← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 106

Sashe 16

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tsorata ya yi ne da ya ji ƙaran horn, Allah ma ya kiyaye ban lura da shi ba ya taho" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har lokacin tana jin sanyin da ƙafafunta suka yi. Gefe kawai ta matsa tana jijjiga Kalifa don bata da ƙarfin halin furta masa komai, shi kuma ya ce

"Allah ƙara kiyayewa ake kula da yara" Yana gaɓa faɗar hakan ya ja mashin ɗin, jakarta ta koma ta ɗakko daga inda ta ajiye don ita dama wayar tata ma ko caji babu domin bata ma riƙe caji sosai shi ya sa bata tarki kiran Nasir ba, bare ma ta san ba ɗauka zai yi ba in ta kira sai in ya ba dama.

Tana nan tsaye a ƙofar gidan lokacin an fara kiran magriba wani mashin da ya karyo kwanar ta gani kamar daga sama ta hangi Nasir a bayan mashin ɗin, sai da suka zo har ƙofar gidan ya sauka daga mashin ɗin ya ba mai mashin kuɗinsa mai mashin ya ja ya bar wajen, Kalifa ne ya hau faɗin

"Abba, Abba, Abba" ,Kallo ɗaya Nasir ya musu ya ɗauke kai mukulli ya fiddo daga aljihunsa ya buɗe ƙofar gidan ya shige har da ɗan turo ƙofar, wani abu ne ya tokarewa Sadiya a maƙoshi saboda abin da ya yi wa Kalifa sai ta ji duk abin da ya mata bai mata ciwo ba kamar wanda ya yi wa ɗansa , abin na matuƙar damunta ita a nata tunanin ko da a ce da Kalifa ta zo gidansa bai kamata yake yi wa yaron haka ba, bare kuma ɗansa na cikinsa. Haka ta daure ta taka matakalar ƙofar gidan ta saka hannu ta tura ƙofar ta shigo gidan ita tsabar bata da nutsuwa ma ta manta da wani abu wai sallama haka ta shigo gidan kamar wanda dama Nasir yake jira sai ji ta yi ya ce

"Ke! Babu manya a gidan ko? Na ce manya sun ƙare a gidanku, idan ma akwai manyan to basu bada tarbiya ba gskiya tun da kike shiga gida babu sallama" Maganar ta mata ciwo sai abin ya zame mata zafi biyu wato ga mari ga tsinka jaka, saboda bai san darajarta ba ya barta wuni guda a titi amma ya zo yana ƙara mata wasu maganganun mararsa tushe.

Daurewa kawai take amma kuka neman ƙwace mata yake, sauke Kalifa ta yi don yanzu hankalinta ya fi karkata ga yin sallolin da suke kanta hakan ya sa da ta sauke Kalifan kawai ta yi gaba don yin alwala, shi ma Kalifan kamar ya san mai yake faruwa sai ya ja ya tsaya a ƙofar falon ya raɓe yake leƙen Nasir ɗin.

Inda ta cika butoci ta je ta ɗauki ɗaya ta yi addu'a ta shige banɗaki ta turo ƙofar, ta tsugunna tana kama ruwa kawai sai ji ta yi an banko ƙofar har sai da ƙofar ta gwaru da jikin bangoda sauri ta tashi tsaye don dama ta gama kama ruwan.

Juyowa ta yi tana kallonsa a tsorace ganinsa a fusace tamkar wani fusataccen zaki, kafin ta furta wani abu ya ce

"Wato ga ɗan iska ko saboda kin rainani ina faɗa shi ne kika yi tafiyarki kika barni in yi ta zuba ko?" ,Cikin sanyin murya da kuma ƙarfin da yunwa ta cinye mata ta ce

"Ka san dai a waje muka wuni ban yi sallar azahar ba bare la'asar kuma yanzu ana kiran magrib... Tun kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin

"To ina ruwana da sallarki, in ban da rashin tarbiya ina magana ki tafi wannan daga gani babu tantama gida kika ɗakko halayyar rashin tarbiya, dama ai an ce tarbiya daga gida take farawa, in ba don ni ba wa zai kwasa iyayenki ma da kin ishe su da Allah annabi Babanki ya sa na aure ki, don na ɗauke masa ɗawaniniya saboda yana so ya kawar da ke, ina faɗa a ko ina ban aure ki don ki zama abokiyar rayuwata ba na san aurena da ke ƙaddara ce baƙar ƙaddara ma kuwa, a yau idan na ga dama zan yanke igiyar aurena da ke kuma in auro wacce ta fiki komai don ke baki cika mace ba!."

Kallonsa take yadda yake magana cikin ɗaga murya, idanunta suka fara tara hawayen da take ta ƙoƙarin maƙale suka fara ambaliya a dakalin fuskarta, a take maganganun da ƙawarta Noor ta faɗa mata suka fara dawo mata, wanda take faɗa mata cewa take kataɓus wajen rama abin da Nasir ɗin yake yi wa iyayenta na cin mutunci tun da iyaye ai sun fi ƙarfin wasa tun da shi bashi da mutunci bai san shi ba. Jin kalamnsa kuwa ai ta tabbatar iyayen nata yake faɗawa magana, ai kuwa ta fara takowa daga cikin banɗakin sai da ta zo gab da shi ta tsaya ta ce

"Nasir" Da mamaki yake kallon ta jin ta kira shi a wani gadaranci ko dai ya kira hakan da muryarta cike da fitsara.

