Sashe 105
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta yi baƙinciki sai dai haka ta daure tana ta sakin dariyar yaƙe Abba kuwa sai godiya yake jerawa Ibrahim ɗin don ya ji matuƙar farinciki. Umma dama da Aliya ta kira ta ta faɗa mata don ba ta bi ta gida ba da ta dawo daga gidan Jiddar saboda magriba ta gabatota san dole za su haɗu da Abba.
Washe gari da Umma da Aliya suka tafi kasuwa bayan Abba ya tafi kasuwa hala shi ma Kasim. Ko da suka kai zoben ba a saya ba duk inda suka je sai a ce sai sun kawo risit ɗin. Sun taka waje kusan bakwai amma duk inda suka je amsar ɗaya ce don kpwa sai ya ce ba zai saya ba in babu shaida domin kar su saya abin sata, duk da rantse rantse da su Umma suka sha yi a wurare da dama kan cewar gobara suka yj da daɗewa ya ƙone risit ɗin, amma sai a ce musu ai da sun koma wajen wanda suka saya sun masa bayani ya rubuta musu wani.
Haka suka gaji da yawo suka koma gida rai babu daɗi .Washe gari ma haka, sai da suka gaji da yawo a kasuwa har wajen ƙarfe ɗaya sannan suka haɗu da wata mata ta ce ita ta san inda za ta raka su a saya don shi mutum hatta kayan sata saya yake kua har yau dubunsa ba ta cika an kama shi ba, tashin farko da suka ji kuɗin sun tsorata domin cewa ya yi miliyan biyu da dubu ɗari da naira dubu uku. Haka ya karɓa ya transper suka tafi suna murna da sharaɗin ko da wani abu ya ka je ya zo karki su kuskura su ambaci sunansa don ya gane alamomin rashin gaskiya a tare da su daga ganin yadda suka razana da kuɗin zoben ya fahimci ba mallakinsu ba ne. Kuma shi ma a hakan ma ya musu zururun dubu ɗari biyar.
Cike da farinciki suka koma Umma ta wuce gida ita ma Aliya ta wuce nata gidan, suka ce sa ƙarasa maganar a waya don dama a akawun ɗin Aliya aka tura kuɗin.
A ranar da su Jidda suka tashi a ranat nr su Umma suka samu labarin wani hamshaƙin boka da ƙawar Umma ta musu jagora. Sun sha baƙar wahala wajen zuwa kasancewar a cikin surƙuƙin daji yake sannan gidansa a kan wani dutse.Bayan an basu izini sun shiga nan ya kwashe abin da yake tafe da su ya faɗa musu ya ce domin an sanar da shi zuwansu da kuma abin da yake tafe da su.
Ya ce zai yi aikin amma da sharaɗin Aliya za ta bashi kanta, sun razana da lamarin buƙatar bokan, sai ƙawar Ummar take mata alama ta amince domin hakan zai sa burinsu ya cika. Sai Umma ta ce sai dai ita ta bashi kanta amma boka ya ce ai sharaɗin a kan Aliya yake don ita ce wacce za a yi wa aikin idan kuma ba za su amince ba su ɗauki takalmansa su bar masa gida. Aliya jin an cr aikinsa kamar yankan wuƙa yake hakan ya sa ta ce kawai ta amince don a neman duniyar da take zuciyarta ta ƙeƙashe ji take komai ma za ta iya sannan tana ganin cewa ba kanta farau ba kuma ba za a ƙare a kanta ba, ta sha jin ana cewa mata da dama sai sun bada jikinsu a wajen boka wa,iyazubillah. Ita kanta zina ba a ɗauke ta a bakin komai ba yanzu a wannan zamanin ba ga ƴanmata ba, ba ga matan auren ba ba ga mazan auren ba sai wanda Allah ya tsallakar amma akwai wanda ko yatsunsu ba sa bari wanda ba muharraminsu ba ya taɓa kuma duk lalaewat zamani ba za su saɓaw Allah ba.
Umma da ƙawarta waje suka fita Aliya suka shiga can cikin ɗakin da bokan yana faɗin aikin da za a yi yana daga cikin wannan sharaɗin in har ta yarda a lokacin da yake tarayya da ita ne zai fara aikinsa. Haka suka yarda da ƙaryarsa ba su san cewa babu wano aiki da zai yi da wannan tarayyar ba kawai ƙishirwarsa yake kashewa da mata mararsa kamun kai masu neman duniyar wanda suka manta cewa komai suka samu a duniyar za su bar shi, hatta ɗankunne ko zobe ba za su shiga kabari da shi ba daga su sai likkafani sannan duk abin da suka saɓawa Allah sai an azabtar da su, da yawa ana mantawa da makoma ne.
Sai da ya gama watsewarsa da Aliya wacce ta manta matsayinta na matar aure, sannan ita kanta zina ko baka da aure haramun ce kusantar ta ma Allah cewa ya yi kar a yi. Sun dawo yana ta washe bakin garaɓasar da ya samu. Ya ce sai bayan kwana bakwai za su dawo. Sai da aka yi kwana bakwai sannan suka kwaso ƙafa suka zo, sai dai ranar su biyu suma zo babi waccrn ƙawar ta Umma da ta rako su, dama ƙawarta ce da suka zauna unguwa ɗaya malotan gidan su Umma ce. A ranar da suka dawo ranar ne ta cika kwana biyar da mutuwa kuma lafiya ƙalau kawai ƙarar kwana ta yanke jiki ya faɗi sai gawarta. Wannan kaɗai bai fahimtar da su cewa duniyar ba za a tabbata a cikinta ba.
