Sashe 24
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah tsare" Ko amsawa bai yi ba ya nufi ƙofar yana sauri so yake ya cimma Alhajin da Malika ta ce yana jiranta a waje ya je ya masa maganar aurr cewa ya fito za a yi aure.
Malika ko da ta fita ta samu Alhajin yana jiranta a mota tana wani yauƙi da rawar kai gaɗe da girgiza jiki domin yanzu ta gane hakan ne yake ɗauke hankalin maza ƴan iska har su kai ga bata kuɗi ta magance matsalarta, Alhajin kuwa wanda ya haife ta ya washe baki haɗe da miƙo hannu ya buɗe mata ƙofa ta shiga yana mata kallon ƙwaf tana magana tana iyayi ya ce
"Sai ina?" Kallonsa ta yi cike da masa wani kallo ta ce
"Sai inda muka saba zuwa" Haɓa ya sosa yana sakin shu'umin murmushi domin ya gane Hotel za su je, yana ƴar dariya ya ce
"Baki da dama Baby Malika" Suna cikin haka ta hango Baba ya taho yana ɗaga babbar riga da sauri ta ce su bar wajen, haka Alhajin ya ja motar Baba sai ƙurar ya tarar a ransa yana faɗin
' Za ka dawo ka same ni wataƙila ya je siya mata cakuleti ne, dole ka fito a yi aure kuwa ka ɗauki ɗawainiyarta' Ya faɗa yana kama hanya domun ya je wajen abokinsa su tafi.
Alhaji tun da ya ja motar suka tafi suna hirarsu, Malika tana jin yanzu ta samu sabuwar rayuwa ta huta da zama da yunwa ko kuma ɗauka ɗawainiyar kanta na abubuwan buƙata na rayuwa, tun da yanzu za ta bada mutuncinta a bata kuɗi a kuma mata duk abin da take so, shi kuma Alhajin yana ganin ya samu yarinya ɗanya sharaf tabbas a nasa tunanin ya tsinci damu a kala sai dai yana tuya yana mantawa da albasa wato akwai ranar ƙun dillanci domin duk abin da mutum ya yi wa ƴar wani shi ma sai an yi wa nasa ƴaƴan, shi yana ganin ya killace nasa ƴaƴa ya zo yana lalata da ƴaƴan wasu duk da su ma wanda ake lalatar da su da laifinsu don su suka siyar da mutuncinsu suka zubar da kima da darajarsu na ƴaƴa mata, domin ai sai bango ya tsage ƙadangare yake samun waje shiga!.
Baba tun da suka je gidan makokin basu samu ganin abokin abokin nasa ba, kaaancewar yana cikin gidan wajen wasu baƙi da suka zo haka suka samu waje a rumfa suka zauna suna ta hira ana zuwa ana gaisuwa. Har wajen sha biyu sannan suka samu suka ga abokin inda ya nuna jin daɗinsa da karamcin Baba na zuwa yi masa ta'aziyya duk da basu da wata alaƙa, bai san cewa cin banza ne ya kawo Baban ba wai gaisuwar Allah da annabi ba.
Har aka kira sallar azahar ba a kawo abinci ba, Baba sai doguwar hamma yake, idanun nan sun kaɗa sun yi jawur don hatta tuwon safe kaɗan ya ce yana tunanin abubuwan daɗin da abokin nasa ya faɗa cewa tun da ya je wajen gaisuwar ake sauke kayan motsa baki. Amma dai shi ban da ruwan roba da ya ga ana ta wadaƙa da shi a wajen bai ga komai ba, tun zuwansu daga an ɗan jima sai a fito da ruwan roba masu sanyi ana rabawa, mai raba ruwan ko da ya zo zuwan farko ya ba su Baba haka Baba ya karɓa ajiye a tunaninsa idan an fara kawo kayan daɗin zai sha ruwan idan ya ci tun fa lokacin babu komai a cikinsa ba ya jin ruwan ma zai samu wuri.
Sawu na biyu ma wani ya ƙara miƙo musu Baba ya karɓa ya ajiye suka zama biyu a gabansa, yana jiran tsammani, a rabo na uku mai rabawar ba miƙawa yake ba ajiyewa mutane yake a gaba ai kuwa ya zo ya ajiyewa abokin Baba yana shirin ajiyewa Baba ai kuwa Baba ya yi farat ɗaya ya ce
"Haba bawan Allah, ruwan nan kun kawo, kun sake kawowa tsakani da Allah dai ko shanaye ne mu ruwan da aka raba ya isa a ce ya kashe mana ƙishirwa, tun da muka zauna a wajen nan muke karɓar gaisuwa ana Allah jiƙansa muna cewa amin amma ku babu aikin da kuke sai ku shiga cikin gida ku jido ruwa kuna ba mutane, bakwa duba yadda idanun jama'a ya yi zuru-zuru haba ku tsagaita da bada ruwan nan tun da shi kaɗai za ku raba, in ba haka ba ni dai kar ka ƙara tunkaroni da ruwa na gabana ma ya isheni" Tun da Baba ya fara magana abokinsa Malam Lurwanu yake danne dariyarsa gudun kar ya saki dariya a wajen makokin a ce bai damu da mutuwar ba, duk da dai wajen dama gefe ne suke zaune kuma ana ɗan hayaniya ba a lura da abin da yake faruwa ba.
Mai raba ruwa cike da mamaki yake kallon Baba, hakan ya sa ya É—auki ruwansa ya bar wajen, Baba wanda ya kauda kai gefe yana muzurai, babu abin da yake tunowa sai abubuwan da abokinsa ya bashi labari da kuma abin da ya faÉ—awa Mama Habiba amma gashi dai wankin hula yana son kai shi dare.
