Sashe 48
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wannan furucin da ya yi da ƙarfi tamkar wanda ya hango wani gagarumin haɗari ya tunkaro su,shi ne ya sanya Sadiya dawowa hayyacinta a kiɗime tana ciccira ido domin ganin abin da yake faruwa, shi kuma mai napep har da sauri kashe kiɗan da ya ƙure ya tsayar da napep ɗin tare da juyowa ya ga abin da ya faru. Baba kuwa kuwa babu ruwansa da kiɗimar da ya saka su bai yi bori da sanyin jiki ba ya ce
"Wai don Allah mai ya sa Nasiru yake son tona mini asiri ne? Ya zai mayar mini da ƴa gida kuma ya garƙamawa gidan mukulli gidan uban wa ya tafi to?" Ya faɗa ya ɗorawa Sadiya Kalifa a cinya, ita Sadiya sai lokacin ta lura da gidan a kulle kuma ta gane duk wannan ɗaga jijiyar wuyan da Baba yake saboda gidan a rufe ne da yake ma basu gama ƙarasowa gaban gidan ba, dogon wuya Baban ya yi ya hango.
Baba kuwa fita ya yi daga cikin napep ɗin duk ya gama tada hankalinsa sai baza uwar babbar riga yake tana neman taɗe shi, Sadiya ta ma rasa bakin magana ikon Allah kawai take kallo, shi kuma mai napep da ya gane mai Baban yake yi wa baloƙoƙon sai ya ja wani ƙaramin tsaki ba tare da kowa ya ji ba. Baba kuwa ƙarasawa bakin ƙofar ya yi ya taka matakalar ƙofar gidan ya taɓa kwaɗon (Padlock)Ɗin da aka rufe gidan cike fa faɗa ya ce
"Sadiya wai ni kika rako ko kuwa ke na rako da kika zaune a adaidaita sahun? " Cikin sanyin jiki Sadiya ta fito tana cewa
"Baba gani na yi gidan a rufe" Yana harararta ya ce
"Kuma don gidan a rufe sai ki zauna a ciki kamar wanda dai so kike ki koma gidana" Bata tanka masa ba ya tsaya tare da kama ƙugu yana hangen ta inda Nasir zai fito. Mai napep kuwa ya wani sako ƙafa waje ya ɗauki mataji(Kumb)Ya ɗan taja gashin kansa cike da tantiranci ya ce
"Yallaɓai karka manta dai duk tsayuwar da nake yi a wajen nan a kuɗi take don haka yawan jiran da zan yi yawan hauhawar farashin kuɗina" A zuciye Baba ya ce
"Abin da ya fi hauhawar farashin kuɗinka, sai ka ce sata kana tsaye ba tafiya kake yi ba bare ka ce mai kake ƙonawa amma kake batun kuɗi yo ba zan biya ba, bayan ma zuwan nawa babu biyan buƙata" Wani irin durowa ya yi daga napep ɗin ya tsaya Baba yana jifansa da wani kallo, mai napep ya waiwaya ya ga layin ba kowa yana ɗaga rigarsa sai ya zaro wata zarɓeɓiyar wuƙa soke a jikin wandonsa, da sauri Baba ya matsa a kiɗime har yana zamewa ya surmiyo daga saman dakalin ƙofar gidan, mai napep ya ce
"Bani haƙƙina, in ba haka ba in farɗe maka ciki daga kai har ƴaƴan naka" Da sauri Sadiya ta ƙanƙame Kalifa cike da tsoro dama ita sai ta ga ma tamkar wani ɗan shaye-shaye ne Baba hannunsa yana rawa ya saka a aljihub babbar rigarsa sai ga kuɗi ya fito da su ƴan dubu-dubu kusan dubu ɗari biyu bakinsa yana rawa yake faɗin
"Nawa ne kuÉ—in naka har na jiran da ka yi" Mai napep ya ce
"Dubu da É—ari biyar" Baba hannu yana rawa ya ce
"Ga dubu biyu ka riƙe canjin" Karɓa mai napep ɗin ya yi ya mayar da wuƙar ya koma cikin napep ya ɗakko ɗari biyar ya jefawa Baba ya ce
"Ni da kake ganina haƙƙina nake nema, babu ruwana da sai na karɓi haƙƙin wani shi ya sa ba na sata, na gwammace duk runtsi na nemi na kaina na kaucewa wulaƙanci, kuma ni da kake gani ko akuya ban taɓa kashewa ba ita ce dai dabba bare kuma mutum kawai barazana ce saboda masu ci da haƙƙin wani" Yana gama faɗar hakan ya shiga napep ɗinsa ya tada ya kunna waƙa ya yi kwana ya bar wajen a guje.
Baba É—ari biyar É—in ya É—auka ya zauna a kan dakalin yana faÉ—in
"Wasu yaran zamanin fitsararru ne, ashe ma duk bige ne ba iya caka wuƙar zai yi ba, ai wallahi da na san haka ne da dubu ɗaya zan bashi" Ya faɗa yana haɗa kan kuɗin ya mayar aljihu, Sadiya kawai kallonsa take da mamakin kalamansa duk da babu wani abu sabo a lamarin Baba.
