← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 106

Sashe 69

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan farraƙaku nan ba da daɗewa ba dole za ku rabu, ni kuma in gina fada ta" Ta faɗa a fili tana tunanin tashi ta yi abin sa ya kawo ta gidan amma kuma tana tunanin ya za a yi ta gane cokalin. Ƙaran wayarta ne ya katse mata tunanin da take tana dubawa ta ga Umma ɗagawa ta yi tana ɗan waiwayawa ta ga tabbas babu kowa dama wannan ƴar aikin take ji tana karawa a kunne ta ce

"Hlo Umma"

Umma ta ce

"Aliya ke kaÉ—ai ce?" Aliya ta ce

"Eh Umma amma ban koma gida ba"

Umma ta ce

"Ayyo dama ina son jin kanun labarai ne to na tambaya cewa ke kaɗai ce don kar in je ko wannan mata mazan yana kusa" Wani takaici ne ya turnuƙe ta da aka ambaci sunan mijinta tana sassauta murya ta ce

",Umma ina gidan Jidda zan kira ki"

Umma da mamki ya gama ɗarsarwa a zuciya na tambayar kanta mai ya kaita gidan Jiddar sai dai tun da ta ce tana can babu damar tambaya sai ta fara ƴar dariyar yaƙe wacce ta soyayar ƙarya ce ta ce

"Kuma yanzu Aliya kina gidan Æ´ar tawa shi ne kike sanya baki haÉ—amu a waya ba maza bani ita" Aliya ta ce

"Hmmm! Umma bata kusa fa sun hayr sama ita da mijin" Umma ta ce

"Aikin banza da wofi idan tusa tana hura wuta ai za mu gani" Tana faɗar hakan ta kashe wayar tana tunanin dole a samo maƙarƙashiyar da za a yankewa Jidda jin daɗin da take ciki domin ita Umma saboda hassada mugun ciwo ko gidan Jidda bata taɓa taka ƙafarta ba tana ta faɗar wai ɓanya basu fiya zuwa gidan yara ba sai da dalili.

Tana ajiye wayar ta tashi tsaye gabanta yana faɗuwa za ta tafi neman cokali hanyar kicin ɗin ta kama har ta tafi ta dawo jin ƙaran wayarta ta ɗauka ma Umma ce sai ta ga sunan Amatullahi ta ɗaga Amatullahi ta ce

"ƙawata ya ake ciki ne Allah sa dai aikin gama ya gama?"

Aliya ta ce

"Ina nan yanzu na samu dama zan je in duba"

To mai kike jira ko sai kin rasa damar da kika samu"

Aliya ta ce

"Ni wallahi tunanina ma wanne ne cokali" Amatullahi ta ce

",Dalla malama ki yi aiki da hankali da tunaninki " Tana faɗar hakan ta kashe wayar ita kuma ta ajiye ta nufi kicin ɗin da sauri,sai kuma ta dakata ta yi wajen dinning ɗin sai kuwa ta ga gabaɗaya kayan abincin ne ba a ajiye plate da cokula ba tsaki ta yi ta je ta tura kicin ɗin wani ƙamshin girki da bai gama barin kicin ɗin ba ne ya ziyarci hancin ta, amma ba wannan ne a gabanta ba sai ta shiga wurwurga idanu manyan kwanduna ne gasu nan da dankali da doya kainiya ganinta komai gashi na a wadace ban da ma ita ai babu wani abunda zai bata mamaki domin gidan dukiya ta zo mai za ta gani ƙwai ma kamar abin banza gashi nan kiret kiret ita kuwa tun da ta ragargaje na amarcin yanzu sai dai ranar da ya ga yana da kuɗi ya siyo guda biyu wasu manyan robobin spices da curry masu ɗauke da sunan MAMANA AFRAH SPICES ta gane jere da nauikan abubuwa da ta tabbatar duk kayan girki ne, tsaki ta yi ta je inda ta ga cokulan ta fara tunanin wanne za ta ɗauka kar ta je ta ɗauki wanda ba nasa ba a samu matsala babu zato da tsammani ta ji an turo ƙofar wanda hakan ya sa ta tsorata sosai hantar cikinta ta kaɗa sai ta ga wannan ƴar aikin ce da ta ji an kira da Saude.

Cike da girmamawa ta ce

"Ayya ban san kina ciki ba shi ya sa ban nema izini ba" Kallon ƙasƙanci Aliya ta jefe ta da shi ita Saude tana mamakin matar tun da ta san Jidda bata wulaƙanta su tamkar ma ba ƴan aiki ba amma ita wannan sai hararrata take frige ɗin kicin ɗin ta buɗe ta ɗakko ruwan roba guda biyu ta rufe har ra je bakin ƙofa sai Aliya ta ce

"Ina za ki kai ruwan wato kin ga bata nan za ki yi sata"

Saude ta ce

"Sha za mu yi fa"

Aliya ta ce

"Lallai samun wuri har ruwan roba kuke sha?"

Saude ta ce

"Aunty Jidda ta ce bata mana shamaki da duk wani abu ba" Tana faÉ—ar hakan ta juya ta bar kicin É—in.

Jidda ko da suka shiga ɗakin ta ajiye jakar a kan ƙaramar lokar gefen gadon bayan ta taimaka masa ya zauna, yana dafe kai duk sai tausayinsa ya kamata.

