Sashe 7
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da suka tashi ƙarfe biyu na rana ne, lokacin rana ta take, dakyar suka samu napep ɗin, sai dai kuɗin da ya yanka musu na Jidda naira hamsin bata cika ba hakan ya sa ta nemi alfarmar ya rage mata amma ya ce ba zai rage ba saboda shi ma ba ruwa yake zubawa a napep ɗin ba mai yake zubawa, suka tsaya a kan cewa idan an kusa zuwa za ta sauka haka ta amince. A daidai wani gidan mai ya sauke Jidda saboda har rance ta ce Aliya ta bata amma ta ƙi bata kuma akwai kuɗin a wajen Aliyar. Tana ji tana gani haka ta sauka da ranar nan ga yunwa da suka kwaso.
Aliya har da wani taɓe baki ta yi da sakin murmushin mugunta, dama da a tafiya ne sai ta ranta mata ko don saboda ta bata amsar exam tun da idan basu tafi tare ba sun zauna a kujera ɗaya ba sai dai ta bayar da takardar a haka ba tare da ta rubuta komai ba, kasancewar banda dusa babu komai a kan nata hasali ma bata karatun shiririta kawai take a makarantar da biyewa ƙawaye ƴan ƙarya, ita kuma Jidda karatun take yi gata da ƙoƙari kanta yana ja sosai da sosai saboda tana da mayat da hankali.
Tafiya take har ta ƙaraso wajen kamfanin simintin nan nasu Ibrahim, tana tafiya sai gumi ne kwance a fuskarta kasancewar ranar da ta take, Ibrahim wanda tun zuwansu da direban ya ce direban ya tafi da motar gida, saboda da Daddy za su tafi gida, ƙarfe biyu da rabi suka tashi Daddy da Ibrahim ne a baya sai direba yana jan su, mai gadin ƙofar kamfanin ya buɗe musu get suka fito, Ibrahim wanda tun bayan zuwansa kamfanin yake ta tunanin Jidda duk da bai san sunanta ba amma tabbas ya yaba da hankali da tunaninsa yarinyar ta birge shi sosai.
Suna fitowa kamar an ce ya ɗago fuskarsa sai kawai ya sauke a kan Jidda wacce take tafiya cikin natsuwa kanta a ƙasa, gabaɗaya ya mayar da kallonsa kwacakom kanta, yana ganin yadda hijabin ya mata kyau, shi dama yana son ya ga mace tana suturta jikinta, tambayar zuciyarsa ya fara yi yana cewa
'Ko ina fitsararriyar ƙawar nan tata, wacce bata san darajar ɗan adam ba, wannan ko kaɗan baku dace da zama ƙawaye ba, ana cewa sai hali ya zo ɗaya ake ƙawance amma dai ku kun sha bam-bam a halayya' Ya faɗa yana bin bayanta da kallon don lokacin ta gifta, ta kama hanyar gidan da ya ga ta shiga lokacin da ta tafi da safe, kuma yana ji a jikinsa inda ya ga ta shiga da safen nan ne gidansu, ko yanzu ya so a ce babu Daddy da sai ya tambaye ta ko da sunanta ne.
Direba yana É—an waige-waige domin zai haura hancin motar saman titi, a daidai nan Daddy ya lura da Ibrahim ya juya bayansa yana kallon waje daga cikin motar, a nutse Daddy ya ce
"Mu'azzam" Amma da yake ya yi nisa bai san Daddy ya kira shi ba, duk da suna zaune a kusa da juna, sai da Daddy ya maimaita ya ce
"Mu'azzam" Ya faɗa yana ɗan taɓa shi, sannan ne Ibrahim ya juyo da sauri yana ɗan murmushi ya ce
"Na'am Daddy" Daddy da ɗan mamaki a fuskarsa ya mayar da hankalin wajen da Ibrahim ɗin yake kallo a ƙoƙarinsa na ganin ya hangi abin da ya ɗaukewa tilon ɗan nasa hankali. Sai dai iya ganinsa bai ga kowa ba, saboda wajen akwai mutane kowa yana dabgar gabansa sannna ita wacce Ibrahim ɗin yake kallo wato Jidda ta riga ta miƙe ta yi ɗan nisan da Daddy ba zai fahimci ita Ibrahim yake kallo ba, kuma ko da a ce ya hango ta ba lallai ya kawo cewa ita ɗan nasa yake kallo ba kasancewar ba halayyar Ibrahim ɗin ba ce kallon mata don su a halin da ake ciki ma yanzu burin su bai wuce ya fitar da mata su masa aure ba, amma ya ƙi sai ya ce wai akwai lokaci!.
Daddy kallonsa ya mayar kan Ibrahim lokacin har sun haura kan titi direba ya É—au hanya ya ce
"Mu"'azzam mene ne ya É—auke maka hankali har ya hana ka jin kirana?" Murmushi Ibrahim É—in ya yi ya ce
"Kawai dai ina kallon jama'a ne Daddy" Ya faÉ—a saboda ba ya son ya faÉ—awa Daddy cewa mace yake kallo ya san idan ya faÉ—a masa gaskiyar abin da yake kallon shikenan kuma yau haka za su wuni suna tsokanarsa shi da Mummy.
ÆŠan zantawa suka shiga yi a tsakaninsu irin na É—a da uba.
A ɓangaren Jidda kuwa lokacin da ta isa gida ta tarar Aliya da Umma suna zaune a baranda a tabarma suna hira, Aliyar tana cin abinci, babu wanda ya amsa sallamar da ta yi sai ma wani kallon tsana da ƙasƙanci da Ummar take bin ta da shi.
