← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 106

Sashe 77

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bani hanya in wuce, sannan ki fito da duka abin da kika san mallakin ki ne daga kicin ɗin ki ajiye a gefe guda, daga an gama haɗa miki naki kicin ɗin sai ki mayar can" ,Yana kaiwa nan ya raɓa gefenta ya wuce, ita kuma Meenal ta saƙala hannunta a kafaɗarsa shi kuma ya saƙalo hannunsa wanda babu kofin ya riƙe ƙugunta suka tafi ɓangaren Meenal ɗin.

GIDAN SU ZALIKA

Gabaɗaya Mamy ta gigice hankalinta ya tashi ji take tamkar zai gushe mata domin abu ne da take gani tamkar ba a zahiri ba addu,a take a zuciyarta Allah ya sa mafarki take, domin sai hakan ya fi mata sauƙin rayuwa a ce wannan abin a zahiri ne. Juya kwallin take a hannunta tabbas pills ne, wato maganin hana ɗaukan ciki. Hannunta yana karkarwa ta buɗe kwalin ta ga duk an ɓalli maganin alamar an sha kenan wato an yi amfani da shi.

A fili ta furta
"Allazina iza asabathum musibatun ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un"A take ta ji wasu hawaye masu zafi suna zubowa daga kwarmin idanunta zuwa dakalin fuskarta, kuka take sosai marar sauti ko ta ji sauƙin abin da take ji a ranta, yau ita ce da matsalolin gidan miji sannan mijinta ya yi watsi da ƴaƴansa tamkar ba ya raye, ya bar mata ragamar komai kuma duk da tana iya bakin ƙoƙarinta amma sai da aka fara samun tangarɗa a lamarin tarbiyar a fili ta furta

"Ina godiya a gareka ya ubangiji da wannan jarabawar, ya Allah ka bani ƙarfi da ikon rungumar duk wata jarabawa da za ka jarabceni da ita, na san ka na ji kuma kana gani ya rabby ka kawowa baiwarka mai rauni ɗauki bani da tsumi bani da dabara" Ta faɗa tana rushewa da wani sabon kukan, ta jima tana kuka har sai da ta ji zuciyarta ta ɗan saki, duk da ta san abu ne mawuyaci wannan mummunan dafin ya fita daga zuciyarta amma dai tana fatan Allah ya yaye mata domin shi babu abin da ya gagare shi.
Maganin ta je ta sanya a drower É—inta, ta dawo ta É—auki jakar ta mayarwa Zalika É—akinta wace har lokacin tana ta shan bacci abinta.

Da safe ta je ɗakin Zalika ta same ta ta fito wanka kana zaune gaban madubi tana shafa mai sannan ga kayan da ta fitar za ta saka a kan gado a ajiye. Ta rufe ƙofar ta je ta samu waje ta zauna bayan ta yi sallama Zalikar ta amsa tana cigaba da abin da take.

Mamy ta ce

"Zalika wajenki na zo ina son magana da ke" Zalika tana shafa powder ta ce

"Ok Mamy" Sai da ta kammala ta zo ta saka kayantw sannan ta zauna a kusa da Mamy tana danna waya.

Mamy ta ce

"Bani jakar can taki zan yi wani abu" Gaban Zalika ya buga kasancewar ta san akwai maganinta a ciki kuma ba za ta so Mamyn ta gani ba. Tana É—an nuna alamar tambaya ta ce

"Mamy jakata kuma mai za ki yi da ite?" A nan ne Mamy ta ji wani abu kamar kibiya ya caki zucuyarta, domin kuwa hakan yana nuni da cewar maganin ne Zalika bata so ta gani, hakan yana nuni da cewar Zalika tana neman maza, duk da Mamy ta san a jakartw ta gani amma zuciya irin ta uwa gani take ba maganin hana ɗaukan cikin ba ne duk da ta san haka ne amma so takr ta buɗe idonta ta ga mafarki ne hakan zai zama mafi sauƙi ga ruhinta.

Mamy tana danne abinda take ji ta ce
"Mene ne a jakar da na ga kin razana? Ba handout ne da biro da wasu abubuwan amfani na makaranta ba, mene ne baƙo a ciki, ko kin manta tun kina nursary ne nake haɗa miki school bag ɗinki idan kin dawo ma ni nake adana miki ita yaushe abubuwan suka sauya kuma" Zalika tana ɗan diriricewa ta ce

"No babu komai Mamy kawai dai ina sauri ne na je na yi break fast sannan ina da lacture ne ba na son na makara" Idanun Mamy suka cika da ƙwalla tana kallonta ta fito da kwalin hannunta da ta ɓoye ta buɗe tafin hannunta gaban Zalika ne ya buga da ƙarfi tana kallon kwalin hannun Mamy inda jikinta ya ɗauki karkarwa tana ƙoƙarin baɗa laɓɓanta don ganin ta ce wani abu sai dai gabaɗaya alamomin rashin gaskiya sun bayyana a gare ta a inda Mamy ta gama fahimtar cewa tabbas ba mafarki take ba Zalika dai ƴarta tallin tal guda ɗaya ƴa mace wacce daga ita bata da wata ƴa macen sai Mubin ita ce ta san namiji, namijin ma ba mijin aurenta ba namijin titi shin zarginta gaskiya ne ? Idan ba gaskiya ba ne da mai zalika za ta kare kanta?

