Sashe 100
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ƴar tawa guda ɗaya to in har suniya kika so ta bari ba sai kin biyo ta haka ba, da kin faɗa ma cewa kina neman raba ta da ranta da tuni ta bar miki gidan, ba dai a kan namiji ne za ki yi kisan kai ba, ku mata sai shishshigi komai ku aikata a kan maza wasu mazan ma ba su damu da ku ba, to ni ina ƙaunarta iya kaɗai gareni sannan sai kin fuskanci hukunci domin ba za mu bar wannan maganar ba" Nasir sai haƙuri yake ba ta amma ko gaisuwarsa ba ta amsa ba tana ta masifa wai za a kashe mata ƴa bai ɗauki hukunci ba.
Sadiya tana ta rantse rantse amma kuma sai harara take samu da tukuicin masifar Momi.
An fito tsakar gidan Momi tana riƙe da hannun Meenal saboda ta ce ma ba ra jin ƙarfin jikin ta Momi ta ce
"Wannn cikin da kika samu ne ake miki hassada ba a so ki haihu a gidan wato sai ita ce za take haihuwa shi ya sa ta yi tunanin raba ki da duniya" Nasir dai É—akin Sadiya ya nufa domin ya tabbatar da cewa filon natan ne suna tsaye a tsakar gidan sai Momi ta ce gabaÉ—aya za a shiga É—akin Sadiya haka suka shiga yana gaba suna biye da shi sai dai da aka zo bedroom É—in za a duba filon a tabbatar sai ga hula a tsakar É—akin da sauri Nasir da ya ga hular ya ce
"Meenal wannan ba hular ki ba ce?" Ya tambaya domin ya gane hular tata ta net ce kuma da zai fita lokacin tana kwance hular tana kan ɗayar kujerar falon a ajiye ta ce ya miƙo mata ya karɓa ta saka a kanta wannan dalilin ya sa ya gane hular. Idanun kowa na ɗakin suka sauka a kan hular inda Meenal gabaɗaya ta rikice har ta kasa haɗa haruffan da za ta bashi amsa, amma saboda ƙarfin hali sai ta ce
"Lah hula ta ce" Ta faɗa da mamakin ganin hular tana mai miƙa hannu ta taɓo kanta, tana sake cewa
"Ikon Allah mai kuma ya kawo hulata ɗakin nan hular da tana kaina na yi bacci ɗazu" Momi ta yi karaf ta ce sato ta aka yi za a shirya miki wata maƙarƙashiya, wataƙila malami ne ya ce a kawo hular da take kanki zai yi wani aiki," Wani daɗi ne ya cika Meenal jin mahaifiyarta ta kawo mata haske, duk da gabanta ya faɗi da ganin hular kuma ta tsorata da lamarin, saboda ko kaɗan ba ta san hular ta faɗi daga kanta ba lokacjn da ta zo ɗaukan filon.
Safiyya ta ce
"Lallai maso abinka ya fika dibara, ban da ƙarfin hali ɓarawo da sallama hula a kankam a je a ɗauke kai zaman kishi sai ka shirya zama da kishiya gaskiya ba wasa ba ne"
Sadiya gabanta ne ya sake faɗuwa jin za a ƙulla mata wani sharri wato ana ƙoƙarin watsa mata tsaba kaji su bita. Cike da tausasa murya ta ce
"Wallahi ban san da zaman hular nan a nan ba na rantse da Allahn da ya halicceni ba ni na É—akko ta ba"
Nasir da ya gaji da abubuwan nan ga shi ya ga sirikar tasa ma kamar ƙoƙarin ƙara kunna wutar bala,in take sai ya ji duk ransa ya ɓaci hakan ya sa ya ji haushin Sadiya domin dai hakan yana tabbatar masa da cewa abubuwan da ake zargi a kanta haka suke tun da ga shi an ga hular Meenal a ɗakinta kuma tana rainawa mutane hankali a fusace ya ce
"Hular ce ta zo da ƙafarta" Kallonsa ta yi idanunta taf da hawaye ta ce
"Wallahi Abban Kalifa ba ji ba ce"
Momi ta ce
"Sadiya ya kamata ki daina yi wa mutane wasa da hankali kawai ki fito fili ki faɗi gaskiya dama an san gaskiya ciwo ne da ita, don haka kawai ki faɗa kanki tsaye ni kuma na miki alƙawarjn za a rufa miki asiri matuƙar kika amsa laifinki"
Sadiya kallonta ta mayar kan Momi ta ce
"Wallahi duka abubuwan da ake zargina ban aikata ba hasali ma na je ɗakin Meenal don na taimaka mata amma shi ne take mini bita da ƙulli dukan kabarin kishiya"
Meenal ta ce
"Allah sarki ni, wato Sadiya saboda kin ga mu biyu ne a gidan nan babu na uku wanda zai yi shaida shi ne kike faÉ—ar son ranki"
Sadiya ta ce
"Ni Allah ne shaidata kuma tun da nake ban taɓa zuwa wajen boka ko malam ba, bare na faɗa masa buƙatata ni Allah na dogara, kuma shi ne shaidata cewa ban ɗauko hulamdon na yi magani ba kuma ban ɗauki filo na je don na rabata da numfashinta ba"
Momi ganin ramin da ta yi wa zSadiya don ta rufta ba ta rufta ba sai ranta ya yi mugun ɓaci ta ce
"Mu da wa muka ce miki muka dogara? Mu ma Allahn dai ne abin dogaranmu" Meenal ta durƙusa za ta ɗauki hularta sai Nasir ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce
"Meenal karki kuskura ki taɓa hular nan"
Sadiya ta kalli yadda fuskarsa ta sauya lokaci guda ɓacin rai ya baibaye fuskarsa.
