Sashe 89
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana iya jiyu yadda ake ta koke-koke a cikin gidan, amma son zuciya ya hana ta yi tunanin cewa, idan gawarta ce ko ta wani nata za a yi wa hakan ba za ta ji daɗi ba, shaiɗan ya hana ta fahimci aairi babu kyau saɓon Allah ne, ta kasa fahimtar haɗarin da yake tattare da neman biyan buƙata ta haramtacciyar hanya, wato aiki da maganar boka da kuma amfani da gawar da a yanzu babu abin da take buƙata sai addu,a da neman gafara sannan kowa yana iya zama gawa a kowane lokaci, da ciwo ko babu, babu jinkiri ga wanda lokacinsa ya yi sannan babu gaggautawa ga wanda lokacinsa bai ƙarasa ba!.
Zuwa wurin boka haramun, aiki da maganarsa ya saɓa da addini, sannan ba ta ma tunanin shi aure lokaci ne bare ma ƴarta tana da auren sun raina samun mijin ne da kuma matsayinsa, kuma hakan yana nuni da yin aure ta tilas domin shi wanda za a yi aikin a kansa tilasta masa za a yi, kuma akwai haɗari ga aiki da bokanci ko yin sihiri.
Da sauri ta zazzage maganin a tafin hannunta tana fatan Allah sa dai babu ita a suman da aka ambata mutanen za su yi tun da idan aka suma har ita yaya kenan.
Babu ɓata lokaci ta zage murya ta ce
"Malam Kalla" Tana faɗa ta shige tsakar gidan ta hura maganin gabaɗaya ya bi iska. Kamar almara take ganin kowa ya zube a inda yake ya sume, tamkar gawarwaki haka ta ga mutanen babu wani mai motsi. Daga can gefen wata tabarma ta hangi Abba da su Liman suna yashe tamkar gawar su ɗin ma. Ba ta hira komai ba ta nufi ɗakin Malam Kalla, malam kalla malami ne mahaddacin qur,ani sannna mai ruƙo da addini.
Ɗakin a cike yake da mutane matansa ne sai manyan ƴaƴansa amma kowanne babu bambanci da gawar domun duk sun sume. Yana kwance a miƙe zumbet an lulluɓe shi da zanen gado, yanayin yadda suke ya nuna ba a daɗe da yin rasuwar ba ma wataƙila ma yana rasuwa akan sanar a masallacin.
Ta na nufarsa gabanta yana tsananta faÉ—uwa sai dai ba za ta yi wasa da wannan damar da ta samu ba din ta san tana gama yin aikin komai zai daidaita su fara cin duniyarsu da tsinkena tsire. Ba ta tunanin su ko za su tsallake wannan rana ba su mutu ba tub da ajalin ba sallama yake yi ba, kowa mutuwar tana zuwar masa ne bagatatan.
Tana taugunne a gabansa ƙafafunta na karkarwa amma haka ta saka hannu ta buɗe gawar ta ganshi idanunsa a rufe ruf kamar mai bacci. Maganin ta buɗe daga leda ta saka yatsu biyu ta tsakuro, ta nufi hancin gawar za ta zuba sai dai me sai ta ga gawar kamar ta ɗan motsa, gabanta ya bada rass amma sai ta saka a ranta cewa tsabar ruɗanin da take ciki ne domin gawa ai ba ta motsi duk wanda ya mutu ya mutu.
Ƙara nufar hancin nasa ta yi ta ƙara ganin gawar ta ɗan motsa hannun gawar ne yake ɗan motsi amma kaɗan sai ka lura za ka gani, ɗan jim ta yi amma sai kawai ta ƙara nufar hancin gawar za ta zuba maganin sai kuwa ta ga kan gawar ya ɗan motsa Umma ta tsaya cak! Ta juya ta dubi ƙofar shigowar amma babu kowa kuma gidan shiru sannan har lokacin babu wanda ya ƙara shigowa gidan. Kallon mutanen ɗakin ta yi don ta tabbatar da cewa ita kaɗai take ganin gawar tana motsi ko akwai wanda yake tayata gani amma ta ga babu kowa sai ita kaɗai.
Kawai sai zuciyarta ta raya mata cewar gizo ne idanunta suke mata domin su hana ta aiwatar da ainihin abin da ta zo yi wanda ta samu wata dama, tana tono kuɗin da ta bayar na aikin sai kawai ta ajiye ledar a gefe ta saka hannun ɗaya ra riƙe hancin gawar ta nufi hancin da ɗaya hannun mai maganin.Kamar daga sama kuma kamar almara Umma ta ga hannun gawar nan mai motsi ya ɗago kafin ta gama tantancewa hannun gawa ya damƙe hannunta!
Tashin farko ta ji kufcewar fitsarin da ba ta shirya masa ba, a yadda take a tsugunne ta ji zaninta jagaf, ga tsananin tsoro da tashin hankali da kuma da na sanin yin wannan aikin tun da dai ta san gawa ba ta motsi amma ita bayan motsin da gawar ta yi ga shi har hannun ta ta riƙe.
Jan hannunta take amma sai ta ji tamkar an saka mayen ƙarfe domin gawar ta riƙe hannun gamgam kamar tare da hannun aka halicce ta. Umma abin ya fara wuce gona da iri domin abin ya fara wuce hankali da tunaninta, ita da ta zo don aiwatar da aiki a cikin ƴan mintuna amma ga shi wankin hula yana so ya kai ta dare.