Ranta ƙuna yake bai dace a ce ya yi mata abin da ya mata ba, ta yaya za a yi a ce mijinta ya kaita gidan ya tafi ahi kuma ya dawo da ita. Waje ta samu ta zauna take ganin ikon Allah sun kwashe ya fi minti arba,in amma babu alamar Nasir sai mutane da suke wucewa, Baba sai hamma yake a jere can da ya gaji ya ce
"Tashi mu je gidan mahaifiyarsa ki zauna w can ki jira shi, ai in ya dawo ya je can ya ɗakko ki" Wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata, jin wai gidan sirikarsa zai kaita, sirikar da ita ce silar duk wasu abubuwan da suke faruwa, sannan ta yi imani da Allah sai sun yi wa Baban wankin babban bargo sannan kuma ya bar mata abin gori na cewar ubanta ne ya dawo da ita. Kamar daga sama ƙwaƙwalwarta ta kai mata wasu tunani a take ta zaɓi ta yi wa Baban ƙarya don tsira da daraja da mutuncin ta, duk da ƙarya ba ɗabi'arta ba ce kuma ba halayyar ta ba ce.
Cike da danne abin da ya É—arsu a zuciyarta ta ce
"Baba ai Hajiyar bata gari ta yi tafiya" Kamar wanda ta faɗa masa saƙon mutuwa ya ce
"Subhanallahi bata gari kuma? Amma ai ba za a rasa sauran Æ´aÆ´an nata a gidan ba" Da sauri ta ce
"Tare suka tafi" Ya numfasa ya ce
"Kai ni dai na ga ta kaina wallahi yaron nan yana son tada mini hawan ruwa, to ke dama baki É—auki mukulli ba" Sadiya ta ce
"Shi ya datse gidan da kansa"
Baba ya ce
"Dama ya shirya shuka tsiyar nan amma dai mu je gidan, kuma wallahi sai dai mu tafi a ƙafa ba zan biya kuɗin adaidaita ba" Yana faɗa ya fara tafiya, haka Sadiya ta bi bayansa tana ɗauke da Kalifa a kafaɗarta, ranta har ya mata daɗi ganin Baban bai zubar mata da mutunci a wajen Nasir da mahaifiyarsa ba, duk da ta san da wuya ne idan bai faɗa masa cewa ya rakata gidan a rufe ba.
Suna tafiya yana masifa wayar Nasir kuwa ya kira ya fi a ƙirga amma bata shiga, ko da suka koma gidan ɗakinsa ya shiga ita kuma ta je ɗakin Mama Talatu.
Mama ta ce
"Sadiya yankuka dawo har gabana ya faɗi ko dai dama yaji kika yi shi ne kika yi ƙaryar tare kuk?" Kai kawai ta girgiza.
Sai a É—akin Mama Habiba suka kwana saboda Sumy ta kafa rashin mutuncin Kalifa ba zai kwamta a katifa ya musu fitsari ba, shi kuma É—akin Æ´anmatan dama bata ma tarki zuwa ba saboda ta san rashin kunya za su mata.
Baba washe gari bai je kasuwa ba, ya kasa fita saboda gani yake tamkar igiyar Sadiya ce za ta tsinke idan ya bar gidan, wato kamar in baya nan Nasir zai dawo ya kawo takardar saki, amma idan yana nan ko da ya zo da niyyar sakin zai roƙe shi ya fasa sakin. Har wajen goma wayar bata shiga, wayar Arfat Baba ya karɓa ya saka lambar Nasir ya hau doka masa kira sai kuwa ya ɗauka da ta kusa katsewa.
Nasir ya ce
"Hello" Baba ya ce
"BuÉ—e muryarka da kyau Babanka ne mahaifin Sadiya" Da sauri Nasir ya cire wayar daga kunnensa ya duba ya dai tabbatar da numbar Baba ba ce dona ya san ya saka duka lambobin Baba a black list. Jin haka sai Nasir ya ce
"Hello ba na ji" Ya faɗa yana ciro wayar daga kunne ya shiga hura iskar bakinsa da ƙarfe, yadda Baban zai ji, Baba jin haka ya buɗe baki yana faɗi
"Baka ji na Nasir" Nasir da sauri ya katse kiran, yana shirin saka lambar a black list sai kiran ya sake shigowa haka ya É—auka Baba ya ce
"Nasir mai ya sa ka kawo Sadiya gida" Nasir yana taɓe baki ya ce
"Laifi ta yi" Baba ya ce
"Amma wannan an yj shegiyar yarinya amma ta ce babu abin da ta yi ka kawota" Nasir ya ce
"Ruwa ai ba ya tsami banza" Nan Baba ya shiga bashi haƙuri duk da bai ji laifin da ta yi ba yana cewa zai saɓar mata Naair ya ce
"Baba kawai a kan maganar matar da zan aura za ka ja mata kunne, ta ce bata son raini in ya so yanzu zan kira wacce zan aura ɗin sai na faɗa mata ka bani haƙuri in ta haƙura to" Baba tsabar son zuciya bai ma ji zafin maganar Nasir ba ya ce