← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 106

Sashe 5

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Burin iyayensa yanzu su ga ya yi aure domin su ga sun samu jika, kasancewar shi kaɗai Allah ya basu. Sai da ya gama shiryawa tsaf ya saka fararen wando da riga sai dai rigar tana da dogon hannu, kayan sun yi matuƙar amsar jikinsa ya ƙara komawa gaban madubi ya taje gashin ya kwantar da shi da brush kumb. Turaruka ya sake fesawa kafin ya ɗakko wayoyinsa da jakarsa da zai tafi kamfani kasancewar Daddy ya ce za su fita da wuri akwai baƙi da za su yi yau, za a tattauna a kan wasu kayan.

Wayarsa ya duba sai ya ga ƙarfe tara hakan ya bashi tabbacin ya sha baccin bayan komawarsa da gari ya waye, ganin miss call ɗin Daddy a ransa ya ce

"To fa! Daddy ina ga ya fita ma ya barni" Ya faÉ—a yana É—akko takalminsa a wajen takalma ya saka ya shiga sakkowa daga matakalar benen, a hankali cikin hutsuwa, Ibrahim mutum ne nutsatstse kuma yana da ibada.

Yana baro part ɗinsa direct part ɗin Daddy ya nufa, sai dai ya samu babu kowa sai ƙaran AC da tv a falon, fitowa ya yi ya nufi part ɗin Mummy da sallama ya tura ƙofar falon, sai dai babu kowa sai mai aiki tana goge -goge, cike da girmamawa ta shiga gaishe da shi ya amsa ko kallon inda take bai yi ba amma dai a muryarsa da ta saurara babu wulaƙanci kuma kowa ya san shi ko a bayan idanunsa suna yabonsa domin ya san daraja da muhimmancin ɗan adam.

Sai da ya je tsakiyar tangamemen falon ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu ya ce

"Ina Mummynah" Dakatawa ta yi da goge -goge ta ce

"Yanzu ta haura sama"

Iska ya hurar daga bakinsa ya ce

"Ki mata magana bana son haurawa saman" A ladabce ta amsa masa tana tahowa za ta yi w Hajiya Faty magana, ganin yana danna waya ta saci kallonsa a ranta tana kissima cewa tabbas duk macen da ta samu Ibrahim a matsayin miji haƙiƙa ta dace.

Kusan tare suka sakko da Hajiyar lokacin yana waya da Daddy Mummy ta ƙaraso ta zauna a kusa da shi, har ya gama wayar ya kashe yana kallonta da murmushi a saman fuskarsa ya ce

"Ina kwana Mummy nah" Dariya ta yi tana masa kallo mai cike da ƙauna irin ta uwa da ɗa ta ce

"Ka manta da asuba ma da kuka dawo daga masallaci ka gaishe da ni?" Ta faɗa tana dariya mai bayyana haƙora.

Shi ma murmushin ya yi ya ce

"To Mummy ko sau nawa É—a ya gaishe da mahaifiyarsa ai ba wani abu ba ne" Kai ta gyaÉ—a masa ta ce

"Mai za ka ci?"

Fuska ya shagwaɓe ya ce

"Ni ba na jin yunwa, tun da kuka rigani karyawa"

Mummy ta ce

"To Mu'azzam rigimamme, ai kai tun da sarkin bacci ne waye zai jira ka yunwa ta masa lahani, Daddyn ka ma da ya ce za ku fita gajiya ya yi da maka waya ya ce in ka tashi ka bi shi"

Yana É—an yatsina fuska ya ce

"Yanzu na kira shi ya ce yana kamfanin siminti kin san baƙin nan da za a yi magana da su ba ƙaramin kaya za su saya ba"

Haka suka ci gaba da tattaunawa ta zubo masa abincin ya zauna a kafet ya ci ba wani da yawa ba, dama dankali ne da wainar ƙwai sai shayi da ya sha shi ma kaɗan. Bayan ya gama ya mata sallama ta masa addu'a ya fito riƙe da jakar da wayoyinsa, ya samu an wanke gabaɗaya motocjn da suke wajen an goge sai sheƙi suke, direba da sauri ya matso ya karɓi jakar ya saka a baya yana gaishe da shi da girmamawa ya amsa, da kansa ya buɗe bayan ya shiga ya zauna direban ya rufe masa marfin ya shiga ya tada motar mai gadi ya wangale musu tangamemen get ɗin suka fita yana ɗaga musu hannu ya mayar da ƙofar ya rufe.

Sun haura titi suna tafiya sai karatun qur'ani da yake tashi a ciki, wanda duk direbobin sun sani idan Ibrahim ne a mota ba a kunna masa waƙa. Sun kusa ƙarasawa kamfanin inda direban ya gangara gefen titi kasancewar ba a farko bakin titi kamfanin yake ba sai an gangara.

Gangarawar da direban ya yi ya fara tafiya kaɗan akwai akwai wani wuri da ruwa ya ɗan taru da yake wajen daga gefen car wash ne da alama ruwan wajen ne ya ɗan gangaro, wasu ƴanmata guda biyu sun taho ɗaya tana ɗagawa wani napep hannu, direban cikin rashin sani tayar ta shiga cikin ruwan, sai ruwan nan ya fantsala bai yi masauki a ko ina ba sai a jikin ƴanmatan nan guda biyu, farar ita kawai ruwan ya fatsu da jikin takalmin ta ne, inda baƙar kuma gabaɗaya ruwan ya ɓata mata rigar jikin ta.

