta ce

"Na'am" Ya ce

"Ina so na miki wata tambaya amma ina jin nauyi" Ta ɗan yi shiru tana jin babu daɗi a ranta don ta yi tunanin ko magana zai mata a kan lamarin Aliya sai da ta ɗan ɗaure fuska don ita bata son wai don za ta auri namiji ko kuma bayan ta aure shi, ta tsaya yake sanin sirrin gidansu ko kuma yake faɗawa wasu daga danginta magana ba za ta lamunci hakan ba, ko yaya naka-nake ne sannan duk daren daɗewa ana iya sauya miji amma ɗan uwa ba a sauya shi, don haka duk yadda nake yake to naka ne idan ka ba namijin ƙofar ya san sirrin gidanku to tabbas wataran gori ko wulaƙanci zai iya biyo baya idan ma hakan bai samu ba babu wani alfanu ga mace take kwashe sirrin gidansu tana faɗawa miji.

Ta É—an sauke ajiyar zuciya ta ce

"Ka faÉ—a in har da sarari zan faÉ—a maka" Ya hurar da iska daga bakinsa ya ce

"Kawai idan ba damuwa ne ina son sanin tarihinki ma'ana ina son sanin asalin labarinki na san mahaifanki sun rasu amma bayan haka ban san komai ba, kuma ba don wai wani abu ba kawai dai ina son sani" Sai da ta kalle shi sannan ta mayar da idanunta tana kallon ƙasa ta ce

"Sunana Hauwa ana kirana da Jidda, mahaifina ɗan asalin ƙasar Niger ne a wani gari da ake kira Doso, mahaifina saboda halin babu da kuma wasu matsalolin wanda yarinta bata bari na san su ba kasancewar lokacin shekarata goma. Wannan dalilan ne suka saka ya baro ƙasarshi ya dawo Nigeri'a , lokacin da ya zo ya dira a garin Kano bai san kowa ba cikin ikon Allah suka haɗu da Abba ya taimaka masa, ka ga wancan gidan shi ne gidan da muka zauna da mahaifana a ciki muka rayu" Ta faɗa tana nuba masa wani gida da yake kallon gidan Abba, wanda gidan yanzu a rufe ma yake babu kowa a ciki, waiwayawa ya yi ya kalli gidan kafin ya juyo yana kallonta ganin idanunta sun cika da ruwa, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ɗora da faɗin

"A kwana a tashi abota mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu don Allah har kasuwa tare suke zuwa da mahaifina Malam Abdullahi, koyaushe mahaifina yana faɗawa mahaifiyata girma da darajar Abba a wajensa a ganinsa ba kowane mutum nr zai nuna karamci kamar yadda Abba ya nuna masa ba, abotarsu ta saka ƙawance mai ƙarfi ahiga tsakanina da Aliya, koyaushe muna tare muna son junansu sanann mahaifanmu mata ma basa nuna mana bambanci gidanmu tamkar gidansu Aliya haka nima. sai dai ita Umma bata ƙawance da mahaifiyata sai dai in an haɗu a gaisa ko wani dalili mai ƙarfi" Ta faɗi hakan tana jan hanci da alama dai akwai wani abu da take kusa zuwa wajen faɗa yadda ya ji muryarta tana rawa, ko kuma labarin da take bashi ne yake taɓa mata zuciya.

Ta ci gaba da faÉ—in

"A watarana wacce ba zan taɓa mantawa da ita ba, ita ce ranar babu makaranta domin ranar asabar ce, muna zaune muna ta hira da mahaifiyata na ce mata wajen Aliya zan tafi haka na fito zan tafi muka haɗu da mahaifina a ƙofar gida zai shigo, nan na masa sannu da dawowa ina faɗa masa wajen Aliya zan je yana faɗin ai dama ya san zancen gizo bai wuce na ƙoƙi, a nan har yake nuna min ledar hannunsa yana cewa maƙocinsa ne na gaba da mu kaɗan ya bashi ɗanyen rogo da yake ya noma kasancewar ina son rogo na hau murna ina cewa zan dawo in ci idan an gama dafawa, wannan ita ce baƙar rana, wannan ita ce rana mafi muni kuma mafi tarihi a cikin rayuwata" Ta faɗa tana kuka tare da share hawayenta shi ma Ibrahim hawaye yake yana bata haƙuri sai da ta ɗan numfasa kafin ta ce

"Ashe wannan rogon shi ne ajalin iyayena, ni kuma kwanana ne a gaba shi ya sa ban ci ba, bayan mahaifiyata ta wanke ta dafa ta zuba min nawa ni da Aliya ta ajiye mana suka ci nasu daga cin wannan rogo sai ciwon ciki babu wanda ya san ciwon cikin har ya yi ajalinsu gabaÉ—ayansu sai da muka je ni da Aliya mu ci rogo a nan na yi tozali da gawar mahaifana kwance kowa da dafara a bakinsa" Kukan da take yi ne ya hana ta ci gaba, sai da ta tsagaita ta ce