Meenal É—agowa ta yi da mamaki tana kallonsa kowa ma shi yake kallo hatta Momi sai da ta ji shayin yanayinsa ta ce
"Kai Nasir lafiya kuwa, ya haka yarinya da hularta kuma ka hana ta ɗauka?" ,Sadiya kuwa har fuslarta ta jiƙe da hawaye ta san shikenan hukuncin kanta zai sauke tabbas ita dai tana ganin jalala a gidan aurenta sai dai ta san duk wanda ya jura wahala ko ƙalubale a rayuwa to tabbas watarana nasara za ta zo, watarana zai taka tudun tsira, saboda hausawa ma suna cewa mai haƙuri yakan dafa dutse, duk wanda ya yi haƙuri zai samu sakamako duk daren daɗewa.
Nasir ya fara magama cike da ƙaraji tamkar ba da Momi yake magana ba ya ce
"Momi ana batun kisan kai ne fa wannan abubuwan da muke yi gabaÉ—ayanmu ba aikinmu ba ne"
Momi a tsorace da lamarin ta c
"To aikin su waye"
Ya ce
"Aikin hukuma ne mana, hukuma ce ya kamata ta yi bincike don tabbatar da gaskiya, wannan lamarin dole sai hukuma ta shiga" Ya faÉ—a yana saka hannu a aljihu ya fito da waya, Momi dakyar ta haÉ—iye tsoron da ta dirar mata ta ce
"Kai haba dai Nasir wace hukuma ana zaune lafiya, ai abu ne na gida, da Sadiya da Meenal ai duk ƴan uwana ne ba kishiyoyi ba ai an zama ɗaya, in zama ya haɗa da aure da haihuwa ai sai an ruguma haƙuri da dangana"
Meenal ta karɓe da faɗin
"Ai dama abin bai kai nan ba" Suka faɗa kowa yana tsoron furucin da Nasir ɗin zai yi game da maganar da suka yi, domin sun san muddin ya sako hukuma su ne a ciki, domin daga an cika bincike su za su kwana a ciki shi ya sa suke ƙoƙarin naɗe tabarɓar kunya da hauka. Sadiiya ta ce
"Ni wallahi na amince a kira hukumar saboda in har za a yi bincike za a gani gaskiya"
Safiyya ta ce
"Ke Sadiya ya ana so a kashe wuta kina rurata, shi fa bincike ba shi da wata rana ko da a addini"
Sadiya ta ce
"Addini ma ba irin wannan binciken ya hana ba, amma ni dai in har za a cire zargin da ake min to na yarda a saka hukuma"
Nasir ya ce
"In dai hukuma ce an saka ta ma an gama don ni ba zan iya wannan abin ba, ina zamana lafiya a zo ake jaza mini gwara...
Momi ta ce
"Nasir ni ai tamkar mahaifiyarka nake, kuma Sadiya ai yarinya ce magana ta ya dace ka bi kawai a kashe maganar a gida ba sai an fitar ba wani ma ya ji, kawai Sadiya ta karɓi kuskurenta"
Sadiya ta ce
"Wallahi ni dai ba zan taɓa karɓar aikin da ba ni na aikata ba, kawai a saka hukumar don ba na so a zo a ɓata mini suna ana cewa na yi yumƙurin kashe kishiyata saboda kishi ko kuma na ɗauki hularta zan mata asiri in raba ta da miji amma in hukuma ce in har jna da gaskiya za ta wanke ni"
Momi a zuciyarta ta c
"Wannan Æ´a Æ´ar bala,i ce, neman since mini zani a kasuwa take dole na samu mafita tyn kafin ranar jin kunya ta bayyana'
A fili ta ce
"Lallai Sadiya dama haka kike da kafiya da taurin kai? To mu ba damu ba ni ba tsohuwar banza ba ce ba zan je ina yawon bin hukuma ba duk su ƙwace mini kuɗi a karshe babu biyan buƙata"
Sadiya ta ce
"Ai ba kowace hukuma ba ce take karɓar kuɗi akwai wanda gaskiya kawai za su fitar"
Meenal ganin Nasir yana bin Momi da kallon kamar bai yarda da ita ba da take maganar rashin kai wajen hukuma da sauri Meenal É—in ta ce
"Wai mene ne ake ta jayayya to a je wajen hukumar ma wane shegen yake tsoron ra mutu bare ta yi rai," Ta faɗa tana kallon Momi da ta mata alama da ido a kan ta ɗauke hularta ta ƙara sunkuyawa Nasir ya hana ta ɗauka a karo na biyu sai Momi ta sunkuya da kanta za ta ɗauka da sauri Nasir ya hana ta ɗauka yana faɗin
"Ai babu wanda zai taɓa hular nan sai hukuma sun zo"
Momi da sauri ta ce
"To uban mai zai haÉ—a hukuma da hula?"
"Nasir ya ce na gaji da wannan jayayyar da ake yi gwara a je wajen hukuma kawai ta nan ne za a tabbatar da gaskiya, kuma wannan hular babu mai taɓawa, hukuma ne kaɗai za su yi aikin su, za su tabbatar da mai laifi za a su gane idan har Sadiya ce ta kawo hular za su gane idan kuma Meenal ɗin ce ta shigo ɗakin da kanta ta jefar da hular shi ma za su gano" Gaban Meenal ne ya bada saurin rasss aka fara kallon kallo a tsakaninsu
Nasir ya ci gaba da magana babu alaɓun wasa ko sasaauci ya ce