← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 106

Sashe 59

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MEENAL

Ko a jikinta yayin da take furucin Hajiya kuma cike da mamaki ta ce

"Meenal ko dai makuwa kika yi?" Meenal ta ce
"Ban gane ba Hajiya rass nake a cikin hanklina nake magana, yanzu ke idan su Husna ne suka yi aure a gidan mijinsu za ki so uwar miji ta takura musu? Ni ma nan gidan nawa mijin ne kuma wallahi abin da na ga dama zan yi babu mai taka min bare ya zubar" Tana kaiwa nan ta sauke wayar daga kunenta ta yanke kira ta koma kan kujera ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Nasir kallonta kawai yake jin ya rasa bakin magana ma Hajiya kuma sai ta saki baki tana bin su Husna da kallo wanda su ma ita suke kallo suna jiran ƙarin bayani duk da yanayinta ya so basu wata amsa amma basu fuskanta ba.

Hibba ta ce

"Mene ne wai Hajiya?" Hajiya ta danne leɓe da haƙuri ta ce

"Ikon Allah wai ni ko dai aljannu sun hau kan wannan yarinyar ne a daren jiya? Gaskiya ba ƙalau take ba ina jin sai an nema mata magani wallahi ba Meenal ba ce" Su ma kalkonta suke nan ta shiga furta musu abin da ya wakana sai Husna ta ce

"Gaskiya abin fa da mamaki ai ko Sadiya da ba ma goyon bayanta bata yi wanna abin da Hajiya akwai dai abin da yake faruwa" Ajiyar zuciya ta sauke don sai yanzu ta ji daÉ—i da ta yi wannan tunanin amma in a ce gaske ne abin da yake faruwa to tabbas babu maraba akwai gagarumar matsala don ba za ta lamunta ba.

Kiran wayar Nasir ta shiga yi amma ba a É—auka ba har ta katse, Meenal cike da yatsina fuska ta ce
"Ko ka karɓi wayar ka ɗauki kiran ko ka kashe don i wallahi ba na son ƙara takura min yake" Kamar wani soko haka ya ga ya koma ya karɓi wayar kafin ya amsa kiran ta katse sai ta sake kira yana kara wayar a kunne ta cr

"Nasir lafiya dai ko, mene ne yake shirin faruwa" Kallon Meenal ya yi sai kuma ya ce

"Babu komai Hajiya" Hajiya ta ce

"Ban gane babu komai ba ko dai akwai matsala ka matsa daga kusa da Æ´ar tawa zan yi magana da kai" Da to ya amsa ya tashi ya nufi hanyar bedroom muryar Meenal ta katse shi da faÉ—in

"Wallahi duk wata ƙulla ƙulla da aka yi ba zan ɗauka ba don ni ba bauta na zo ba, in ban da ma ana son yin wata ƙullalleniya ya za a yi ina matarka sai ka matsa za a yi magana da kai" Bai tanka mata ba ya koma ɗaki Hajiya ta rage murya ta ce

"Nasiru wai daga jiya zuwa yau baka fahimci akwai sauyi a tare da yarinyar nan ba?" Nasir ya ce

"Eh na gani Hajiya wani abu ne"
Hajiya ta ce

"Allah sarki Meenala ni wallahi na san ba ita ba ce yarinyar kirki me biyayya Allah sa ba jifanta aka yi ba wallahi ka san gidan kishiya"

Nasir ya ce
"Jifa kuma Hajiya daga zuwa sai a jefe ta, kum... Bai ƙarasa ba ta balbale shi da faɗa tana cewa ya je ya bata kulawa ya mata abin da take so ko ta takale shi da faɗa kar ya kulata don ba a hayyacinta take ba, ba don ya yarda ba ya amince kuma sai ya ji suna saka masa tsoronta a aransa.

Yana zuwa falo ya ce

"Yanzu mai za ki ci" Ta wani rausaya idanu ta ce

"So nake ka je ka ce Sadiya ta soya min doya da dankali ta dafa min shayin goruba" Kallonta ya yi ya ce

"A gidan nan babu dankali ko ƙwaya ɗaya, bare doya Sadiya ai tuwo take yi dama kayan dankalin a gidan Hajiya suke shi ne nake ci a can kuma yanzu tun da ke ƴarta cw shi ne ta aiko har da ke amma Sadiya ko a cokali bata taɓa aiko mata dankali ba" Kamar daga sama sai ji ya yi ta ja tsaki da sauri ya ɗago ya kalle ta ya ce

"Wa kike wa tsaki" Banza ta masa ya buɗe ƙofar ya fita ba tare da ya ci abincin ba. Yana fitowa ya fice daga gidan dama ya ɗauka mukullin motarsa a falon yana zuwa ya tada mota, ita kuma ta koma ɗaki ta ɗauki waya ta kira ƙawarta ta ce

"Ƙawata" Daga ɗaya ɓangaren ƙawarta ta amsa da faɗi

"Inyee amarya ki ce ta waru, wato dai an dace an tsallake rijiya da baya, tun da na ji muryarki na gane ba matsala amma da ina nan cike da fargaba" Dariya ta fashe da ita ta ce

"Ai na faÉ—a miki komai ya yi daidai wallahi da bakinsa bai furta ba kuma bai nuna wata alama ba ke gabaÉ—aya babi wannan maganar fa" Ta faÉ—a suna ta darawa abin su

Safiyya ta ce
"Shikenan ƙawata sai ki sha sha,aninki gida naki"

