Sashe 31
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baka bada abinci ba" Ya juyo cike da gajiyawa ya ce
"Abinci, abinci, abinci" Sai da ya maimaita sau uku sannan ya yi wani tsaki, store ya je ya buÉ—e ya É—akko taliya guda É—aya ya rufe ya fito ya ce
"Gashi nan kuma wallahi kar ki juye duka, idan kika zuba rabi sai ki ɗan ƙara ki ajiye idan na dawo zan mayar store" Cikin sanyin murya ta ce
"Ka bada kuÉ—in cefane babu kayan miya sannan mai ma saura kaÉ—an, sai in ba almajiri ya siyo" Cike da tijara ya ce
"Wallahi naira biyar ba zan bayar ba wannan idan kina jero buƙatu ai sai ki talauta ni, wallahi shi ya sa nake so in yi aure ko na samu sassauci na san amaryar da zan auro za take tarairayar aljihuna tana buɗe bakin jakarta don ta tallafa mini" Yana kai wa nan ya saka takalmansa ya fice.
Bayan ta gama gyaran gidan ta yi wa Kalifa wanka ita ma ta yi, wanke wanke ta yi da wankin banÉ—aki ta gyara kicin tas. Ganin Kalifa ya yi bacci ta haÉ—a kayan wanki ta je ta wanke, duk abubuwan nan da take gabanta yana faÉ—uwa domin tana ta juya maganar Nasir a ranta a kan maganar ciki, ita kanta bata son ta samu ciki yanzu ba ma yanzu ba ita idan son samu ne Kalifa ya zama shi kaÉ—ai ne wanda zai zama rabo tsakaninta da Nasir domin ta san gidan nan ba gidan dauwamarta ba ne, babu ma alamar zaman zai É—ore duk da ta san mutuwar aurenta tamkar rasa wani sashe na zaman lafiyarta ne a gidan mahaifinta amma dai tana zaman jiran tsammanin ta inda mafita za ta zo mata watarana!.
Tuno da tsinken pt na awon ciki wanda lokacin da take shayar da Kalifa Nasir ya zargi ciki ne da ita ya ringa mata rashin mutunci da hana rayuwarta sakat, shi ne da ya ga babu haza ya siyo pt ɗin ya ce ta gwada, tana dubawa babu ciki shi ne ya ringa jero hamdala kamar dai wani abu ne daban, sai ka ce ba shi ne mamallakin cikin ba, kamar dai ba shi ne yake lallaɓowa ya karɓi haƙƙinsa ba.
Kasancewar lokacin guda huÉ—u ne sai ta ajiye ukun yanzu ta É—akko guda É—aya domin ta gwada, sai ta ajiye masa idan ya zo ya ga layi É—aya ne babu ciki sai ya sakar mata mara ta yi fitsari. Tana É—akkowa ta je ta samu wani É—an murfi ta shiga bayi ta yi fitsarin ta fito gabanta sai faÉ—uwa yake tana fargabar sakamakon.
Ko da ta zo ta ɓare pt ɗin ta tsoma a fitsarin ta ciro yayin da fitsarin yake tafiya a cikin pt ɗin domin fitar sakamako tare da matsananciyar faɗuwar gabanta yake tafiya. Lokacin da ya gama tafiya idanunta ra runtse da ƙarfi tana ta karanto addu'a a a zuciyarta a kan Allah ya sa ba ciki ne da ita ba, in ban da ma irin rayuwar da ta samu kanta a ciki a ce wai kana fargabar ganin kana ɗauke da ciki sai ka ce wani cikin shege!.
Hannunta karkarwa yake, kai gaba ɗaya ma sai jikin nata yake karkarwa shahada ta yi ta buɗe idanunta warai sai a kan sakamakon layi biyu ne a jiki raɗo-raɗo ƙafafunta da ta ji suna barazanar jumurin ɗaukar gangar jikinta da sauri ta zube ƙasa tana zaunawa zaman dirshan a fili tana furta
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un"
*JIDDA*
Kunnuwanta ta sakawa auduga daga maganganun da su Umma suke yadawa a cikin gidan, duk wanda ya shigo gidan ganin kaya tana jin yadda Umma take nuna musu akwatuna 24 a matsayin lefen Aliya ta faɗa musu har da mota duk da motar Abba ya ɗauke ta ya kai gidan abokinsa aka ajiye ta, sannan sai ta nuna akwati biyu da kit a matsayin lefen Jidda mutane su yi ta faɗin Aliya ta yi goshi don wasu ma ganin kayan ya sa sun ɗauka wani hamshaƙin mai kuɗi ne Aliyar ta aura.
Umma duk ta kasa sukuni sun hana ransu sakat da ƙyashi da hassada ji take tamkar ta sauyawa Aliya da mijin Jidda a nata ganin ai Jidda ba za ta auri wanda ya fi mijin ƴarta Aliya ba.
Hassada suke nunawa a fili amma ita Jidda ko a jikinta, sai dai kuma da ya rage saura sati guda biki sai Umma da Aliya suka keɓe a lokacin da Jidda bata nan tana gidan su Salama sun tafi rabon cingam da kati, duk da har gidansu Ibrahim Salama ta rakata da Mummy ta ce sai ta je ta gaishe ta, sun ga tarɓa ta mutuncin kuwa a nan Jidda ta fahimci ta samu surukar arzii, sannan ta ƙara fahimtar ba ƙaramar ƙauna take yi mata ba, hakan ya sa ta ƙara jin hankalinta da kwanta da auren Ibrahim ko ba komai idan uwar miji tana sonka za ka samu salama a gidan mijinka.
