← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 106

Sashe 34

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai ba magana nake miki ba Sadiya? Wato kin mayar da ni kare in yi ta haushi?" Cikin inda -inda ta ce

"Ci...ci...ciki ne da..." Wata wawiyar tsawa da ya doka ita ce silar tashin Kalifa da ya koma baccin safe sai kukansa ta ji,

Nasir ya ce

"Wato kin samu ciki shi ne kike ƙunbiya-ƙunbiya baki faɗa mini ba, wato ga Nasir ɗangote ko Nasir A A Rano shi ya sa za a ke mini haihuwa a kai-akai tun da ni me dukiya ne ko? Ɗan rufin asirin da Allah ya mini kike so sai kin kwantar da ni Sadiya ki tara min ƴaƴa tsufa ya hau ni, a zamana bani da kataɓus sai ƴaƴa to wallahi baki isa ba!" Ya faɗa yana nunata da yatsa, fitowar Kalifa ya sa ya kalli Kalifan yana sakin wani wawan tsaki, shi kuma Kalifan da sauri ya kauce daga hanyar da Nasir ɗin yake tsaye ya yi wajen Sadiya yana ɗan kuka tare da murza idanu.

Fuuuu ya juya tamkar zai tashi sama, ɗaki ya shiga jim kaɗan sai gashi da rigar a hannu haɗe da singlet, a ƙofar ɗakin ya saka singlet ɗin ya ɗora rigar hannunsa riƙe da waya ko maɓallin rigar bai ɓalla ba hatta takalminsa tana gani a baibai ya saka, ƙofa ya nufa sai jin rufowar ƙofar gidan ta yi gararaf!.

Kalifa ta kama ta tsayar a gefe ta wanke wajena ta ɗakko shi suka nufo ɗakin, tana zuwa ta zauna a kan kujerar Kalifa yana kan cinyarta, bata ankara ba sai ta ji hannun Kalifa a kan fuskarta yana share mata hawaye, kallonsa ta yi tare da rungume shi, tana jin son ɗan nata har ciki ranta, tana rayawa a ranta ta san komai daren daɗewa za ta fita daga cikin wannan uƙubar, sannan tabbas ta san Nasir ranar nadama tana zuwa zai gane shayi ruwa ne, amma dai a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, don rayuwa tana cike da darasi ne sai dai mutum bai ga damar ɗauka ba, amma a kowane sakan a kowace awa akwai abubuwan da mutum zai koya kuma ya gane sai dai ruwansa ne ya yi aiki da shi ko kuma ya watsar amma dai shi ubangiji mai yin hisabi ne a kan komai!.

Wajen ƙarfe goma ta ji an turo ƙofa, sallamar Hajiya ce ta fara tashi a cikin gidan, cike da ladabi Sadiya ta amsa, sai dai fitowarta daga ɗakin domin yi wa Hajiya iso lokacin Kalifa yana biye da ita dama wanka ta masa tana shafa masa mai. Gabaɗaya fuskar Hajiya a haɗe take tamkar an faɗa mata mutuwa ko wani mugun abu, amma sai Sadiya ta daure ta ce

"Sannu da zuwa Hajiya bismillah ki shigo" Wani kallo ta jefi Sadiyar da shi ta ce

"Ba abin da ya kawoni ba kenan, ko an ce miki zama na zo idan zaman nake son yi in zauna a gidana a ɗakina mana, kin san dai ai kujeruna sun fi naki komai sau miliyan" Sadiya ta ji babu daɗi a ranta amma sai ta danne ta yi murmushin yaƙe wanda iyakarsa leɓe ta ce

"Haka ne sun fi nawa " Wani kallon ke kika sani Hajiya ta mata ta ce

"Nasir ya je mini da wata maganar banza wai ciki ne da ke" Abin ya yi wa Sadiya ciwo wato cikin sunna ne ma maganar banza hakan ya sa ta ce

."Eh gaskiya ne" Hajiya ta É—an yi mamakin amsar da Sadiya ta bata duba da Sadiyar bata fiya kausasa harshen ba amma amsar tata sai ta ji tamkar dai a fitsarance ta yi amma sai ta ce

"To abin da nake so da ke shi ne, mun yanke shawara da Nasir da Æ´an uwansa cewa wannan ciki zubar da shi za a yi" Da sauri Sadiya ta É—ago kai tana kallon Hajiya cike da mamakin kalamanta.

*BABA*

Duk kiran da yake yi wa Sumy tana jinsa amma ta ƙi amsawa hakan ya sa ya fara rafkawa Mama Talatuwa kira, Mama jin kiran ta tunkari ɗakinsa tana zuwa ta ganshi a ƙasa a kwance yana sharɓa uban gumi ta ce

"Subhanallahi Malam lafiya" Baba da ya buÉ—e baki zai bata amsa jin gudawar ta taho sai ya ji tamkar idan ya buÉ—e baki kashin zubowa zai yi bai yi wata-wata ba ya sake komawa banÉ—aki, sai gashi yana tafiya yana É—an sunkuyawa yana dafa bango yana faÉ—in

"Wayyo Allah, gaskiya gudawa bata da daɗi ko in ce bata da imani, kalli yadda ta ƙarar min da ƙarfi lokaci guda, ɗan katan daɗi da na ci duk ta saka na kai masai(Toilet ) Haba ai sai na gwammace daman awara na ci don ji ba don idan ban yi gudawar nan ba a wando za ta zubo da ba zan yarda in yi kashin abinci ƴan gayun nan da na ci ba" Tana ta kallonsa har ta samu ya zauna tana son amayar da magana amma tana tsoron masfifarsa sai da ya zauna da sauri ya zame ya kwanta yana cew

