← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 106

Sashe 18

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oho sai yanzu na je ghana, kai duniya mutane sai a barsu, wato dai Allah ya tona maka asiri ashe dai ganin kana da kyau shi ya sa kake aron mota da kaya masu kyau kana yaudarar Æ´aÆ´an mutane ko? Har da aron direba da yake janka a mota, wato ka zaci ba zan gane ka ba, to ta Allah ba taka ba wannan ai kai ne a wanki gara!" Ta faÉ—a tana wani zagaya shi, gabaÉ—aya sai Ibrahim ya kasa magana ita kuma ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har da faÉ—in É—an talaka dama bai iya samun wuri ba wato har da cewa wa yake nemanta lokacin da ta je wajensa a motar ashe dai duk kanwar ja ce shi ma dai talaka ne bai ajiye ba bai bayar ajiya ba.

Shi dai yana kallon ta tsabar mamaki ma ya rasa mai zai ce.

Ganin haka sai ta ce

"Shi ne ka lallaɓo koɗaɗɗun ƙafafunka da wasu tsoffin kayanka sa suka gaji da wanki, to wallahi ni na fi ƙarfinka ne, kar ma ka ɓata lokacinka wajen mini magiya ko roƙona don ina cikin mutanen da suke cewa da wuya ta kar su ai gwara daɗi ya kar su"

A can cikin gida kuwa Umma ce ta ce Jidda ta ɗauki bokiti ta fita famfon waje ta ɗakko ruwa ta ƙarasa wankin, da yake ruwan ya ƙare, duk da akwai mai ruwan da yake kawo musu ruwa amma saboda ta ga Abba ba ya nan ta aike ta ɗakko ruwan, haka ta ɗauki bokitin ta fito ba don ta so ba.

Aliya tana cikin masa wannan maganar har wani nuna shi da yatsa take a daidai nan ne Jidda ta fito, sai da gabansa ya buga da ya ganta sanye take da wani blue ɗin hijabi har ƙasa hijabin yana da hannu sai bokiti a hannunta fuskarta babu walwala. Tun da ta fito kallo ɗaya ta musu ta wuce da yake wajen famfon kusa da gidan da yae kusa da gidansu ne ta tara ruwan ta ciko ta ɗakko.

Ta zo za ta shige gida ganin abin da Aliya take yi wa Ibrahim sai ta ce

"Haba Aliya, a titi kike wannan É—aga muryar?"

Cike da É—aga murya ta ce

"An yi É—in uwar pan shishshigi" Juyawa ta yi ta shige gidan, shi kuma kallon ta kawai yake yana son ganin gudun ruwanta, sai da ta gama masa É—iban albarka ta ce

"To a yi gaba ko a samu wata dai amma wannan Aliyar sai Kasim!." Tana faÉ—a ta juya ta tafi tana wani juya mazaunan da su da babu duk É—aya.

Gefe ya koma yana ƙarewa jikinsa kallo yana mamakin cewa kenan dai shi talaka a wajen wani shi ba komai ba ne, sannan wasu suna ganin duk rashin mutuncinka in har kana da kuɗi to kai mai kirki ne in kuma baka da shi da kai da babu duk ɗaya, dama ya fahimci cewa Aliyar nan ƴar son banza ce don ranar ma a idanunta ya ga son banza ƙiri ƙiri.

Ko da ta je gidansu Amatullahi nan ta shiga bata labarin Ibrahim suka ringa zaginsa suna ce masa matsiyaci, Aliya ta ce

"Oh har zan ce in yi saki na dafe da Kasim ɗina ashe dai ba arziƙi ba ne yake kirana tsiya ce"

Amatullahi ta ce

"Humm! Ba ke kike cewa wani kyakkyawa ba ne"

Aliya ta ce

"Ke dai bari a yau na gane cewa duk arahar kunu ta banza ce in babu gaya a ciki" Suka ci gaba da É—aga kayan Kasim suna zuba masa albarka.

Fitowar Jidda za ta ƙaro ruwa sai ta gan shi jingine da bango, amma sai ta masa kwarjini ya kasa mata magana har sai da ta ciko bokoti tana ƙoƙarin ɗakkowa ya ƙarasa wajen ya ce

"Kawo in taimaka miki" Kawai da ta juyo sai ta kasa hana shi kwarjini ya mata ta ga yana da kima da kuma kamala. Ɗakko mata ruwan ya yi har ya kawo ƙofar gidan, kasancewar ya saba ruwa a banɗaki sai dai ya tara ya yi wanka tunaninsa zai ji nauyin bokiti amma da yake soyayya yake yi wa bauta sai ya ji ko alamar nauyi babu kamar dai ya ɗauki bokiti mai auduga ne. Yana zuwa ya ajiye ya ɗago yana kallon ta cike da jin daɗin abin da ya mata ta ce

"Sannu da ƙoƙari na gode ƙwarai"

Wani daÉ—i ne ya cika shi kamar ya taka rawa jin muryarta tana masa godiya da jinjina masa.

Har za ta É—auki bokitin ta juyo ta ce

"Don Allah ka yi haƙuri abin da Aliya ta farfaɗa maka" Yana jinjina dattakon ta ya ce

"Ni dama ...am dama ke zan ce ta yi min magana da ke shi ne ... Ya faÉ—a yana inda -inda

Cike da mamaki ta kalle shi tsantsar mamaki yana bayyana a kan fuskarta ta ce

"Ni kuma?" Ta faɗa zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, ta san dai jiya ta yi ta addu'ar ita ma Allah ya fito mata da mai son ta wanda zai aure ta ya riƙe ta da daraja idanu ta ɗan runtse ta buɗe ta ce

"Lafiya dai ko?"