Cike da kulawa ta ce

"Kanka ne yake ciwo?" Kai ya gyaÉ—a mata, taimaka masa ta yi ta kwanta bayan ta ja masa filon ya kwanta sai ta shiga masa addu'a bayan ta masa cikin sanyin murya mai cike da nuna kulawa da kuma damuwa da wanda ake yi wa magana da muryar ta ce

"Mu tafi a kai ka asibiti ina direban ne" Dakyar ya mata magana ta hanyar faÉ—in

"Ba sai na je asibiti ba, direbana na aike shi a bakinnget ma na ce a ajiyeni"

Ta ce

"To ba ga direbobi a gidan ba"

Ya ce

Ki bar batun asibitin nan"

Ta rausayar da kai kamar za ta yi kuka ta ce

"To a kira likita ko in kira Mummy sai ta faɗawa Daddy?" Maimakon ya bata amsa sai ya saka hannunsa ya riƙe dantsen hannunta kawai ya mayar da idanunsa ya rufe yana faɗin

"Ki bani magani bana son kowa ya sani idan na sha magani na samu bacci zai daina" Shiru ta yi tana bhn kyakkyawar fuskarsa da kallo yadda zara zaran gashin idanun da suka ƙawata idanun suka ƙara masa kyau sai kuma yadda fuskar ta yi fayau da ita.

Tana cikin kallon ta ji cike ta kulawa ya ce

"Kar ki saka damuwa a ranki kin ji Jiddana" Idanun ta lumshe ta buÉ—e ta ce

"Ita damuwar da kanta ta san na cancanci na saka ta a raina domin da kanta ta ziyarce ni tun a kallon farko da idanuna suka maka, a inda ƙwaƙwalwa ta harba saƙon kana cikin damuwa tun a lokacin gaɓɓaina suka yi sanyi yanayin jikina ya sauya" Furucin da ta yi ya tabbatar da sun zama hanta da jini shi da ita, don shi ma haka ne yake faruwa da shi idan ya ganta a damuwa!.

A hankali ta zame riƙon da ya mata fitowa ta yi domin ta samo masa abinci kaɗan ya ci ya sha maganin, sai da ta sakko ƙasa da ta ga kwanukan abincin da suke ci da Aliya sannan ta tuna cewa Aliya tana gidan don gaba ɗaya ta manta damuwar Ibrahim ɗinta ya dishashe tunanin komai.

Tunaninta ko ta shiga bedroom ne za ta shiga bayi, dining ta nufa tana zuwa sai ta ga ashe bata ajiye masa plate da cokula ba hakan ya sa ta nufi kicin ganinsa a É—an buÉ—e ta tura sai kawai ta ga Aliya tana tsaye, Aliya kuma sai da ta ji gabanta ya faÉ—i domin bata tsammaci zuwan Aliya a yanzu ba don ita zuciyarta ma tana faÉ—a mata cewa suna can suna soyayya saboda bata san cewa bashi da lafiya ba.

Cike da wayuncewa ta ce

"Kawai kicin ɗin nake ƙarewa kallo kin san ina son ganin jeran kicin, nawa ma sai na yi ta kallonsa duk da bai haɗu kamar wannan ba" Jidda bata san lokacin da ta yi dariya ba ta ce

"Kina da abin daariya yanzu saboda kallon kicin É—in ne kika bar cin abinci?"

Aliya ta ce

"Haba Jidda ya za a yi in iya ci bayan tare muke ci kika haura sama"

Jidda ta ce

"Ai da kin ci ni yanzu abinci zan kai masa kaÉ—an ya samu ya ci ya sha magani ba ya É—an jin daÉ—i ne"

Aliya ta ce

",Wayyo Allah sawaqe" Jidda ta amsa da amin

Kicin wear ta nufa ta ɗauki plate guda biyu, sai kuma ta je wajen na cokula ta ɗauki cokali a inda gabaɗaya cokulan iri ɗaya ne a wajen sai kuma ƙasan wasu ne amma masu mariƙa ja ne wanda ta ɗauka kuma coffee ne jikin inda ake riƙewar. Ta haɗa da saving spoon suka fito tare tana tsokanar Aliya wai har ta gama kallon kicin ɗin ita kuma sai take ta murna a ranta ta gane cokalin da yake amfani da shi.

Ita ta tsaya a dining tana zuba masa abincin ita kuma ta ƙarasa ta ci gaba da cin abincin amma naman kazar take ci don ta yi amanna ba za ta rage naman ba saboda ta san idan ta koma nata gidan miya ce zallah ko naman miya babu sai ranar da ya ga da sarari ta siyo naman miyar ko kifi a saka, in kuma kasuwa ta yi kyau sai ya siyo naman a dafa ita a da ne ta matsu ya samu aiki amma yanzu da samun aikinsa da rashinsa duk ɗaya tun da dama tana so ne tun da ta ga yanzu shi yaron kasuwa ne ba wai hamshaƙin ɗan kasuwa ba kenan duk abin da yake nemowa buga-buga ne.

Jidda tana gama zubawa ta rufe da ɗaya plate ɗin ta haura sama Aliya tana raka bayanta da harara kamar idanunta za su faɗo. Tana gama daina hangota da sauri ta tashi ta nufi kicin ɗin ta ɗauki cokalin ta tsaya tana kallon cokalin tana dariyar cin nasara kasancewar bata rufe ƙofar ba Saude da ta dawo ta ga abin da take lokacin da ta kawo kai kicjn ɗin, mamaki ne ya kama Saude dalilin murna da kuma dariyar a kan ganin cokali Aliya kuma da ta ga mutum sai kawai gabanta ya faɗi don bata ma gama tantancewa cewa Saude ba ce duk tunaninta Jidda ce ta dawo bata san lokacin da ta ɓoye cokalin a baynta ba wanna ya sanya wani abu ya ɗarsu a zuciyar Saudr tun da ba yarinya ba ce budurwa cenza ta yi shekara sha buyar zuwa sha shida.

Aliya kuma da ta dawo hayyacjnta daga duniyar tsoron ta ga Saude ce ta doke tsaki ta ce
Chapter 69 · 0% Book details