A take zuciyar Mamy ta shiga raya mata

'Lallai akwai aiki ja a gaban iyaye mata wajen sanya idanu a rayuwar ƴaƴansu yanzu a ce har yarinya tana iskanci a waje amma uwarta bata ankara ba, shin ina fitar budurci da ake gane cra wannan ne karo na farko da yarinya ta fara sanin ɗa namiji? Amma a ce uwa bata lura ba duk da kasancewata uwa mai sanya idanu a rayuwar ƴaƴana amma har abu ya yi nisa ban sani ba, kenan wayon ƴaƴan yanzu har ya kai su ɓoye abin da babba zai kasa ganewa!

Mad about you
Delina de merly
My way intense
Gucci guilty men
Vanilla 28 kayali
Khamrah
I want choo
Creed aventus
Amber oud
Sugar baby
Club de nuit
Olympea
Stronger with you
Reef 33
Dior sauvage
212 VIP man
Blue de channel
Pink shiffon
Jadore
Bombshell
Pure seduction
Versace bright crystal
La vie est belle
Versace Eros man

*🎉 PROMO NA ƘARSHEN SHEKARA GA MATA! 🎉*
*Ki bar tsohon shekara da matsala, ki shiga sabuwa da gyara!*

Mun yi sabbin kaya don nuna soyayya da kulawa ga wanda suke son mallakar É—aya daga cikin waÉ—annn abubuwan ko kuma duka.

*Ga kayanmu masu inganci da kike bukata:*

1️⃣ *Maganin Matsi Gam-Gam* Don matsi 1500 maimakon 2500
2️⃣ *Maganin Sanyi* Yana kawar da dukkan nau’in infection da wari, ƙaiƙayi, ƙuraje rikicewar al,ada 2500 maimakon 4k.
3️⃣ *Sabaya 3 in 1* Gyara breast, hips sannan tana gyara jiki 5k maimakon 7k.
4️⃣ *Maganin Gyaran Breast* Yana ciko da breast, ga masu shirin yin yaye da kuma wanda breast nasu yake buƙatar gyara 3k maimakon 4500.
5️⃣ *Daka* Tushen ni’ima 1500 maimakon 2500.

🎁 PROMO NA MUSAMMA
Ranar ƙarshe 31 ga Disamba, 2025

Ki gyara jikinki, ki faranta ran mijinki, ki shiga sabuwar shekara da armashi.

MAMAN AFRAH
09025576222

https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=hqrt1

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣4️⃣

JIDDA

Da matuƙar tashin hankali a tattare da ita take faɗin

"Lafiya mai ya faru?" Ta faÉ—a duk ta diririce saboda yadda ta ga mijin nata hankalinsa a tashe. Bai bata amsa ba don hankalinsa yana ga wayar da yake amsawa sai ta ji yana faÉ—in

"Gani nan Mummy" Yana gama wayar ya yu hanyar fita daga ɗakin cikin sauri lura da ta yi kamar hankalinsa ya bar jikinsa ta yi saurin riƙo rigarsa ta baya, tare da yin sauri ta sha gabansa suna fuskantar juna tamkar za ta saki kuka ta ce
"Ina tambayarka ko lafiya amma shi ne baka faÉ—a min ba" Kallonta ya yi sai kuma ya ga ta bashi tausayi hannunsa ya kai ya shago gefen fuskarta ya ce
"Ki yi haƙuri hankalina ne ya tashi, Mummy ce ta ce Daddy ya yanke jiki ya faɗi " Cike da tashin hankali ta ce
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ƙofar ya buɗe suka fito dagaɗaya ta ga ya fice a hayyacinsa, suna sakkowa ƙasa ya nufi hanyar fita Jidda ta ce
"Ka jirani in ɗakko hijabina" Bata jira cewarsa ba ta yi hanyar ɗakinta sai gata ta ɗakko hijabi a hannu a falon ta shiga sakawa tana gama sakawa sai ta ga Baba Kuluwa riƙe da plates za ta shiga kicin ta buɗe baki ta ce
"Baba zan fita za mu je gidan Mummy" Baba Kuluwa ta ce
"Lafiy Hauwa'u" Jidda ta ce
"Daddy ne ba ya jin daɗi" Fatan samun lafiya ta masa Jidda tana juyawa sai ta ga Ibrahim ɗin ba ya nan da sauri ta fita ganin ya bar ƙofar ma a buɗe. Ko da ta fita ta same shi har ya shiga mota, tana zuwa ta ce
"Ka ba direba ya kaimu na ga kamar ba za ka iya tuƙin ba" Cikin sanyin murya ya ce
"Zan iya" Bata sake magana ba ta buɗe ta shiga mai gadi da suke zaune suna hira da sauran ma'aikatan gidan ya tashi buɗe musu get kowa yana ɗaga musu hannu cike da girmamawa suka fita, gidan Mummyn suka kama hanya ko magana Ibrahim ba ya yi kasancewar jin muryar mahaifiyarsa da ya yi tana kuka a waya ƙaran wayarsa da take ajiye a gefe ne ya sanya Jidda ɗaukan wayar ta miƙa masa ganin sunan Mummy da sauri ya danna ya kara a kunnensa, ji ya yi Mummy tana faɗa masa sun tafi asibiti adirshin asibitin ta faɗa masa don haka ya juya kan motar suka kama hanya.
Chapter 77 · 0% Book details