Umma ce ta kalli Aliya da ta zuba uban tagumi, duk ta bi ta rame ta yi duhu ta ce
"Aliya na faɗa miki ki dajna saka damuwa a ranki, kar ki je ki samu wani ciwon kin san dai dama an ce hassada mugun ciwo ce bare kuma ta haɗu da damuwa a zuciya abin sai ya miki illa don abin sai ya yi yawa wai shege da hauka" Aliya ta buɗe bakinta da kuka yake son ƙwace mata ita damuwarta idan ta tuno kayan akwatin Jidda sai ta ji duniyar ta mata zafi, gani take gabaɗaya kayan da ita suka dace ba da Jidda ba saboda ita ce kyakkyawa kuma ita ce ma dai ta dace da auren miji kamar Ibrahim ba Jidda ba.
Tana jan hanci ta ce
"Wai Umma ya kike so in yi ne? Ina zan saka raina yanzu gwala gwalan da aka sakawa Jidda a lefe ni fa idan aka cire zoben ciki gabaɗaya sai ya saya kayan lefena har da canji, ga wasu miliyan uku a ajiye, sannan da kunnena na ji Salama tana cewa wai miliyan biyu ya bada kuɗin ƴanmatanci amma saboda Jidda matsiyaciya ce dakyar ta karɓi dubo ɗari biyu shi ma sai da Salama ta saka baki, yanzu da ni ce ba shikenan na samu wajen baje hajar karɓar kuɗaɗe ba, kina dai gani dakyar Kasim ya bani dubu hamsin shi ma yana min ƙorafin babu a rayuwa na tsani a furta min kalmar babu yanzu dubu hamsin mai za ta mana" Umma ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daɗi ta ce
"Ai ni yanzu ban san ba ya za a yi ma, wallahi na rasa mafita ko kaɗan gashi su Jidda ita da ƙawayenta Ibrahim ya biya musu kuɗin gyaran jiki ya kwaso kayan da za ta raba ya kawo mata suna nan jibge a ɗaki kamar babu gobe" Aliya kawai sai ta rushe da kuka ta ce
"Har kuɗin ƙunshi ya biya fa, jiya da dare ma kuɗin da ya bata ta miƙo min dubu ɗari wai ko za mu ƙara ni kuwa na jefa mata kayanta kar ma ta yi tunanin kuɗinta wata tsiya ne a wajena"
Umma tana zaro idanu ta ce
"Dan ubanku kika bata kuɗin? Wane shegen ya ce miki ana mayar da hannun kyauta baya, ai kai faƙiri baka biyewa mai arziƙi bayan kin san kina da buƙatar kuɗin"
Aliya ta ce
"Umma akwai damuwa fa a ce wai ni ce Jidda za ta taimakawa, ki ga wata shegiyar haÉ—aÉ—É—iyar mota wallahi da ni motar nan ta dace Umma" Ta faÉ—a tana kukan takaici.
Umma tana jin tamkar ta dishashe auren ma, amma abun da Allah ya nufa ya daÉ—e da yi, hakan ya sa ta ce
"Yanzu tun da dai Abbanku ya ce walima za a yi kin ga kayan can da Ibrahim ɗin ya kawo mata ya isa ku rarrabawa ƙawayenku to ya za ki yi tun da Allah ya ƙadarta miki talaka za ki aura, ai kawai mu bada kai bori ya hau"
Cikin rashin fahimta ta ce
"Umma ban gane ba"
Umma ta ce
"Aliya dole mu sauya taku, dole mu ɗauki haƙuri da jumurin halin da muka tsinci kanmu, ina nufin yanzu dole mu fito mu nunawa Jidda soyayyar ƙarya, mu danne duk wani ɓacin rai da za mu ji a tattare da ita, mu jata a jiki ta haka ne za mu samu shiga jikinta ta saki jiki da mu ko bayan an yi auren in ya so sai mu yi amfani da damarmakinmu wajen cika duk wani buri da muke da shi nan gaba!" Shiru Aliya ta yi tana nazarin maganar Umma duk da tana jin hakan da wuya ta iya amma kuma in har hakan ne dole ko da dariyar yaƙe ta yaƙi Jidda ta ga ko za ta yi nasara a kanta!
Tsaye Aliya ta tashi ta rungume Umma ta ce
"Umma ta kin fi ta kowa, Umma mikiya mai hangen nesa, tabbas ta haka ne za mu samu abin da muke so, don na ci alwashin sai na mallaki Ibrahim ko ta halin ƙaƙa, sai na zamewa Jidda ƙadangaren bakin tulu" Ta faɗa tana sakin Umma ta shiga juyi a tsakiyar ɗakin ta ce
"Umma kalli diri da kyauna ban dace da Kasim ba da Ibrahim na dace, ban dace da rayuwar talauci ba da gidan arziƙi na dace"
Umma ta ce
"Ai ki saka a ranki ƙwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wahala ba, ke ko zaman kishi ne gwara ki yi da Jidda"
Aliya ta ce
"Wallahi kuwa tun da ba uwarmu É—aya ba uban ma kowa da nashi, bare a ce auren miji É—aya ya haramta a garemu!".
Haka suka ringa tsara yadda abubuwa za su kasance wajen yaƙi da zukatansu ganin basu nuna ƙiyayya a fili ba.