Ko da aka tashi yin sallar azahar abokinsa yana masa dariyar ƙeta a ɓoye, aka idar da sallar da yake ba masallaci aka je ba a nan wajen aka yi jam'i shi kuma abokin da aka yi wa mutuwar suna can suna ta karɓar gaisuwar jama'a. Ko da aka idar da sallah Baba yake yi wa abokin masifa wai sai sun tafi gida a nan ya ce masa su dakata wataƙila ko an yi jinkirin kawo abincin ne, ana jimawa aka fara kawo abinci da nama kala -kala Baba ya zage ganin banza ta faɗi ya ci abinci musamman naman da ya ci ya yi yawa, lemuka ma sai da ya saka biyar a aljihu fanta, cola, mirinda nutrimilk lacasera. Duk a aljihun babbar riga ya zunduma su daga an miƙo masa lemo sai ya karɓe bakin nan washa-washa da sai wangale shi yake. Sai da ala'sar sakaliya suka yi wa wa wanda suka je dominsa sallama, abokin Baba sai jin Baba ya yi da za su masa sallama yana faɗin
"To Allah jiƙansa, Allah sa kwanciya hutu ce sai goben idan Allah ya kaimu da abin aro za mu dawo" Amsa masa aka yi ana musu godiya.
Lokacin da Baba ya dawo gida ya nufi É—akinsa ya ajiye lemukan nan, sai dai ciwon ciki yake damunsa tun a hanya ya fi zaton ko naman da ya ci da yawa ne ya saka masa ciki.
Wani murÉ—awa da cikinsa ya yi sai banÉ—aki yana can ya fito ya sake komawa zuwansa uku Sumy da take É—akin Mama ta ji yana zabga mata kira yana faÉ—in
",Sumayya kawo min maganin gudawar nan da kika siya da safe"
*JIDDA*
Suna can ita da Salama suna ta hira abinsu, Kasim kuwa tun da ya faɗawa Ummarsa cewa ga yadda Babansa ya ce haka ta bashi baki a kan cewa ya yi haƙuri ya bar maganar don ya san cewa Babansa kaifi ɗaya ne ba zai lamunci wani abu ba bayan wanda ya yanke hukunci a kansa, sannan zai ga kamar ƙarya ce idan aka ce sai an kai a mota.
So yake ya sanar da Aliya halin da ake ciki amma kuma yana tsoron abin da zai biyu baya, saboda ya san sai ranta ya ɓaci amma duk da haka ya san ai umarnin mahaifinsa gaba yake da nata, hakan ya sa ya koma ɗaki ya kwanta yana ɗan jin fargaba yana fatan kamar yadda ta yi farincikin kayan saka rana wannan ma ya faranta mata rai fiye da wancan lokacin!.
Aliya dai ta gaji da zumuɗi ta ɗaga waya ta kira Kasim, Kasim ganin kiranta sai da gabansa ya faɗi da ƙarfi har kiran ya tsinke bai samu zarafin ɗagawa ba, kiran ya shigo a karo na biyu har ya tsinke bai ɗaga ba, sai faman kallon sunan ta da yake a saman wayar. A karo na uku ya yi ta maza ya ɗaga yana ɗagawa ya tsinci muryarta cikin farin ciki tana faɗin
"Hello" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, sai lokacin ya ji hankalinsa ya kwanta wannan alama ce ta nasara wato ranta bai ɓaci ba sanadin kai kaya a baro bayan ya mata alƙwarin kai kaya a mota kamar yadda ta buƙata, kuma da alama kayan ma sun birgeta hakan ya sa cike da ƙarfin gwiwa ya ce
"Barka da wannan lokaci amarya kuma sarauniyar zuciyata" A can ɓangaren Aliya ta murmusa lokacin da suke wayar suna saman wani katakonda suka taka ita da Amatallahi a ɗakin Umma suna window suna jiran ganin masu kaya don su ganewa idanunsu.
Cike da farinciki ta ce
"Na'am sarakin zuciyata" Ji ya yi kamar ya taka rawa don murna. Suna magana Amatulllahi tana musu tsiya wai basa kunyarta a daidai nan ayarin masu kawo kayan Kasim suka yi wa gidan su Aliya tsinke!. A kan idon Aliya mai tura baro mai ɗauke da akwari biyu da ƙaramin kit ya taho inda mutanen suna biye da shi, wani ihu Aliya ta saki wanda ya ɗauki hankalin Amatullahi ta juya ɓangaren da ta ga Aliyar ta kalla a take ta yi arba da abin da Aliya ta gani, Kasim kuwa ihun da Aliya ta yi sai da ya cika masa kunne ya fara tunanin mene ne wannan wanda ya saka ta farinciki lokaci guda kafin ya gama wannan tunanin muryar Aliya ta dawo da shi daga tunanin ta hanyar faɗin
"Kayan Jidda a baro aka kawo akwati biyu da kit" Take faÉ—a tana tuntsurewa da dariya, mamaki al'ajabi da kuma tsoro suka É—arsarwa Kasim a zuciya mamaki na farko shi ne shin dama abu iri É—aya suka ti shi da mijin Jidda da yake ganinsa bashi da wani hali sannan kuma shi ma a baro ya aika lefen ko kuwa? Tsoron da ya ziyarce shi kuma yana tunanin shin kenan ita Aliya bata ga nata lefen ba dama, kafin ya samu wannan amsar tambayar da yake yi wa kansa sai ya ji Aliya ta ce