Sashe 14
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ibrahim ne ya musu sallama ya ce zai je ya kwanta, kasancewar dai yaƙe yake musu don kar su fahimci yana cikin damuwa, yana zuwa part ɗinsa ya shiga ya kulle, bai watsa ruwa ba kasancewar bai daɗe da yin wanka ba, jallabiyar jikinsa ya cire ya saka sleeping dress masu laushi ya kwanta tare da yin addu'a. Bayan ya shafa addu'ar ya shiga tunanin mafitar da yake a kan lamarin Jidda don a gobe ba sai jibi ba ya yi wa kansa alƙwarin sai ya je mata da kalmar so kuma son na aure!.
Tunanin wani abu ne ya faÉ—o masa hakan ya sa ya É—auki wayarsa ya shiga kiran Abeed abokinsa bayan ya É—auka yana ta masa surutu Ibrahim ya ce
"Dalla malam ka tsaya na faÉ—a maka abin da ya kawo ni, ka tsaya kana ta zuba kamar lalataccen famfo"
Abeed ya ce
"To dama ai kamar jiran kiranka nake ka san maganata ni da kai bata ƙarewa" Banza ya masa akan abin da ya faɗa don ya san kawai surutu ne zai cika shi da shi kp ya ringa bashi labarin ball ɗin da aka ci shi kuma yanzu ba wannan ne a gabansa ba, don ba ya so ma ya faɗawa Abeed ƙudurinsa gudun ya masa dariya ko ma ya ce sai ya bishi wajen Jiddar.
Cike da ƙosawa da kalaman Abeed Ibrahim ya ce
"Ni tambayarka zan yi ko ka san wani mai wanda mutum zai shafa ya yi baƙi kuma ya yi muni?" Ya faɗa hankalinsa kwance don shi ya shiryawa faɗawa komai a kan Jidda.
Abeed jin babu alamar wasa a furucin da abokin nasa ya yi sai ya ce
"Man da za a shafa a yi baƙi da muni ko dai mai da za a shafa a yi fari da kyau?" Shi ma ya tambaya babu alamar wasa a maganarsa kamar yadda Ibrahim ɗin ya yi.
Shiru Ibrahim ya yi yana É—an nazarin kamar ba zai ce komai ba har sai da maganar Abeed ta katse masa tunani jin ya ce
"Magana nake maka ka ƙyaleni?" Wani yawu ya haɗiye yana fatan dai ba cewa zai yi ba a samun man ba ya ce
"A,a kamar yadda na faɗa maka mai wanda zai saka baƙi da muni, ka san dai ai ni dai in ba zabiya zan komai ba mai zan yi da fari, kyau kuma ni da indiyawa da larabawa ko za a samu bambanci bainwuce a ce ni bahaushe ba ne su kuma larabawa da indiyawa, to mai zan yi da kyau?"
Abeed ya ce
"Wai kana nufin kai ne kake neman wannan man da ka ambata mai za ka yi da shi?"
Maimakon ya amsawa Abeed tambayarsa sai ya ce
"Tambaya za ka min ko amsa min tawa tambayar za ka yi" Ya faÉ—a yana jin tamkar ya janyo shi daga wayar ya yi ta bugu har sai ya huce.
Abeed baki ya taɓe kamar Ibrahim ɗin yana ganinsa ya ce
"Kai malam ni ban san inda ake siyar da wannan man ba, to wai kai mai ya sa ma za ka shafa wannan man? Wane mai bada gurguwar shawarar ne ya baka shawarar nan, bayan kana da kyau wanda ƴanmata suke maka caaaa... Wani takaici ne ya cika Ibrahim jin abin da Abeed ya faɗa shi kuma a halinnda yake ciki yanzu gani yake ko wata mace aka alaƙanta shi da ita tamkar an ci amanar Jidda ne, wayar ya sauke daga kunne ya datse kiran haɗe da yin cilli da ita can gefe ya kwanta tare da juyawa wayar baya. Abeed kuwa dama ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, dama ya san hakan zai ta faru don ya san Ibrahim ya tsani maimaita tamabaya.
Washe gari ko da ya tashi bayan ya yi shirin fita office, don yau shi kaɗai zai tafi kamfanin don Abba ya ce zai zauna ne ya yi wasu rubuce -rubuce a kan kayan da za a shigo da su daga waje na kasuwancinsa wanda duk manyan kasuwanni da shaguna yawanci wajensa suke sarar kayan. Yau ba kamfanin wajen gidan su Jidda zai je ba, ɗaya kamfanin yin shinkafa zai je, duk ransa ba daɗi don a ganinsa idan ya doshi hanyar wajen gidan su Jidda ma ai daɗi zai jia ransa. Bayan sun kammala break fast ya fito riƙe da jakar wajen aikinsa da wayoyinsa, suna tsaye da Mummy tana jero masa addu'a mai wankin da ya ba wankin gwanjo jiya ya zo yana mai cewa
"Barka da safiya Hajiya" Ya gaishe da Mummy cike da girmamawa, bayan ta amsa ya juya ya ce
"Barka da safiya yallaɓai" Ibrahim ya ce
"Alhamdulillah, mu je in buÉ—e maka part É—in nawa ka saka min kayan, ya faÉ—a gudun kar ya bashi mukullin idan ya tafi kafin ya dawo Mummy ta tambaye shi kayan mene ne bakko guda a cike.
Bayan ya saka masa ya dawo ya mata sallama, kamar ya sani kuwa sai da ta tambaye shi kayan mene ne don Mummy tana da sanya ido a kan lamurinsa, duk da ya mallaki hankalin kansa amma tana lura da al'amuran da suka shafe sa.