A waje ya ce Umma ta dakata zai yi wa Aliyar bayani nan Umma ta fita ta zauna saga gefen dandazon mstan da suke zaune dodo guda suna jiran zuwan layinsu, don su kaiwa boka buƙatarsu zuciyoyinsu sun karkata ga kaiwa wanin Allah buƙatarsu da faɗa masa damuwarsu sun manta Allah kaɗai yake maganin matsala da damuwa wajensa kaɗai ake samun biyan buƙata.
Yana fita boka ya É—akko wata Æ´ar kwalba ya ce
"Wannan kwalbar maganin ciki za ki samu abinci ko na sha ki zuba masa a ciki" Idanu Aliya ta zaro jin wani baban lamati don ba ta manta tababar da ta sha wajen sauya cokali ba, amma sai ta amsa da cewa to.
Ya ci gaba da faÉ—in
"Wannan maganin idan kin tabbatar ya cj abin da kika saka maganin ko ya sha sai ki saka a ƙasanki sannan ki shafa wannan turaren " Ya faɗa yana miƙa mata. Karɓa ta yi tana jiran ƙarin bayani ya ce
"Idan ya sha abin shan duk inda mace take burinsa ya yi tarayya da ita kinnga ke kuma kina nan to za ki yi duk yadda za ki yi tun da kin ce matarsa ba ta ƙasar ma"
Aliya cike da É—oki ta ce
"Malam ka tabbata zai mu,amalanceni"?"
Ya kalle ta ya ce
"Ba saka kokwato a aikinmu"
Ta ce
"Ai na sani kawai dai mutumin yana da taurin rai ne, sannan ya tsane ni ko ganina ya yi sai fuskarsa ta sauya, kuma ko magana ba ta haÉ—amu hasalima iya gaisuwa ne yake haÉ—amu"
Boka ya ce
"Ba kallon ke mace ba kuma mutum to ko da a ce dabba ya gani wato ki ƙaddara bayan ya sha maganin ya ga akuya to saa ya haike mata kawai zai ji yana son kaɗaicewa da duk wata halitta indai mace ce" Murmushjn nasara ta yi tana faɗin
"Na gode sosai boka Allah ya...
Hannu ya É—aga mata ya ce
"Sai kuɗin aiki dubu ɗari biyar ne" Transper ta masa sannan yana nannaga mata sai nan da kwana bakwai ko takwas za ta aiwatar da aikin. Tun da suka taho Umma takr mata nannago a kan ta san idan za ta ajiye maganin don ita Umma ta tsani ma a ce wai magani ba za a aiwatar da aikinsa ba sai an ƙayyade masa kwanaki saboda ta fi son sha yanzu magani yanzu.
A yadda Jidda ta faÉ—a musu cewa sati uku za su yi sai dai daga baya ya zamana sati biyu ne kuma sai ta sha,afa ba ta faÉ—a musu ba. Duk da sau biyu suna waya da Abba amma tun da ta ta fi ba su yi waya da Aliya ba sai Umma ce da suka gaisa a wayar Abba lokacin da ta kira shi, domin sau biyu tana kiran wayar Umma ba ta samun ta.
Sun yi ibada sosai Jidda ta mayar da hankali wajen yin addu,a da neman tsari sannan uwa uba ta sha yi wa iyayenta addu,a da nema musu gafara da rahmar ubangiji aljanna kuwa ta roƙa musu mafi girma da ɗaukaka haka kanta da kuma ginshiƙinta mijinta abin alfahrinta Ibrahim. Ta tsawaitawa Abba addu,a bisa jajircewarsa na kasancewa tsani kuma matakala da ya maye mata gurbin mahaifi. Su Umma ma ba a barsu a baya ba domin tana jinsu a tsakiyar zuciyarta a ƙarshe ta sha saka jama,ar musulmi a addu,ar neman shiriya da samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Yau ya kama talata a yau ne suka kammala komai yau ne jirginsu zai tashi zuwa Nigeri,a ƙarfe sha biyu na rana jirginsu ya taso daga jidda awa shida ya kawo su Nigeri,a jirginsu ya sauka ƙarfe shida na yamma.
A ɓangaren Aliya yau ya cika kwana takwas daidai da dawowarsu daga wajen boka kuma yau ne ya dace ta aiwatar da aikin da zai zama cikar burin nasu. A nata hasashen kuma iya saninsu saura sati guda Jidda ta dawo wanda sun yi imanin idan ta sauka a Nigeri,a lokacin ta zama tarihi a zuciya da rayuwar Ibrahim.
Ko da ta ga dab da magriba ta tabbatar lokacjn yana gida domin wani matashin saurayi ɗan zauna gari banza da ta saka shi zama a unguwar yake kular mata da motsi shige da ficen Ibrahim a ranar. Bayan ya sanar mata ya ga shigarsa gidan, don haka lokacin da ta zo sai da ta leƙa wata tula ta tabbatar da mai gadi ba ya harabar wajen, ta yi saɗaf saɗaf ta turo ƙofar domin ta tabbatar yana banɗakin. Har ta shiga falon da yake ƙasa ba ta samu kowa ba a falon shiru don ta ji Jidda ta ce su Saude za su koma ƙauyensu har sai ta dawo.
Bayan kujera ta samu ta haura wanda yake da É—an faÉ—i inda yake daga wajen kwana ta bango aka saka kujerar kasancewar kujerun irin wanda ba a saka su har bango ne.