Sashe 58
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yamma tana kwance a falonta wayar sabuwar riƙe a hannunta ga kuma lambar Ibrahim da take son kira bayan ta yi ta sauya muryar da za take masa magana da ita yadda ba zai taɓa fahimtar cewa ita ba ce so take ta yi amfani da damarmaki ta fara gina kanta a zuciyarsa yau da gobe kafin ta masa dirar mikiyar da duk runtsi duk wuya sai ya aure ta.
Tafiya yake a mota ya kusa ƙarasawa gida, ya ɗan fita ne shi ne ya dawo, yana tafiya yana tuno masoyiyarsa da yadda ta sauya gabaɗaya rayuwarsa idan ya tuna Jidda babu abin da yake sai saka mata albarka da fatan gamawa da duniya lafiya.
Wayarsa ce ta shiga ruri, tunaninsa ma ita ce sai dai ɗago wayar ya sauya masa akalar tunaninsa domin kuwa wata baƙuwar lamba ce a rubuce a saman screen ɗin raɗo-raɗo.
MAMAN AFRAH
0902557622
[11/18, 12:08 PM] ðŸ˜: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=wwt
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
*BABA*
Cikin sauri yana ɗauke da iccen ya nufi store ɗin Hafsat da take tsaye laɓe daga bakin ƙofa ta ciki, riƙe take da kwano wanda ta ciko da shinkafar, Baba babu tunanin komai ya nufi ɗakin tana jin yana dab da shigowa ta saki kwanon shinkfar ya faɗi, a bakin ƙofar suka ci karo amma sai Hafsat ta shammace shi ta fita ba tare da ya kwala mata iccen ba, da gudu ta nufi wajen katangar gidan Baba ya rufa mata baya iccen yana rinjayarsa tana zuwa ta ɗare katangar dakyar kasancewar ba wani tsawo ne da ita ba Baba kuwa ganin za ta tsare kuma ba zai iya ɗagawa ta yadda zai rafka mata ba, don yau iya ganinsa sai ya rotsa kan ɓarawon shinkafarsa tun da dai har Allah ya nuna masa shi muraran.
Ganin ba zai iya ɗaga iccen ba sai ya yi wurgi da shi saboda ƙarfin hali ya kama katangar shi ma ya ɗare don ya yi alƙawarin ko a shi ko a ɓarawon shinkafa.
Hafsat ganin Baba ya hayo saman katangar sai gabanta ya shiga faɗuwa saboda kar ya je ya gane ta, duk da ta saka hular sanyi a kanta ba zai ga gashinta da zai nuna mace ba ce kuma ba lallai yadda yake a rikice ya yi la,akari da duk wani abu na jikinta da zai alamta masa ba namiji ba ne. Baba kuwa ganin ɓarawon zai dira sai ya miƙa hannu ya kama rigar Hafsat a zuciyarta ta ce
"Shikenan na shiga uku yau in asirina ya tonu daidai yake da barina gidan nan ko makamancin haka, amma ba zan yarda ba duk sai na tona asirin kowa matuƙar nawa asirin ya tonu" Bismillah ta yi a zuciyarta ta saita ƙasa ta dira inda Baba ya riƙe a jikin rigarta kasancewar rigar yadin ya gama cin duniyarsa bashi da wani ƙarfi saboda tsufa kawai sai ta yage ya zamana gutsuren yana hannun Baba ita kuma ta dira waje.
Baba ya kalli gutsuren rigar ɓarawon a hannunsa takaici y ishe sa har zai dira sai ya hango ɓarawon ya zura da gudu, sannan ya hanga ya tabbatar tsakar dare ne ba ya hango kowa sai haushin karnuka, tunnainsa ɗaya kar ya bi bayan ɓarawon ya je ya shaƙe shi a banza a wofi wannan tsoron da ya ɗarsar masa a zuciya yana tunanin kar ma dai ko akwai wuƙa a aljihun ɓarawon kamar yadda mai napep ɗin da ya kai shi gidan Sadiya da zai mayar da ita ranar da Nasir ya dawo da ita ya shammace shi ya fito da wuƙa, bai yi wata-wata ba cikin sauri ya duro daga saman katangar ko ta kan iccen bai bi ba ya nufi ɗakinsa ko ɗakin shinkafar bai koma ba, yana shiga ɗakin duk sai wani tsoron ya ɗarsu a ransa yana tunanin da mai ya kai shi zai je ya bi bayan ɓarawo ya kashe shi ya kashe banza.
Bai runtsa ba har asuba yana ta tunanin ɓarawon nan ashe dai zuwa yake yana ɗauka har yake zargin iyalansa ashe dai su hidima suke masa da kuɗinsu. Sai da aka shiga masallaci sannan ya fito ya yi alwalar ya buɗe ƙofar gidan ya fita, ita kuwa Hafsat tun lokacin da ya koma ɗaki da aka jima ta lallaɓo ta hayo katangar ta dawo gidan.
Yana dawowa daga masallaci ya kewaya bayan gidan nasa yana duba sawun ɓarawo sai dai tun da daga gefen gidan ne kaɗai ƙasa da yake kuda da kwalta ne babu inda sawun ya je, haka ya haƙura ya dawo gidan.
Yana zuwa ya shiga store ɗin ya ga yadda aka zubar da shinkafar nan ransa ya ɓaci a nasa ganin wannan ɓarawon ya ga makwancinsa. Haka ya sha masifa a gidan babu wanda ya kula shi a ƙarshe ya je ya siyo ƙaton kwaɗo ya datse ɗakin tun da ya ga ashe taƙadarin ɓarawon har mukullin gare shi tun da gashi yana buɗewa.