Meenal ta c

"Ai ki ƙaddarw ni kaɗai ce a gidan nan bani da kishiya kuma sai na koyawa kowa hankali"

,Safiyya ta ce

"Girmanki ne ai yanzu zan haɗo kan ƙawayenmu yuya guda mu zo" Nan ta bata labarin yadda suka ƙare da Hajiya tana kashewa ta kira Momi mahaifiyarta bayan sun gaisa Momi ta ce

"To ya kika ga yanayin zaman karki kuskura a rainaki matsawar dangin miji suka rainaki kowa kanki zai zuba shara da bola gwara a raba rani kowa ya ɗauka ko ita Hajoyar karki raga mata domin kowa kansa yake so ita ma duk yadda muke da ita ɗanta za ta fara so" Nan Momi take ɗora ta har tana faɗawa Meenal cewa za ta je wajen malamin ta ya dasa soyayyarta a zuciyar Nasir da kuma ƙin son rabuwa da ita duk runtsi!.

Nasir yana fita ya nufi gidan Hajiya, ya samu Hajiya zaune suna ta magana da ƙannaensa Hajiya ta dube shi ta ce

"Wai Nasir ya na ganka duk a firgice kamar ba mai sabon aure ba" Nasir ya busar da iskar da ya cika bakinsa da ita ya ce

"Hajiya wasu halayya ne nake gani daba wajen Meenal duk abin ya É—aure mini kai ... Tun kan ya kai aya ta tari numfashinsa da faÉ—in

"An faÉ—a maka ba cikin hayyainta take ba amma ni na san Æ´ata ba irin Æ´nmatan zamani ba ce" Ya yi É—an shiru ya ce

"GabaÉ—aya ta sauya kamar ma ba sabuwar amarya ba"
Nan Hajiya ta fara faɗin sai ta je ta samo mata magani wataƙila jifanta aka yi ko dai an yi mata wani abu da ya saiya mata tunani. Ko faɗawa ƙawarta mahaifiyar Meenal bata yi ba ta kama hanyar gidan malami ta ce ya bata karya tambaya bayan ta gama rattabo masa bayanin abin da yake faruwa ya bata tabbacin idan aka yi amfani da maganin komai zai warware.

Lokacin da ta baro gidan malamin bata zame ko ina ba a napep sai gidan Nasir lokacin Nasir ya koma gidan ganin taron ƙawayenta sun cika falon wasu ma yana iya jiyo hayaniyarsu a bedroom, hakan ya sa ya faɗa mata zai ɗan fita bayan ya ɗakkowa Sadiya tsakuran abin da za ta dafa wanda ba zai isa ba ya bata. Shi a tunaninsa ƙawayen kawai ratsowa ne suka yi sai kawai Meenal ta ja shi gefe ta ce masa

"Nasir ina mukullin store" Da mamaki yake kallonta sai dai kuma ya danne mamakin ya ce

"Mukulli kuma?" Ta ce

"Tambaya kake ko neman sani?" Lafazin da ta yi ya so bashi mamaki don shi abubuwa ne sabbi a wajensa Sadiya bata taɓa masa tambaya ko bashi amsar rainin hankali komai cikinn girmamawa da mutuntawa matsayinsa na mijinta. Cike da mamakin dai ya ce

"Mai za ki yi da mukullin store?"

Ta ce

"Wai ban gane ba shi mukullin store ɗin har wani abu ne da za ake tuhumar mutum don ya ce a bashi?" Hannu ya saka a lajihu ya fito da mukullin daga ciki da yake mukullayen suna da yawa a haɗe sai ya nuna mata wanda shi ne na store ɗin, tunaninsa ko zuwa za ta yi ta ga yanayin store ɗin sai kuma ya ga ta saka hannu ta cire mukullin daga jiki ta miƙa masa sauran, tsabagen mamaki ma ya kasa magana ko ƙara bi ta kansa bata yo ba ta yi gaba, duk abin da suke Sadiya tana kallonsu kasancewar labule windonta a ɗan ɗage yake sannan kuma tana iya hangon su.

Wani murmushi ta yi a zuciyarta ta ce

"Mafari kenan"

Kicin ta wuce tana ƙarewa kicin ɗin kallo ta ga kayanta a gefe kayan Sadiya ma haka a wulaƙance take kallon kicin ɗin duk da a share yake tas a goge sai gawayi da yake gefe da Sadiya ta ɗora ruwan abinci a ƙaramar tukunya ita saboda ana zaluntar ta ma ko kuɗin mahaɗin ba a bata ba bare kuma a bata don mugunta saboda ya ga tana sana,ar mai, amma duk da haka bata ma tanka masa. Meenal ganan cooker gas ɗinta ta ƙarasa ta ga silindar gas ɗin babu komai ai kuwa da sauri ta fito tana ƙwala masa kira don har ya juya ya je zaure ya juyo ya dawo shi ya rasa ma mai ya sa ba ya mata tsawa ko kuma rainin hankalin da yake yi wa Sadiya wacce duk wani cin kashi yake saukewa a kanta.

Yana zuwa yake binta da kallon rashin fahimtar kiran da ta masa, yana ayyanawa a ransa wannan wace irin amarya ce da bata kara ko kunya a kwana ɗaya tak ta saki jikinta tana sha,anainta tamkar dai dama ta daɗe a gidan, ba ma wannan ba sai ya ga yanzu ta daina wannan tafiyar da take tana tale ƙafa. Wani farr ta yi da idanu ta ce
Chapter 59 · 0% Book details