Direban ne cikin nuna rashin jin daÉ—in abin da ya yi ya ce

"Subhanallah" Ibrahim da yake danna waya ya ɗago shi sai lokacin ma ya ga abin da yake faruwa, amma sai ya rasa ma mai zai ce. A waje kuwa Aliya ce cike da masifa ta danƙaro wani ashar mai gunna ta yi tana kallon motar ranta yana matuƙar ɓaci ta ce

"Wannan daga gani ƴan Allah baku mu samu ne, wato karere masu cin arziƙi don babu yadda za a yi wanda ya taka arziƙi ya san darajar wannan kyakkyawar motar ya saka ta a cikin ruwan caɓali" Ta faɗa tana kama tsantsa, yayin da direban ya yi parking a gefe yana neman izinin Ibrahim a kan zai fita ya basu haƙuri. Ibrahim ne ya ce

"Sai ka kula ka ga Daddy yana kirana tun ina gida, gashi ka zi ka janyo wannan duk ta cikawa mutane kunne da hayaniya" Da to ya amsa, ita kuma Aliya kasancewar bata ganinsu da yake glass ɗin baƙi ne baka ganin wanda yake cilin motar.

Jidda wacce take kallon rigar jikinta yadda ruwan nan ya ɓata, fuska ta ɓata ba tare da ta ce komai ba tana tunanin yadda za ta koma gida ba ta sauya kaya saboda duk sun jiƙe, kuma gashi makarantar fa za su je exam za su shiga.

Direban yana fitowa tun kafin ya buÉ—e baki Aliya ta fara zaginsa tana cewa

"Ai dama na san sai dai direba wanda ba a gaji arziƙi ba kuma ba a san darajar kuɗi ba, shi ya sa kake zunduma wannan kyakkyawar motar a ruwa marar kyau, da a ce ma kuɗi ne za ka biyani ladan mata min takalmin da ka yi da ba haka ba, to yanzu dai na san haƙuri ka fito ka bani kuma wallahi ina so ka sani ko za ka tafi tsirara sai ka biyani diyyar ɓata min takalmi" Ta faɗa tana ɗaga jijiyoyin wuya, shi kuma direba ya dage sai bata haƙuri yake kamar zai ari baki ya ce

"Haba baiwar Allah, yanzu ki kalli ƴar uwarki ita ce aka yi wa abin da ya cancanci a bata haƙuri, kalli yadda aka ɓata mata jiki amma ke da ruwan ma kaɗan ne ya taɓa ki kike wannan abin" Jidda ganin suna hayaniya ta ce

"Kai Aliya dan Allah ki yi haƙuri mana, kin zauna kina ta ɗaga jijiyoyin wuya a kan wannan abin ƙanƙ... Hannu ta ɗagawa Jidda ta ce

"Dalla malama rufewa mutane baki, ana maganar waɗanda suka san ciwon kansu a kan haƙƙi ai ke bakya saka baki ba, ni idan ni ya ɓatawa kaya kamar yadda ya ɓata miki da tuni na sharara masa mari" Da sauri direban ya kai hannu ya dafe kumatunsa tamkar dai an mare shin.

Jidda kuma ranta ne ta ji babu daÉ—i jin an ce mata bata san ciwon kanta ba, kuma dama ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya.

Aliya ce ta ɗaga hannu ta miƙawa mutumin a kan ya bata kuɗi, ɗari biyun da ta rage ya fito da ita ya miƙawa Jidda, yana cewa

"Baiwar Allah ki karɓa ki saya omo ki wanke kayan da na ɓara miki" Kafin ya kai kuɗin saitin Jidda Aliya ta saka hannu ta warce tana cewa

"Matsiyaci wai ɗari biyu, to na karɓe dama an ce sata a gidan ɓarawo rance ce, kuma raba arne da makami ibada ne" Ta ce tana saka kuɗin a jakar hannun ta.

Jidda ce ta buÉ—e baki ta ce

"Bawan Allah da baka wahalar da kanka wajen bayar da kuÉ—inka ba, da ka bari za su maka amfani amma ka É—auka ka bayar, kuma ai kowane É—an adam ajizi ne sannan yana iya yin laifi" Kai direban ya shiga gyaÉ—awa jin maganar hankali da hikima duk abin da ake yi Ibrahim yana kallonsu ta glass daga cikin motar.

Ya yaba da hankali da nutsuwar Jidda, sannan ya lura ta san daraja da muhimmancin É—an adam kamar yadda shi ma ya sani.

Aliya kuwa ta wuce Jidda tana aika mata harara a inda da za ta wuce ta saka hannu ta daki bayan motar, napep take tsayarwa amma bai tsaya ba hakan ya sa ta tsallaka titin ta koma ɗaya ɓangaren, a nata tunanin ta tafi ta bar Jidda don ba za ta juri har sai ta jira ta ta koma gida ta sauya kaya ba, ba ma wannan ba ita a rayuwa ta tsani take tafiya da Jidda kasancewar Jidda baƙa kuma mummuna a zahiri Jidda bata da wani kyau, baƙa ce tana da faɗin fuska sannan tana da matsakaicin tsawo, tana da manyan idanu sai daj hancinta gajere ne kuma mai faɗi. Saɓanin Aliya da take fara tas kyakkawa ajin farko, tana da tsayi sannan tana da doguwar fuska dogon hanci wanda ake yi wa laƙabi da kamar biro duk wani abu da ya danganci kyau Aliya tana da shi wannan dalilin ne ma ya sa take ganin ta ciri tutar da sai ta zaɓi miji ta darje, miji ma na nunawa sa'a mai hannu da shuni wanda take ganin ko da ɓarawo ne in dai yana da kuɗi kuma yana da kyau to fa ta ga mijin aure don shi ne zaɓi kuma burinta.
Chapter 5 · 0% Book details