← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 106

Sashe 85

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sadiya mu zuba ni da ke yanzu dai baki da tsumi baki da dabara idan musgunawa ta ta ishe ki ke da kanki za ki san na yi" Tana cikin wannan maganar sai sheɗan ya ƙara kissima mata wani mugun abun da sauri ta tattara kuɗin ta mayar tana mayar da jakar drower ɗinta ta fito daga ɗakin, mukullan ta sake ɗauka sai kawai ta nufi kici ɗin Sadiya ta buɗe ta dawo ta buɗe ƙofa ta aiki wani yaro ya siyo mata kananzir ta rufe ƙofar ta je ta yi abin da za ta yi ta mayar ta rufe ta ta kai ƙaramar jarkar lemon coca cola da aka sayo a ciki ta ba wani almajiri shara ya zubar mata dama jarkar tana ciki.

Sadiya sai bayan magriba ta dawo bata ma san ta jefar da mukullin ba sai da ta dawo ta buɗe aljihun jakarta ta ga ba ya nan ɗan ja baya ta yi tana haska fitilar wayarta kawai sai ta ga Kalifa ya miƙo mata mukullan ta tambaye shi sai ya nuna mata ƙasa kusa da inda take tsaye hakan ya sa ta gane a gabanta ya ɗakko sai ta yi tunanin yanzu da ta buɗe jakar ya faɗo bata sani ba.

Hankali kwance ta buɗe musu ƙofar suka shiga don zuciyarta wasai take ji babu damuwa domin Kaka ta mata nasiha da kuma ƙara bata haƙuri a kan lamarin zaman auren ta tana nuna mata komai ya yi farko yana da ƙarshe don kowace gona tana da kunyar ƙarshe ta faɗa mata idan dai mace ta haɗu da fitinanniyar kishiya ko fitinanniyar uwar miji ko dangin miji sai ta yi haƙuri duk mai haƙuri watarana zai dafa dutse har ya sha romonsa. Ta ƙara koya mata dabaru da kissa da za take nunawa kishiyar duk abin da take mata ba ya damun ta.

Sai batun ƙauracewa ɗakinta da Nasir yake da ma ƙaurace mata baki ɗaya shi ma ta ce ta yi haƙuri lokaci ne, sannan shi lokaci alƙali ne watarana da kansa zai neme ta don Kaka ta faɗa mata cewa namiji tamkar sauyin abinci haka ya ɗauki mace ta bata misali da cewa shin za ta juri cin abinci ɗaya kullum? Wato koyaushe a ce ta ci shinkafa da miya sai Sadiyar ta nuna za ta so sauyi watarana mana yau ta ci shinkafa gobe taliya jallof jibi wake da shinkafa ta haka Kaka ta nuna mata cewa to akwai ranar da Meenal za ta gunduri Nasir ɗin ya ji yana son kasancewa da Sadiya don kowacce mace halitta da baiwar ta da ban wata ta fi wata kawai dai idan kana da kyau sai ka ƙara da wanka!.

Sai da ta buɗe drower za ta ɗakko rigar bacci bayan ta yi wanka sai kawai ta ga kamar dai kayan ba haka suke ba, saboda Sadiya tana da lura da al,amura kawai sai ta fara zargin kayanta ba haka ta bar su ba duk kuwa da Meenal sai da ta gyara komai, a ƙarshe Sadiyar ta saka a ranta cewa ita da ta kulle ƙofar ɗakinta kuma ma ai babu yadda za a yi a shigo mata ɗaki me ma za a yi a ɗakinta.

Bayan sun kwanta Kalifa ya yi bacci, don tana jin lokacin da Nasir ya dawo amma ko ɗakinsu bai zo ba dama kuma ta san da hakan. Kuɗin da maƙociyar Kaka ta bata na kayan kori da spices da ta ce a turawa maman afrah za a kawo musu curry kwano ɗaya spices na shayi rabin kwank sai spices na girki kwano ɗaya, jan yaji rabi yajin daddawa kwano ɗaya, sai kuma kuka da kuɓewa da niƙƙaƙƴiyar daddawa. Don ita ma natan babu, kuɗin ta ɗakko ta lissafa tana tunanin da safe za ta yi wa maman afrah magana ta tura kuɗin sai a sako musu a mota. Lokar da take ajiye kuɗaɗenta ta buɗe za ta saka kuɗin a ciki domin tana da kuɗi a monie point sai ta yi wa maman afrar transper, tana buɗewa ta ga wayam babu jakar gabanta ya buga da mugun ƙarfi, ta sake dubawa amma babu jaka babu alamar ta, lokar ta ciro daga ciki dukanta ta shiga leƙwa amma jakar ta ce ɗaukeni inda kika ajiye!.

