Sashe 13
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Jiddaaaa" Yana mai jan harafin ƙarshe na sunan nata, ya jima a haka har sai da aka fara kiran sallar magriba ya tashi tare da gyara kujerar ya mayar da ita daidai ya mayar da hannunsa kan mukullin motar ya kunna tare da fara ƙoƙarin janta duk da yana jin tamkar jijiyoyin jikinsa sun daina aiki, kamar dai ba zai iya jan motar ba, yana ƙoƙarin yin kwana, sai ya ga wani mai mashin da yake ɗauke da wani mutumi ya tsaya a take mutumin ya sauka yana sanya hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙawa mai mashin ɗin, yana bashi ya juya ya fara tafiya mai mashin ɗin yake miƙa masa canji amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya bar shi, haka ya shiga magana shi dai Ibrahim kasancewar ba a kusa yake ba bai ma san mai yake cewa ba sai dai ya san godiya yake masa.
Mai mashin ya ja mashin É—insa ya yi gaba, a inda Ibrahim ya bi bayan Abba da kallo har ya shige cikin gidan da ya ga Jidda ta shiga.
Sosai ya yaba da yanayin dattijon kuma daga gani ya san tabbas yana da dattako da tsayuwa a kan iyali.
A zuciyarsa ya ce
'Wannan ne mahaifin Jidda kenan?'Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma yana ta tunanin wace ce Ummar da ya ji Jidda ta ambata tana maganar za ta mata gorin aure, in dai kuwa haka ne to tabbas ba mahaifiyar Jidda ce a gidan ba, ko dai mahaifiyarta ta mutu ko kuma bata gidan sun rabu da mahaifin ta, a take ya ji wani tausayinta haɗe da zazzafan son ta ya ƙara dirar masa, sosai yake jin son ta a jiki da ɓargonsa ya yadda yake jin tozalin da idanunsa suka yi da ita yau sai ta ƙara fasa masa wani sabon son don tamkar ta motsa masa mikin da yake cikin zuciyarsa ne.
Haka ya baro unguwar ransa duk babu daɗi, gashi babu biyan buƙata sannan kuma ya yi wani mugun jin da zai hana zuciya da ruhinsa sakat. A daidai wani masallaci ya yi parking daga can gefe fitowa ya yi alwala ya yi ya bi jam'i sai da ya idar sannan ya shiga mota ya ƙarasa gida ransa duk wani iri, tabbas ya faɗa tarkon so son ma na wacce bata san yana yj ba, son da zai ringa saka shi fargaba tun da bashi da tabbacin mallakar wacce yake yi wa so ɗin.
Yana shawo kwanar gidansu ya figi motar da mugun ƙarfi, don yanzu hatta motar ma haushin ta yake ji, a yau ne ya ji ya tsani kuɗi da kuma kyawun da yake da shi, yana ta tunanin cewa da shi mummuna ne kuma talaka babu abin da zai hana shi tunkarar Jidda a yau. Sai dai ta wani ɓangaren ya ji daɗin jin furucin ta ko ba komai zai yi amfani da damarsa wajen kaɓa zuciyarta sai dai ya san abin da zai yi.
Horn yake da ƙarfi mai gadi da yake sallah bai zo ya buɗe ba, shi kuma bai fasa doka horn ɗin ba. Ya jima yana yi duk da ya san mai gadi ba zai ƙi buɗe ƙofa da gamgan ba, mai gadi ko da ya yi sallama daga sallah sai da ya karanta gabaɗaya azkar ɗin da ake yi bayan idar da sallah, sanna ya taso a nutse ya wangale ƙofar, ya ja baya Ibrahim ya shigo da motar da gudu yana yin wani parking a tsakiyar wajen. Fitowa ya yi daga motar mai gadi duk sai ya sha jinin jikinsa ya ɗauka ko shi ne ya ɓatawa Ibrahim ɗin rai da bai buɗe ƙofa da wuri ba, da sauri ya ƙarasa yana mai cewa.
"Afwan yallaɓai ina sallah ne" Hannu kawai ya ɗagawa mai gadin ya shige cikin gidan, bai bi ta kan part ɗin Mummy ba direct part ɗinsa ya nufa yana ta sauri shi kanshi bai san dalilin saurin nashi ba.
Yana shiga bai tsaya a falo ba ya shige bedroom wayoyinsa ya É—ora a kan madubi ya cire hula da rigar jikinsa ya cilla kan gado agogon hannunsa ya cire ya ajiyee yana hango shi a madubi sanye yake da farar singlet fara tass tamkar takarda sai wandon yadin da ya cire rigar, hasken fatarsa da kwantaccen gashin sa tamkar ba'indiye shi ya sa ya ji zuciyarsa ta tsinke saboda tunowa cewa masoyiyarsa bata son kyakkyawan namiji.
Kan gadon ya koma yana ture hula da rigar da ya cire gefe don ba al'adarsa ce jefar da kayansa a kan gado ba shi mutumin ne mai tsafta. Amma yau yanayin da ya shiga ya sa yana abu wanda ba halayyarsa ba. Tashi ya yi ya kunna AC haɗe da ƙure mata gudu a take sanyi ya haɗe ɗakin duk a nufinsa ya samu sassaucin zafin zuciyarsa da yake azalzalarsa na rashin wacce yake so. Ya koma ya zauna wayarsa ta fara ƙara amma bai tashi daga zaunen ba, har kiran ya tsinke, wani ya shigo sai a karo na uku sannan ya tashi ya ɗakko wayar ganin suna Mummy ɓaro-ɓaro ya yi saurin ɗagawa tana tambayarsa rashin shigowarsa ɓangarenta ya sanar da ita wanka yake son yi sai lokacin ta ji ɗan dama a ranta don ta san da wuya Ibrahim ya shigo gida bai fara shiga part ɗinta ya ganta ba. Suna gama wayar kiran Abeed ya shigo ɗagawa ya yi suka yi magana ya ajiye ya koma ya kwanta reran a kan gadon idanunsa a rufe yana ta nemawa kansa mafita.