Sanar da ita yanyi cewa wasu kaya ne da ya saya, yana mata sallama direbansa ya buɗe masa mota bayan ya shiga ma'aikatan gidan wanda suke wajen suna ta kawo gaisuwa cike da bashi girma yana amsawa, rufe masa ƙofat aka yi direban ya shiga ya tada motar mai gadi ya buɗe suka fita ya mayar ya rufe yana musu fatan alkairi, ɗago masa hannu Ibrahim ya yi da yake yau motar da ya fita da ita mai farin glass ce ana gani.
Kamar jiya ma yau ya shirya wajen ƙarfe biyar na yamma, bayan ya fito wanka bai shafa mai ko turare ba kawai wannan kayan ya ɗakko ya saka kala ɗaya riga da wando baƙaƙe, ya kalle shi a madubi, duk da tsuffin kaya ne kasancewarsu baƙaƙe sai suka ƙara haska fatarsa hakan ya sa ya ji gabansa ya faɗi don tamkar ma kyau aka ƙara masa, da sauri ya cire ya ɗauki wata jar riga wacce daga gwiwar hannun ma ta ɗan fashe, ya saka baƙin wando, duk da a cukwuikuye suke amma dai ya ga sun masa kyau. Kai ya dafe ya koma bakim gado ya zauna yana tunanin ko dai baƙin mai ko na gawayi zai samu ya dishi farin fatarsa amma sai ya yi tunanin zai koma kamar dodo kuma ba ya so ma Jiddar ta ɗauka ko mahaukaci ne ta ƙu kula shi. Wayar da ya sa direba ya siyo masa tsohuwa key pad ita ya saka sim ɗinsa guda biyu ya ajiye nasa wayoyin masu tsada a kan madubin, dakyar ya samu takalmi yana fatan kar ta gane takalmin me tsada ne, wata hular sanyi ya ɗauka duk da zafin da ake ya saka amma sai ya ga ta yi kyau, ya ajiye ya ɗauko hularsa da yake sakawa da yadi, ya ɓata karin jikin hular ya saka ya danna a kan ta rufe wannan lallausan gashin kan nasa, sannan ya fito da kunnuwan waje sai ya zama gashi nan dai kamar wani wanda ba wayayye ba amma dai in mutum yana da hankali to yana kallon fatarsa kaɗai zai gane ɗan hutu ne bai saba da wahala ba.
Fitowa ya yi kasancewar Mummy yau ta fita gidana biki, bai san bikin waye ba amma ta ce masa ta tafi gidana biki, Daddy ma ya fita shi da wasu abokansa da suka zo wajensa.
Part É—insa ya rufo ya fito ya saka mukullin a aljihu yana gama sakawa ya ga mukullin ya faÉ—o sai a lokacin ya lura, ashe ajjihun a yage yake, a É—ayan ya saka sai ya ga babu yaga.
Tun da ya fito yake addu'ar Allah ya sa kar ya haɗu da wani daga ma'aikatan gidan, cikin ikon Allah har ya je bakin get bai haɗu da kowa ba, dama ko wajen ajiye motoci bai kalla ba kasancewar yau ba a ma managar mota. A hankali ya kama ƙaramar ƙofar ya buɗe amma sai da ƙofar ta yi ƙara ƙiiƙiii mai gadi da yake banɗakinsa ya ji ƙaran taɓa ƙofa dama yana shirin fitowa ne, hakan ya sa ya ƙara ƙaimi wajen sauri ya fito yana cewa
"Waye?" Lokacin har Ibrahim ya fita ya rufo ƙofar, yana fitowa ya fara sauri don ya san dole sai mai gadi ya leƙo, kuma baya son kowa ya ganshi, mai gadi kuwa da sauri ya ajiye butar hannunsa, ɗan taku ɗaya biyu ya yi yana leƙo hanyar cikin gidan ko zai ga wanda ya shiga amma bai hango kowa ba.
Da ɗan sassarfa ya nufi get ɗin ya buɗe ƙaramar ƙofa domin leƙawa ya ga ko fita aka yi tun da ba shigowa aka yi ba, Ibrahim da yake ta sauri don ganin ya bar layin nasu jin an buɗe ƙofar don ƙaran ta ziyarci kunnuwansa, da sauri ya raɓe daba jikin wata katangar wani gida yana leƙo mai gadin har ya gama kalle-kallensa ya koma ya rufo ƙofar, Ibrahim ya fito daga maɓoyarsa ya cigaba da tafiya yana fatan Allah bashi nasara a kan abin da zai je nema, yana fatan ya samu Jidda ta amince masa don ko a gobe in ta amince ya yarda a ɗaura musu aure!.
Tafiyar tashi bata je ko ina ba ya ji ya gaji kasancewar bai saba da wahala ba, napep ya tare ya shiga tare da faɗa masa inda zai kai shi, sai da suka kusa zuwa inda za a gangara ya ce mai napep ya samu wuri ya sauke shi, haka ya fito tare karɓar account no mai napep ya masa transper na kuɗinsa har da ƙari, mai napep sai godiya yake kamar ya ari baki, amma zuciyarsa cike da tambayoyi da wasi-wasi don ya tabbtar wannan ba ƙaramin mutum ba ne duba da yanayin maganarsa irim ta wayayye kuma mai ilimi, sanna kana kallonsa ka ga wanda yake zaune a hutu ba a wahala ba, sai dai yanayin kayan jikinsa ya sa kana iya jiyo warin abin gwanjo daga jikinsa.