MAMAN AFRAH
09025576222

https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣6️⃣

SADIYA

"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un" Sadiya ta furta a fili tana miƙewa tsaye ta shiga dudduba wajen tamkar dai jakar za ta gani gabanta yana faɗuwa ta shiga dubawa amma bata gani ba duk hanklinta ya tashi saboda kuɗinta ne da take son fita kunya idan ta haihu duk wani tanadinta yana cikin kuɗin amma ta rasa yadda aka yi ta rasa jakar, tun da ta tabbatar a lokar ta saka tun da kafin ta fita ma ta saka kuɗi a ciki. Da sauri ta janye ƙaramar bedside ɗin daga wajen ta duba bayan bed side drower ko ɓera ne ya ja don ra fara tunanin ko lokar a fashe take daga baya amma sai ta ga babu wani waje da yake da alamar fashewa a jiki.

Lokar saman ta janyo tana birkicewa wai ko dai a ciki ta saka duk da Sadiya bata da mantuwa komai nata a nutse take, ma,ana ta san a lokar da ta saka kawai dai tana dubawa ne amma wayam babu ko alamar jaka bare a je batun kuÉ—i.Birkice ta shiga yi a É—akin amma babu jaka babu alamarta haka ta fito falo kamar zautacciya domin ita ta san irin wahalar da ta sha a kuÉ—in tun da halaliyarta ce duk wani mai neman halal kuwa ya san neman halak da wuya!.

Duk hankalinta ya tashi sai da ya dawo ta ga kuɗin da ta karɓo na curry da sauransu sai ta yi tunanin wancan kuɗin ne da take nema amma sai da ta zo ta tuna haka ta dawo ta zauna tana ta ambaton Allah a zuciyarta har dai ta samu nutsuwa a zuciyarta. Tana iya jiyo ƙaran TV daga ɓangaren Meenal kuma ta san shi ma mai gidan ya dawo amma ko leƙo ta bai yj ba domin ta ji zuwansa.

Ita dai ta san ɗakinta a kulle kuma ko ma ba a kulle ba abu sabo abu ne da ba a taɓa.yimata ba wato sata, saboda ta san in har ba ita ta yi niyyar yin alheri ta ba mutum kuɗinta ba babu mai ci sai dai ko Nasir idan son kuɗinsa ya tashi ya ce ta bashi don kawai taƙamar tana matarsa bayan kuma shi ba bata yake ba. Haka ta jure ta haƙura ta kwanta tun da babu wanda za ta tunkara da maganar, haka ta yi addu,a ta kwanta tana ta tunani da ciwon rai ya ishe ta kawai sai hawaye ne suke zuba, ta jima tana hawayen nan har da sheshsheka kafin daga bisani bacci ya yi awon gaba da ita bata falka ba sia wajen ƙarfi biyu da kwata haka ta tashi ta yi alwala ta yi nafila bayan ta idar ta zauna ta yi karatun qur,ani sannan ta karanta sunanyen Allah tare da salatin annabi S.A.W ta ɗaga hannu ta ce

"Ya Allah kai kake ƙaddara komai a lokacin da ka so, ya Allah na san kai kake bayarwa kuma kai kake hanawa Allah ka san damuwata a kan jakata da na rasa ya Allah idan rabona ce ka bayyana min ita idan kuma babu rabona ka sauya min da abin da ya fi alkairi, na yarda da duk wani abu da za ka ƙaddara min" Haka ta gama faɗawa ubangiji tana hawaye tare da jero wasu buƙatub nata sannan ta ƙara yin salatin annabi S.A.W ta shafa addu,ar Ta koma takwanta sai ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi duk damuwa da nauyin da zuciyar ta yi babu shi!.
Da asuba ta yunƙura dakyar ta yi sallah ta sake karatun qur,ni da yin addu,o,in ta.

Da safe da ta fito sai take jin duk babu daɗi yadda babu nepa a ɓangarenta ita bata san ma wanda za ta faɗawa ba, ɓangarenta basa son ta kai ƙaransa shi kuma nata ɓangaren basu damu da ita ba basu san muhimancjn ta ba, sai dai kawai ta san akwai sakayya. Tsakar gidan ta nufa, da yake wajen ƙarfe bakwai ne ruwan zafi za ta ɗora saboda yunwa take ji kasancewar mace mai ciki akwai jin yunwa, ga shi kuma ita bata da nepa bare ta jona a nepa. Tana zuwa ta buɗe kicin ɗin sai lokacin ma ta tuna gawayin nata ya kusa ƙarewa, a haka ta ɗauke na ƙasan buhun duk da ya zama ƙareci duk ƙanana ne, ta samu ta hura da ya kama ta ɗora ruwan. Waje ta samu ta zauna a kicin ɗin tana jiran ruwan ya tafasa tana zaunen tana kallon kayan sana,ar da suke gefe a cikin kicin ɗin aajiye manja farin mai da sauransu tana tuna yadda jakar kuɗinta ta ɓace jiya, tunaninta ɗaya yanzu idan suka ƙare yadda za ta haɗa kuɗin ta saro wasu domin ba lallai ta haɗa kuɗin ba kasancewar asarar da ta same ta duk da ta san Allah ne ya ƙaddara mata.
Chapter 85 · 0% Book details