Zuwa can ya tashi zaune kamar an tsikare shi da sauri ya ɗakko wayarsa, sunan direbansa ya kamo hannunsa har rawa yake don yana ganin wannn hanyar ce zai bi ya samu mallakar Jidda don zai yi duk yadda zai yi ya samu soyayyarta ya kuɓuto ta daga gorin da ya ji tana furtawa da bakinta cewa za a yi mata idan bata samu miji mai auren ta ba. Bugu ɗaya biyu direba ya ɗaya ya ce
"Barka da dare yallaɓai" Ya faɗa cike da girmamawa. Amma maimakon Ibrahim ɗon ya amsa sai ya ce
"Ina za a samu kayan gwanjo?" Tambayar ta zo masa a ba za ta amma sanin kyauta irin ta yallaɓai ɗin sai ya yi tunanin ko kyauta zai yi da su, duk da ya san kaya sabbi dal yake bayarwa.
"Za a samu wane iri?" Ya faÉ—a yana jiran jin amsar sa
"Daidai ni?" Maganar ta zo masa a bazata amma sai ya ce
"Ana samu yallaɓai akwai wani abokina maƙocinmu ne ma yana buɗe dila ta kaya kuma masu kyau kamar sabbi... Kafin ya gama magana Ibrahim ya ce
"Bana son wanda suke kamar sabbi na fi son tsoffi wanda suka ji joki idan son samu ne ma wanda suka fara gashi" Shiru direban ya yi sai kuma ya ce
"To yallaɓai sai dai a karɓo ƙarshen dila irin wanda aka gama zaɓewa aka bari su ne wanda ake karyar da farashin su saboda tsufansu"
Ibrahim ya ce
"Yawwa su zan saka maka kuÉ—i a account yanzu ka je ka samo min su" Amsa masa ya yi da
"To" Ƙit ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya.
Haka direbansa ya kawo masa kayan cikin wata bakko don kuɗin da ya tura masa ko rabi ba a ɗauka ba, part ɗinsa ya kai masa ya bashi umarnin tafiya tare da crwa ya riƙe sauran kuɗin. Direban yana fita ya buɗe kayan da sauri yana fito da su, sosai sun ji jiki ba ma wannan ba warin da kayan suke irin na gwanjo su ne suka sa ya kusa yin amai, waya ya ɗaga ya kira mai wanki ya bashi kayan ya ce a wanke amma kar a goge, don a ransa ya san ba zai iya saka su babu wanki ba, don ba don Jidda ba babu mai saka shi saka gwanjo.
Yana ɗaukan kayan shi kuma ya fito ya nufi part ɗin Mummy don lokacin har ya yi wanka ya saka wani kayan sun je masallacin isha'i da Daddy, a falon ya same su yana shigowa cike da kulawa suka tashi suka nufo shi, kowa ya rungumi gefen ɗaya daga jikin Ibrahim ɗin suna matuƙar son ɗan nasu. A haka suka ƙarasa saman dining ɗin in da Mummy da Daddy suka kama shi cike da kulawa suka zaunar da shi a kujera, Mummy tana dariya cike da wasa ta ce
"Haba Daddyn Mu'azzam ya kake neman kayar min da ɗa bai gama zama ba fa ka janye hannunka" ,Ta faɗa tana kallon Ibrahim da yake ta murmushi kyawawan haƙoransa a waje. Daddy ma cike da wasa ya ce
"Wai kina nufin kin fini son shi ne?"
Mummy ta ce
"Eh mana"
Daddy ya ce
"To bari mu ji daga bakin Ibrahim ɗin, Mu'azzam tsakanin ni da Mummynka wa ya fi son ka kuma wa ka fi so?" Ya faɗa yana daga tsaye har da kama tsantsa shi ala dole yana jiran ya ji mai za a ce kar a je ba a zaɓe shi ba.
Mummy kuma ta kasa tsayar da dariyar da take marar sauti, shi kuma Ibrahim yana ta kallonsu ɗaya bayan ɗaya yana tunanin ta inda zai ɓullowa wannan diramar tasu.
Mummy ta ce
"Kai muke jira"
Ibrahim ya ce
"Duk kuna sona na sani, ni kuma na fi son...
Kowa ya yi saranda yana jiran kar a zaɓi ɗan uwansa ba zaɓe shi ba, kowa ya san idan ba a zaɓe shi ba za a masa dariya. Kamar daga sama suka ji Ibrahim ya ce
"Ni kuma ina ƙaunarku ku duka" Gabaɗaya sai aka kaure da dariya Mummy da Daddy suka nemi kujerarsu suka zauna, Mummy ta zubawa kowa abincin suka shiga ci cike da annashuwa.
Bayan sun kammala suka koma tsakoyar falon suna tattaunawa, a nan mai aiki ta shigo ta kwashe kwanukan ta tsafta ce dining É—in.