"Ashe dai wannan rogon taki ne aka zuba mai ƙarfi a gonar wanda gubar da jikin takin da yake jikin rogon bai fita ba shi ne ya yi ajalinsu duk da cewa an dafa shi amma dai takin bai bar jiki ba" Daga shi har ita kuka suke ta ci gaba da faɗin

Tun daga wannan rana na yi bankwana da iyayena, sannan Abba ya je har Doso amma neman duniyar nan ba a samu wanda ya san mahaifana ko wani wanda yake da alaƙa da su, riƙona ya koma hannun Abba har kawo yanzu" Ta faɗa tana share hawaye, ko a fuska bata faɗa masa irin ƙalubalen da ta shiga bayan mutuwar iyayen ba da irin canjin da ta samu daga Umma da Aliya ba wanda shi ne har yau bata sauya zani ba, a ganin Umma babu yadda za a yi Abba yake riƙe da ƴar da bai san wani dangi nata ba, sai kuma ƙoƙari da farin jininta wanda shi ne ummul aba,isin faruwar komai.

Ya daɗe yana jimanta abin sai ya ji wani mugun tausayinta ya shige shi, tabbas tsautsayi ba ya wuce ranarsa sannan rashin sani ya fi dare duhu da sun san rogon zai yi ajalinsu da basu ci ba, amma dama rai ba bakin komai yake ba. Haƙuri ya ringa bata har dai ta huce da za ta shiga gida ya ɗakko waya iphone 16 ya bata a kwalinta, dakyar ta karɓa sai da ya ɓata ransa, don dama kayan fitar biki da ya ɗinka mata cewa ta yi kar ya kawo saboda ita ko kaɗan bata son ran Aliya ya sosu.

Da sallama ta shiga gidan, Umma ta amsa tana washe baki, suna zaune da Abba suna magana ita kuma Aliya tana ɗaki ko da ta shigo a kan tabarmar ta durƙusa ta miƙawa Umma kwalin wayar tana mata bayanin wanda ya bata, Umma sosai ta nuna murna tana nunawa Abba ya karɓa ya saka albarka, Umma ta miƙo mata ta karɓa ta nufi ɗaki, abin mamaki tana shiga Aliya ta ce

"Ƙawata ƴar uwata" Lafazin ya zo mata a bazata har ta kasa riƙe farincikinta ta ajiye kwalin wayar a kan katifa ta je ta rungume Aliya tana faɗin

"Aliyata ta dawo gareni haƙiƙa na yi farin ciki" Ta faɗa har lokacin tana rungume da Aliya, tabbas tana son Aliya, Aliya kuwa ji take tamkar ta shaƙe Jidda amma haka ta daure ta danne zuciyarta ta nuna mata farincikin ta.

Bayan sun saki juna ta ɗakko wayar cike da murna ta nuna mata wani abu ya caki zuciyar Aliya wai Jidda ce za ta riƙe Iphone bayan ita tana fama da waya mai screen a ragargaje, haka ta danne zuciyarta ta nuna mata farincikin ƙarya, don yanzu dai ta ga Jidda ta kere ta a komai.

An shiga hidimae biki a inda Umam ta ɗauko duka kayan kicin ɗin da ta saya domin Aliya ta raba a biyu ta ce kowa ya ɗauki ɗaya a fili tana nufin saboda soyayya amma a baɗini ta bayar ne don su ƙara saka yarda a zuciyar Jidda, ita kuma Jidda sai take ji tamkar bata yi rashin mahaifiyata ba irin yadda Umma take nuna mata soyayya da kukawa. Ana saura kwana huɗu biki aka je aka yi jere mutane anguwa da kuma ƴan uwa, gidan Aliya suka fara zuwa ciki da falo da banɗaki sai ɗaki ɗaya da kuma kicin shi ma ba mallakin Nasir ba ne mahaifinsa ne ya bashi a kan cewar kafin ya mallaki nasa. Ranar da ya kasance saura kwana uku aka je aka yi wa Jidda sam barka jama,a suna ta yabon gida da kuma yadda kaya ya amshi gida faɗa ma ɓata baki ne.

Amare sun sha gyara don sai Aliya da ƙawayenta suka bi ayarin gyaran jikin su Jidda komai dai a na Jidda aka musu suka fito gwanin sha,awa an sha lalle ja da baƙi.

Umma aka samo mata number maman afrah marubuciya a jikin littfinta ta ruɓaɓɓiyar igiya, jin ana ta yabon kayan matan maman afrar mai suna DARAJAR MATA haka ta saya musu tsumin ƙorama, maganin sanyi mai suna a fatattaki sanyi kasancewar duk wani maganin mata ba ya aiki in dai akwai sanyi a jikin mace. Daka mai suna sirrin ma,aurata wanda yake saukar da ni,ima ga mace sai ɓulɓul na gyaran breast sosai maman afrah ta musu haɗi na kece raini wanda zai kankaro musu mutunci wajen mazajensu Umma ta yi hakan ne don Jidda ta yarda ɗaya suke da Aliya. Mai buƙatar maganin sanyi ko magungunan mata ya yi wa maman afrah magana a 09925576222
Chapter 32 · 0% Book details