Ganin abin ba na ƙare ba ne ta shiga ture gawar amma gawar tana ƙame kawai dai ta riƙe hannun Ummar ne. Umma ta fara tunanin kar fa asirinta ya tonu tun da dai sai ta ambaci sunan mamaci sannan kowa zai dawo daga suman da ya yi ga shi kuma yanzu gawar ta ƙi sakin ta kenan hakan yana nuni da tonuwar asirin ta ko yaya?.
Abu dai ya faskara!. Don yanzu Umma kokarin kwatar kanta kawai take ta ma saddaƙar cewa yiwuwar aikin da ta zo yi sai sa,a. Tana kiciniyar kwakwace kanta ta zubar da maganin hannun nata wanda za ta zuba a hancin gawar, amma ba ta shi take ba wannan lamari ya girmi tunanin ta.
Jan hannun ta yi da ƙarfi aikuwa sai ta ji gawar ta saka ɗaya hannun ta damƙi ƙafarta guda ɗaya shikenan sai Umma ta sare cewa asirinta rana dab da tonuwa, don ta san ida har wani ya shigo gidan wanda shi ba ta yi aikin watsa magani da shi ba to ta fara zargin zai ganta wannan yana nufin Abba zai san abin da ta zo yi kuma sakamaon ta ta sani ba sai an faɗa mata ba kuma kowa zai san mai ta zo aikatawa tun da gawar ba ta wani nata ba cw sannan mai ya kaita wajen gawa da har ta riƙe mata ƙafa da hannu!?.
Wajen kiciniyar ƙwaƙwace kanta ɗan sauran maganin da ya rage a ledar wanda take ganin shi ne ya rage mata tun da na hannun ya zube, tana rayawa a ranta idan ta samu kwace hannunta sai ra tura maganin a hancinngawar amma a kokarin ganin ta tsira ta ture ledar gabaɗaua ya zube dama ba wani yawa ne da shi ba don ta ga ledar ma iska ta matsar da ita daga kusa da ita ta yi can gefe guda. Kukan takaici ne na zuci wannn da ya fi na fili ciwo ya kufce mata, don tabbatar an kuma mace ta haifi mace wato asara dai ta wannan aikin ma an yi ta kamar yadda aka yi asarar aikin cokali, yanzu abu ɗaya ya rage mata yadda gawar za ta sake ta.
Addu,a ta fara son karantowa don ta ga yanzu ita kaɗaice ta rage mata amma addu,ar ta kasa ambatawa ko da a zuciya ne domin dama ba ta da ƙarfin gwiwar furtawa a fili.
BABA
Hankali tashe yake kallon yadda hayaƙi yake biyowa daga cikin store ɗin nasa wanda ya tabbatar da cewa karkaf kayan amfanjnsa ne a cikin ɗakin wannan abin daidai yake da karayar arziƙinsa a cewarsa kenan hakan ya sa ya takarkare ya zandama ihun da kowa na gidan sai da ya fito a sukwane domin yanayin yadda ya yi ihun tamkar wanda aka daɓawa wuƙa a ƙirji.
Ganin abin da yake faruwa sai kowa ya yi turus suna ganin wuta tana ci tamkar wanda aka kunna ta, Baba kuma sai miƙa hannu yake kamar mai neman sadaka duk ya gigice dama ga shi mai sarewa a kan abu barw kuma wannan yana gani ƙiri-ƙiri wuta tana cin store ɗin nashi da yake ji da shi wanda hatta iyalansa yana musu ƙauro. Zaman dirshan ya yi yana kuka wiwi tamkar an ce masa Kaka ce mahaifiyarsa ta mutu. Hafsat ce ta yi waje tana cewa.
"Gobara jama,a a kawo ɗauki" Lokacin har Mama Habiba da Mamar Sadiya sun fara ɗakko ruwa suna watsawa don yanzu hatta ƙofar ɗakin ta cinye. Samari ne suka shigo gidan wanda suke zaune a ƙofar gidan aka shigo ana ta zubawa wutar ruwa dakyar aka samu ta mutu, sai dai gabaɗaya ta ƙone komai na ɗakin ƙurmus. Samarin nan suna ta jajantawa Baba gobarar amma sai faɗi yake
"Ku kawo É—auki jama,a na taiyace na talauce wayyo ni" Ganin kamar ba a hayyacjnsa ba y a yake suka jajantawa matan gidan suka tafi sama gabaÉ—aya cikin Æ´aÆ´an babu wacce ta taimaka wajen kashe wutae kafin samarin su zo su ma matan daga Mama Habiba saj Mamar Sadiya ne kawai suka kaiwa wutar É—auki.
Mamar Sadiya da Mama Habiba ya ce
"Habiba ke da Talatuwa ku zo ku kamani ku kaini ɗaki, na ga ku ne kuka fi tausayina ku ne kaɗai kuka kaiwa wutar nan ɗauki, sauran kamar ma farinciki suke da faruwar hakan" Haka suka zo suna masa kama-kama duk ya saki jiki sai sharɓar kuka yake, sai da suna dab da shiga ɗakinsa kawai sai ya zauna kamar wanda aka turo ya kifa uban tagumi yana cewa
"Wayyo hatsina wayyo shinkafata da na san wannan ƙaddarar za fa faɗa musu da na daɗe da kaiku kasuwa na karɓi kuɗina" ,Ya faɗa yana face hanci.
Mama Habiba ta ce
"Haba Malam ina kake so ka kai imaninka ne ai baka da tsumi ko dabara a kan hakan, tun da Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru haka za ka rungumi ƙaddara...
Ko ƙarasawa bata yi ba ya hayayyaƙo ta da masifa yana faɗin