Yana kallon yanayin ta ya ce

"Na zo don in bayyana miki soyayyata wallahi ina ƙaunarki da gaskiya tun daga ranar da na fara tozali da ke" Ya faɗa zuciyarsa tana zillo kawai gani yake ba za ta amince da shi ba saboda kyaun da yake da shi tun da da kunnensa ya ji ta ce bata son mai kuɗi kyakkyawa.

Jidda kuwa jikin ta ne ya fara rawa kasantuwar abin ya zo mata a bazata, kuma dai mutumin ya birge ta musamman da ta ga cin mutuncin da Aliya ta masa bai biye mata ba duk da bata san abin da ya haÉ—a su ba sannan da taimakon ta da ya yi ya É—aukar mata ruwa.

Rasa amsar da za ta bashi ya sa ta ce

"Sai na yi tunani tukunna"

Wannan furucin nata ya saka shi a wasi-wasi amma ya danne ya ce

"Babu damuwa Allah sa ki yanke abin da ya fi zama alkairi " Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta ji wani iri kamar dai bata kyauta masa ba kamar dai bai ji daÉ—in furucin ba.

Bata ce masa komai ba ta sunkuya ta É—auki bokiti har ta fara tafiya ya ce

"Jidda" Har tsakiyar kanta ta ji kiran sai ta ji tamkar shi kaÉ—ai ne ya iya kiran sunanta daidai, sai dai bata san dalilin hakan ba, juyawa ta yi bayan ta ajiye bokitin ta ce

"Na'am" Ta faɗa idanunsu suna sarƙewa da juna da sauri ta yi saurin kawar da nata, kasancewar sai ta ji kallon da idanunsa suka jefe ta da shi ya sha bamban da kallon kowane mutum.

Iska ya É—an hurar daga bakinsa ya ce

"Ki daure ki bani phone no ki" Kamar ba za ta ce komai ba har ya cire rai za ta bashi sai ya ji ta fara karanto masa, nan ya shiga rubutawa a ƙaramar wayar da ya taho da ita. Tana gama faɗa masa va tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta ɗauki ruwan ta shige gidan.

Tsabar murna bai san ya isa bakin titi ba don ko wahalar tafiyar ba ya ji, wani irin farinciki da yanayi marar misaltuwa da yake ziyartarsa, haka ya yi kwanan farinciki amma dai ya kasa kiran wayarta don sai ya rasa mai zai ce idan ya kira.

Bayan kwana biyu, har lokacin bai koma gidansu ba kuma bai kira ta ba, sai dai yana ta dakon soyayyarta. A ɓangaren Jidda tun daga wannan ranar ta ji ta damu da Ibrahim sai dai rashin kiranta a waya sai ta ji duk babu daɗi, tun tana jiran kiransa har ta cire rai, da ko baƙuwar no ta gani sai ta yi tunanin shi ne har dai ta cire rai daga kiran nasa. Sai da aka yi sati sannan watarana da yammaci yana zaune a ƙasan wata bishiya a wata unguwa yammaci ne mai cike da ni'ima sassanyar iska tana kaɗawa, yana zaune saman motarsa ya kamo sunan ya shiga kiranta, Jidda tana hura wutar da take tuwon dare ta fara jiyo ƙaran wayarta, amma bata je ta ɗakko wayar daga ɗaki ba. Har kiran ya tsinke bata je ba, Ibrahim kuma sai ya fara wata zufa hankalinsa ya tashi ya fara tunanin ko dai ta yanke shawara marar kyau a kansa, kuma da ya yi tunanin ai bata san numbersa ba sai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanata a ƙara gwada kiran.

Tunanin ta ma ko Salama ce ita ce idan ta fara kira bata san ta daina ba, hakan ya sa ta iza wutar ta nufi ɗakin, tana ɗaukan wayar ta ga baƙuwar no dama gidan babu kowa sai ita kaɗai duk sun fita gidan biki. Bata san mai ya sa ba amma sai da gabanta ya faɗi tana dannawa ta ƙara wayar a kunne.

Sassanyar muryarsa mai amo mai daÉ—i da ita ya fara mata sallama, idanu ta lumshe kaÉ—an ta buÉ—e su bata san dalili ba amma sai ta ji ta yi farin ciki da kiran, bata san ko don ta daÉ—e tana jiran ya kira ta ba ko kuwa mene ne oho.

Amsa sallamar ta yi sai ya ce

"Sunana Ibrahim ni ne kika ba numberki ranar da kika ɗauki ruwa" Wani murmushi ya kuɓuce mata marar sauti a zuciyarta tana raya da a ce ya san cewa bata da wani saurayi da bai wahalar da kansa wajen tuna mata ranar da suka haɗu ba.

Cike da murnar da bata bari ta bayyana ta a fili ba ta ce

"Na gane ka"

Ya ce

"Ya batun tunanin kin yanke hukuncin"

Ta ce

"Hukuncin me?"

Ya ce

"Hukuncin na cancanta ki kula ni ko ban kai ki kula ni ba" Maganarsa ta bata dariya hakan ya sa ta dara har yana iya jiyo sautin dariyar ta cikin wayar.

Jingina ta yi da bango ta don dama a tsaye take ta ce

"Ban amince ba" Gabansa ne ya buga da ƙarfi a take ya ji gabaɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, ɗan walwalar da ya tsinci kanaa sanadin magana da ita duk sun gaushe.
Chapter 18 · 0% Book details