BAFFA
Rayuwa ta ci gaba da kaaancewa a gidansa har yanzu babu abin da ya dame shi da matsalar iyalinsa, Mamy kuma koyaushe cikin zulumi take dangane da yaran nata kowane yanzu abubuwan da yake ɓullowa da shi da ban, daga ta toshe waccan ɓarakar sai su fito da wata sabuwa. A ɓangaren Zalika yanzu kanta ya fashe domin kuwa na zaɓawa kanta rayuwa marar kyau da take ganin ita ce mafita a wajenta, rayuwar da wasu daga cikin ƴanmatan zamanjn nan suka zaɓawa kansu wanda ta biyewa shawarar ƙawarta Islam wacce tuni ta yi nisan da vata jin kira rayuwar siyar da mutunci wanda suke ganin holewa ne, bata yi la,akari da yadda mahaifiyarsu take ƙoƙarin inganta tarbiyarsu ba tun da mahaifinsu bai damu da tarbiyarsu ba ya sakarwa mahaifiyarsu ragamar komai.
Zaune suke a wani wajen shaƙatawa su biyu sai wani baƙin Alhaji da mai ƙaton ciki ya gyara zama yana mai saka hannu a aljihu ya ciro waya yana cewa
"Gaskiya islam baki da dama yanzu kuɗin shan ice cream ɗin ne har 500k" Ya faɗa yana ɗan dariya irin tasu ta manyan riƙaƙƙun ƴan duniya a ƙalla ya haife su amma ba ya tunanin abin da yake musu za a iya yi wa nasa ƴaƴan kawai duniyar ce a gabansa.
Islam ta yi wani farrr da idanu ta ce
"To kai Alaji 500k nawa take a wajenmu ai dama sai dai shan ice cream É—in ka san dai mu manyan yara ne" Dariya ya yi ya kalli Zalika da take É—an danna waya ya ce
",Wai haka ne?" ,Ya tambaya yana É—aga gira É—aya wani murmushi ta yi ta ce
"Kai za ka ba kanka wannan amsar"
A maimakon ya saka musu 500k sai ya tura musu 1m Islam tana ganin alert sai kawai ta karkaÉ—a kai tare da cewa
"Yesss Alaji shi ya sa kake birgeni ka iya kyauta babu beb É—in da za ta maka rowar komai tun da kana buÉ—e bakin aljihu" a faÉ—a tana mayar da kallonta kan Zalika da take darawa. Ji ya yi kansa ya fashe saboda haka sai kawai ya ce
"Zalika mu mayar da Islam makaranta sai mu je hotel mu ɗan huta ko" Tana murmusawa ta tashi tsaye Islam ɗin ma ta miƙe tana musu tsiya cewa wato ƴar wariya ce. Sun kaita har cikin makarantar kafin ya karya kan motar suka wuce hotel Islam ta nufi cikin makarantar tana jin daɗin haɗuwa da Zalika kasancewar ita Islam ƴar talakawa ce kuma tana da son ƙarya da son abin duniya, inda ita kuma Zalika ba son abin duniya ne a gabanta ba kawai ta zaɓi wannan rayuwar ne da aka nuna mata ita ce mafita tun da tana ganin mahaifinta bai damu da su ba, sannan dama waje nan ne inda kowane uba zai sakawa ɗansu ido saɓanin ita uwa da take gida sai abin da ya zo kunenta na labari, don uban shi ne jagaban gida duk da uwa ma tana nuna tata bajintar domin dole a jinjinawa uwa ma wajen bada tarbiya.
Sai dab da magriba ya ajiye ta a inda suka yj za su haɗu da Islam, kuɗin suka raba inda ta tari napep ta koma gidansu. Yanzu kam tana jin tashen balaga, don Mamy ta lura da sauyin Zalika kan dana shayinta ko jin tsoronta yanzu ko faɗa take mata ma sai ta ga dama za ta tanka bare har ta bata haƙuri. Kawai kamar rai bata ma son a mata faɗan don haka Mamy har ta yi faɗan ta gaji!.
Da daddare misalin ƙarfe uku na dare Mamy ta tashi ta nufi ɗakin Zalika, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta mayar ta rufe, tana ta bacci hankali kwance, don ta ga shi ma Mubin sai wajen tara ya dawo dik abubuwa sun haɗe mata goma da ashirin. A hankali ta lallaɓa ta ɗauki jakar da Zalika ta fita da ita yau ta fito daga ɗakin ta rufe mata nata ɗakin ta nufa tana son a matsayinta na uwa ta fara binciken sirri ba tare da sanin Zalikar ba, tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar ta nufi bakin gado ta zauna gabanta sai faɗuwa yake, don dama ta duba wayarta jiya sai ta ga ta saka pswrd, tana son ta san abin da take aikatawa don tana jin zargi a ranta.
Hannunta yana karkarwa ta buɗe jakar ta ciro komai na ciki ta birkice sai dai bata ga wani abu da ya danganci rashin gaskiya ba haka ta haƙura tana ɗn jin sanyi da sawaba a zuciyarta, tana dab da mayar da kayan saj ta ga ƙaramun zip daga ciki har za ta rufe jakar sai kawai wata zuciyar ta bata shawarar dubawa ko za ta samu wani abu da zai tabbatar mata wani abun. Tana zige zip ɗin abin da ta gani a ciki ya yi masifar faɗar mata da gaba, a take hankalinta ya tashi don bata san ma ta miƙe tsaye da abin a hannunta ba sai da ta ganta riƙe da abun tana tsaye a kan ƙafafunta cankarkar, jiri ya fara ɗaukanta....