"Ni wallahi ina ga mazaunan nan nawa ba za su zaunu ba ma, kai jama,a lokaci guda mutum lokaci guda ba mutum ba"

Mama Talatuwa ta ce

"Dama haka cuta take yanzu mutum yanzu gawa... Kafin ta ƙarasa ya ce

"A bakin ki Talatuwa kuma sai kin rigani mutuwa, ni nan tsawon rai zan yi sai na haifi na miji ko kangararre ne ya taimaka min na san daÉ—in haihuwa sannan zan mutu" Cike da mamakin maganarsa ta ce

"Allah ya huci zuciyarka dama ni ban maka fatan mutuwa ba, ai cuta ba mutuwa ba ce" Shiru ya yi don jin cikinsa yana kartawa ya ce

"Ki nemo Sumayya ta kawo min maganin gudawar da Habiba ta bata ta saya da safe" Da to ta amsa ta tashi ta fito, É—aki ta nufa ta samu Sumy ta ce

"Sumayya Babanku ya ce ki kai masa maganin gudawa" Shiru ta yi sai kuma ta tashi ta fita, tana zuwa É—akinsa ya fara masifa

"Ke saboda ke shegiyar yarinya ce ina wannan halin amma ba za ki kawo min maganin ba?" Tana danne Æ´ar dariyarta ganin Baban ya yi zuru-zuru don ta tuna matsayinsa na mahaifinta bai nuna tausayawa ba gareta ya bata kuÉ—in maganin ba sai yanzu kuma zai ce ta bashi hakan ya sa ta ce

"Baba dama fa guda huÉ—u ne ni kuma duka na shanye" Cike da masifa ya ce

"Si kike dai in fitar da kuÉ—i ko in banda ma almubazzaranci a ce magani biyu ma bai isa ki shanyw ba sai kin sha huÉ—u" Bata yi magana ba ya ce

"Ai kuwa da in banda hamsin ko É—ari a siyo min maganin gwara na zauna gudawar da kanta in ta gaji da fitowa ta tsaya min"

Haka Baba ya yi ta gudawa har dare amma bai sha magani ba, sai da ya ga yana dab da rasa ransa sannan ya bada naira hamsin aka siyo masa ya sha.

Washe gari ma haka gudawar ta dawo don haka ya galabaita ma, sai masifa yake yana cewa ƴaƴansa basu da amfani da a ce maza ne da yanzu sun kai shi asibiti Arfat ce ta lallaɓa lokacin baccin wahala ya ɗauke shi ta je ta auno shinkafa kwano biyu ta ɗora ta dafa ta lallaɓa aljihun rigarsa ta ɗauki dubu biyar ta yi miya har da naɓa don dama mahaifiyarta ce da girki.

Aka dafa shinkafar nan har dare kowa yake wadaƙa da ita ya ci ya ƙoshi don dama cikin wacce ya noma ce da ya jibge sai kayan abinci sun yi tsada zai fito da ita ya sayar, shi ma da ya tashi haka Mama Bilki ta kai masa shinkafa da miya da nama ya karɓe ya ci yana ta saka albarkar cewa ashe tana son sa tun da har bakin girkinta tana sayen abinci ta dafa kowa ya ci lallai yana alfahri da ita.

Ko kaɗan bai san cewa abincinsa ba ne kuma a aljihunsa aka samu kuma a aljihunsa kuɗin cefanan ma ya fita, yana da halin da zai wadata iyalansa amma ya gwammace ya musu ƙwauro ya ce kowacce ta je ta nema ba ya musu kallon su mata ne kuma ba ya tsoron hakan ya zama hanyar lalacewarsu.

*JIDDA*

Daga ita har sauran wanda suke kusa da su na motar kallon Aliya suke, hatta direban motar sai da ya taka wani uban birkin da sai da wanda yake bayansa ya kusa buga masa tasa motar, Allah ya rufa asiri ma lokacin ba wani gudu ake yi ba tun da suna ƙoƙarin kutsa kai cikin gidan Jiddan ne. Kowa ya hau tambayar ko lafiya, shi dai direban ƙarasawa ya yi ciki ya yi parkin don duk girman gidan sai da gabaɗaya motocin suka shiga ciki.

Ƴar uwar Ummar ce ta ce

"Lafiyarki Aliya mai yake damunki" Aliya da shigowarsu cikin get ɗin gidan ya sa ta sake susucewa hankalinta ya ɗuguzuma da tashi, ganin gidan da ƙwayaye tarrr ya haske ko ina kamar rana ga motoci ne tamkar wajen aiyar da su suna gefe a lulluɓe, hakan ya sa ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu. Ita ma ƴar uwar Abban ta ce

"Ko dai jifa aka yi wa yarinyar nan ne a kan aure in ba haka ba yanzu nan take lafiya ƙalau amma kuma a ce ta gigice haka?" Ƴar uwar Umma wacce ranta gabaɗaya ya ɓaci na ganin gidan Jiddan ta ce

"Allah ne ya san karatun kurma" Jidda kuma duk ranta ya sosu ta ce

"Aliya mene ne ?" Aliya ji ta yi da Jidda ta yi magana tamkar ta ɗauki wuƙa ta daɓawa Jiddar ai dai dole idan Jiddar ta mutu Ibrahim ya aure ta, ta zauna a wannan gidan mai kyau wanda a ganinta kowacce mace za ta yi buri da mafarkin samu!.

Direban ma gabaɗaya ya maido hankalinsa kansu shi da abokinsa na gafensa, Aliya kuma da sauri ta danne abin da take ji ta tattaro nutsuwar ta ta buɗi baki tana mai miƙa hannu wajen ƙafarta ta ce
Chapter 34 · 0% Book details