ÆŠaki ta nufa ta ajoye jakar hannun ta, ta cire hijabin ta fito ta É—auki ruwa a buta ta shiga banÉ—aki, ruwa ta kama ta fito dama fashin sallah take shi ya sa bata ma yi sallah a makaranta ba. Sai da ta zo saitin su Umma ta ce
"Umma ina abincina?" Kallon sheƙeƙe Umma ta mata ta ce
"Wanda kika kawo na ajiye miki?" Ta faÉ—a tana kallon Jidda da take wasa da yatsun hannun ta.
Jin bata amsa mata ba ta ce
"Na ce wanda kika kawo min in dafa miki?" Kai ta girgiza, sai Ummar ta ce
"Tun da kin san baki kawo ba kar ki tambayeni"
Aliya jin ta ƙoshi sai ta ajiye cokalin ta ture plate ɗin gabanta ta saki wata gyatsa, haɗe da komawa ta kwata tare da ɗora kanta a kan cinyar Umma tana mai cewa
"Wash Allah na ƙoshi kuma na gaji"
Umma ta ce
"To ba sai ki huta ba, dama an je ana taa gwagwarmayar jarabawa, Allah dai ya baki sa'a"
Aliya ta ce " Amin Ummana, ai daɗin mai uwa a gaban murhu sai ya ci ya ƙoshi"
Jidda jin wannan furucin ya sa ta tuna da tata mahaifiyar hakan ya sa ta ji ƙwalla ta taru a idanunta yanzu shekara goma sha ɗaya kenan da ƙada ta rufe idanunta idan ta tuna lokacin mahaifyarta tana raye duk abin da ta ci sai ta ajiye mata, ko da bata nan haka za ta ajiye mata wani lokacin ma ita ta haƙura ta ajiye mata, amma yanzu mutuwa mai rabawa ta raba su, mutuwa mai yankan ƙauna ta raba tsakani.
Ɗaki ta nufa ta je ta hau kan ƙaramar katifar ta, kwantawa ta yi rubda ciki ta ɗora kanta a kan filo, idanu ta lumshe tana jin yadda yunwa takr addabar ƴaƴan hanjin ta, wanka ma take son yi amma kuma yunwa ba za ta barta ba.
Idanu ta rufe wasu zafafan hawaye suna gangarowa, tana jin tamkar yau ne ta rasa mahaifanta, tana jin kewarsu a zuciya da ruhinta, abubuwan da suke faruwa bayan mutuwarsu masu É—aure kai da kuma al'ajabi su ne suke saka take ta tunanin shin dama haka rayuwa take?.
Juyi ta yi sai kuma ta ji Umma tana ƙwala mata kira, da sauri ta tashi zaune tana goge idanun ta, sai da ta tabbatar cewa babu hawayen sannan ta fito ta ce
"Gani Umma"
Umma ta ce
"Gashi nan sai ki ɗauka, wato kin je ɗakin kin ƙule sai ya dawo ya zaci wani abun aka miki ya ishe mutane da tambaya" Ta faɗa tana turo mata plate ɗin da Aliya ta ci abinci ta rage, kaɗan aka ƙara abincin a kan sauran Aliyar, ba tare da ta ce uffan ba ta ɗauka ta juya tana dab da shiga ɗaki Aliya ta ce
"Eh mana kya É—auki ki tafi ai ko godiya babu, tun da ga baiwar ki da kika ajiye ta girka miki ta dafa ta baki" Juyowa Jiddan ta yi ta ce
"Na gode Umma Allah ya saka fa alkairi" Ta faÉ—a jin Ummar bata amsa ba kuma dama ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne, sai ta juya ta shige É—akin.
Tas ta cinye abincin duk da bai wani ishe ta ba, amma dai ta ji yanzu ta dawo dai-dai shiru ta yi tana tunanin mai ya sa Umma ta sauya, mai ya sa a da can baya lokacin iyayenra suna raye bata nuna ta tsane ta ba sai yanzu? Mai ya sa a da take nuna mata ƙauna daga ita har Aliya amma yanzu tamkar basu taɓa son ta ba ma. Ta jima tana saƙa da warwarar kafin ta fito da kwanon lokacin ana kiran sallar la'asar banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito Umma ta kalle ta ta ce
"Haka kawai kike yi wa mutane wasan ruwa da sabulu, abin da duk wankan da za ki yi ba sauyawa ,a ki yi ba kina nan a baƙar ki" Bata ce komai ba ta shige ɗakin.
Bayan ta saka wani kayan ta ɗakko kayan ta da ta ɗora a kan ƙofa da safe ta haɗa da wanda ta je makaranta da shi ta wanke ta shanya. Ganin rana ta yi sanyi ta sharo ɗakin nasu duk da babu datti, tsakar gidan ta fito ta share tas ta kwashe. Kayan wanke-wanke ta haɗa ta wanke, bata gama gyaran gidan ba sai da la,asar lis.
Butoci ta ciccika ta ajiye, lokacin Aliya suna ɗaki ita da ƙawarta Amatullahi.
Tahowa ta yi za ta kai kwando kicin cikin rashin sani ta bige Umma da ta fito daga kicin, a ƙufule Umma ta ɗaga hannu za ta wanke fuskar Jidda da mari, a daidai nan Abba ya shigo da sallama, turus ya yi yana kallon Umma...
MAMAN AFRAH
09925576222
*🩺 GHT HERBAL SOLUTIONS 🩺*
*Maganin da ke dawo da lafiya, da izinin Allah!*
Muna sayar da ingantattun magunguna na zamani da aka gwada kuma suka shaida aiki.
*Duk wannan cutar ana warke wa sosai mutum ya dawo nml*