Baki ya saki yana kallon ta ta ci gaba da faÉ—in

"Duk abin da za ka yi ka tsaya iya kaina amma iyayena ba sa,anninka ba ne da za kake faÉ—a musu abin da duk ya zo bakin ka ba zan É—auki haka ba"

Haɓa ya riƙw cike da mamaki ya ce

"To mai za ki iya idan an sako iyayen naki ko kina da matakin ɗauka ne? Iyayen naki da basu damu da farin ciki da baƙin cikin ki ba ni fa a wajena baki da maraba da wacce aka min tallar ta ko aka bani sadaka"

Ita ma a harzuƙe ta ce

"Ko ma ya suke iyayena ne kuma ko ma ya suka ɗaukeni wannan tsakaninmu da su ne, ni dai gargaɗina na ƙarshe da kai kar ka sake cin mutuncin iyayena"

Idanu ya ƙanƙance ya ce

"GargaÉ—i? Sadiya ni Nasir ne kike yi wa gargaÉ—i kamar wanda bakin uwa ya kamani har wata mace za take faÉ—a min magana"

Bata bi ta kan tambayarsa ba ta ce

"Ni da sakakkiya a gidan nan banbamcin mu kaÉ—an ne, ko kaÉ—an baka darajani, tsakani da Allah kana gani na amma ka tafi bayan ka san gidan a kulle na wuni a titi ni da É—anka ko kishin iyalinka baka yi, duk namijin da ya san darajar kansa da ta iyalinsa ba zai wofintar da su su wuni a titi b...

Wani gigitaccen mari ya ɗauke fuskarta da shi, da yake marin ya je mata ne a bazata sai ta ji tamkar ba da hannu aka mare ta ba, marin da Kalifa ya gani ne ya sa ya ruɗe ya fashe da wani kuka ya yi kanta ya je bayanta ya ƙanɗame ta har lokacin yana kuka, bata kula Kalifa ba duk da kukan nasa yana taɓa mata zuciya. Tana dafe da kumatun da ya mara ta kalle shi idanunta taf da hawaye ta ce

"Ni ka mara Nasir?"

Kamar zai kai mata wani marin ya ce

"An mare ki fitsararriya ko za ki rama ne? Har ni za ki ce ban san darajar kaina ba, kuma wallahi sai na faɗawa wannan uban naki ya gargaɗe ki don zai iya zuwa ya ga gawarki matuƙar baki yi wa bakin ki linzami daga furta min kowace kalma ta zo bakinki ba" Yana gama faɗar hakan ya juya ya nufi falo, Kalifa ta ɗauka har lokacin yana kuka da alama tsorata ya yi da marin da aka mata tana ɗaukansa ya maƙalƙale wuyanta bata san lokacin da ta fashe da kuka mai sauti ba. Ta jima tana kuka mai cin rai kafin ta yi shiru ta goge hawayen, jin Kalifa ya yi shiru ya kwantar da kansa a kafaɗarta, sai ta duba sai ta ga ya yi bacci haka ta kawo shi falon ta kwantar da shi a kan kujera ta koma ta yi alwala ta zo ta kabbara sallah.

Lokacin Nasir yana bedroom, sai da ta yi azzahar da la'asar tana yi tana hawaye duk sujadar da ta kai sai ta faɗawa ubangiji damuwarta a kan ya magance mata, tana shirin miƙewa ta yi mageriba sai ga Nasir daga bedroom ɗin kamar an jefo shi, gabanta ya zo ya tsaya yana riƙe da wayarsa da take ringing da alama wani yake kira don wayar a handsfree take ma.

Kamar daga sama sai jin muryar Baba ta yi yana cewa

" Assalamu alaikum malam Nasiru mutumin kirki" Wani murmushin gefen baki Nasir ya yi kafin ya haÉ—e rai kamar Baban yana ganinsa ya ce

"Ni wallahi Baba ba na cikin yanayin da zan amsa sallama gabaɗaya raina a ɓace yake"

BuÉ—ar bakin Baba sai ya ce

"Sadiya ce ko? Wannan yarinya mai ya sa bata jin magana wai, haka fa ta kwaso jiki wai wuni ta zo gidan nan na korata ɗakinta da tsakar rana shi ne kuma da ta dawo ta ɓata maka rai" Sosai Sadiya ta ji duk ta muzanta dole Nasir yake mata abin da ya ga dama saboda mahaifinta shi yake bashi kowace dama, shi yake zubar da kima da darajarsa, shi ya sa ba ya siya mata mutunci bata san wane irin uba ne ta samu ba.

Nasir ba yabo ba fallasa ya ce

"Ai Sadiya bata san darajar miji ba ko kaɗan, ban da zagi da baƙaƙen maganganu babu abin da take a gidan auren ta, yanzun nan ta gama cewa ban san darajar kaina ba da ta iyayena" Ya faɗa cike da ɓacin rai, Sadiya jin har da ƙarya ya shirga bata yi mamaki ba da ya yi haƙuri ma in dai Baba ne a kan a samu matsalar da za ta koma masa gida ba sai da ƙarya zai mata faɗa ba.

Baba ya ce

"Bata wayar" Wani kallo Nasir ya mata yana wani ƙanƙance ido irin na fitsararru ya miƙa mata wayar tana ƙoƙarin danna wayar Nasir ya katse ta da faɗin

"Kar ki kuskura ki cire min waya a handsfree ki bari in ji, idan ma shi yake ɗaure miki tsantsa ki rainani" Yana gama faɗar haka ya koma kan kujera ya zauna tare da harɗe ƙafafu.

Baba ya ce
Chapter 16 · 0% Book details