← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 106

Sashe 35

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani abu ne na ji ya cije ni a ƙafa ta" Ƙofofin motar aka buɗe suka suka fito sauran jama'a kuwa da basu san mai yake faruwa ba duk sun fito daga motocinsu suna shige ciki suna son ba idanunsu abinci domin su kashe ƙwarƙwatar idanunsu, haske-haske aka shiga yi ƙasan kujerun amma ba a ga komai ba, har ma ana tunanin ko kunama ce amma ta ce ba kunama ba ce. Ƴar uwar Umma ce ta kama lafayar ta rufa mata tare da riƙe hannunta, a inda ƴar uwar Abba ta kama Jidda wacce duk ta shiga damuwa da yanayin da ta ga Aliya.

Ƙofar sa za ta sada su da ainihin cikin gidan suka nufa mata sai sakin guɗa ake yi, amma Aliya suna dab da shigewa ƙofar ta ja ta tsaya ta ce

"Aunty ni ba zan shiga ba" Ƴar uwar Umma ta ce

"Me ya sa mu shiga mana ki raka ƴar uwarki kin san dai ba zama za a yi ba yanzu za a fito a tafi raka ki naki ɗakin, kuma kin san dai Abbanku yance hatta ƙawaye kar a bar kowa a gidan amarya su zauna wani siyan baki gabaɗaya za a tafi a bar amarya" Aliya wacce take jin idan ta shiga ciki ta ga ɗakunan tamkar za ta haɗu da taɓin hankali hakan ya sa ta ƙara togewa duk wanda ya zo sai ya raɓe su ya wuce. Ƴar uwar Umma ta rasa ya za ta mata gashi dai ita bata shiga ba, suna nan sai ga wasu daga cikin matan sun fara fitowa suna shiga mota hakan ya sa Auntyn ta kama Aliya ta mayar da ita motar duk da motar ma tana ɗaya daga cikin motocin da suka zo ɗaukan Jidda daga ɓangaren Ibrahim.

A can ciki kuwa tun da aka shiga da Jidda bata bari addu'a ta kufce mata ba, don sai da ta yi lokacin fitowa daga gida, da za su shiga gidan nata ma ta yi a zuciyarta duk da lokacin ne Aliya ta tada musu hankali. Har aka zaunar da ita a bakin gado tana ta maimaita addu'o,in neman tsari inda mutane suke ta mata sam barka da addu'ar zaman lafiya, wasu kuma ƴan baƙin ciki suna taɓe baki musamman Amatullahi ƙawar Aliya wacce take jin haushin ni'imar da Jiddar ta samu, wasu kuma suna mata fatan alkairi, wasu suna jin dama su ne suka samu wannan daukar da wannan kyakkyawan mijin, don kana shigowa babban falon da tangamemen hoton Ibrahim za ka ci karo yana wannan kyakkyawan murmushin nasa mai tafiya da zukatan ƴan mata da yawa!.

Jidda tana bakin gadon a zaune tana lulluɓe kanta a sunkuye sai wasa take da yatsunta da suka sha kyakkyawan ƙunshin baƙi da ja duk da kasancewarta baƙa amma lallan ya haska hannun tamkar ka gudu da hannun. Sai dai idanunta yana ta hawaye rana ta tuna mahaifanta sannan zuciyarta a cunkushe da damuwar da ta lura ƴar uwarta Aliya. Salama ce ta je ta dafa ta ta ce

"To amarya za mu tafi sai mun sake dawowa, a toh wallahi ba don Abba ya hana a zauna ba da sai na jira zuwan abokan ango!" Ta faÉ—a tana dariyar wasa Jidda ta buÉ—e dashashshiyar muryarta ta ce

"To yanzu ma sai ki zauna" Murya Salama ta rage tana magana ƙasa-ƙasa ta ce

"Ko na zauna na miki zaman É—aki?" Daga cikin lafayan take kallon ta Jidda da take kallonta don ta san zolayarta ne take yi.

Jin Jiddar bata ce komai ba sai ta É—ora da faÉ—in

"Taɓ ba zan zauna ba wannan angon naki ya yi ƙuli-ƙulin kubra da ni don daga gani ya shiryawa wannan ranar a toh za a kashe arna" Wata ƙawarsu da ta zo kusa da su ta ce

"Ai yau angon nan va arna kawai zai kashe ba musulmin ba ba zai barsu ba" Suka fashe da dariyar zolaya ita da Salama duk Jidda tana jinsu. Jin ana ta horn suka fara mata sallama suna fitowa.

Ƴar uwar Abba ko da ta fito ganin Aunty da Aliya a tsaye a gefe da Amatullahi ta ce

"Haba Aliya ai dai kin raka ƴar uwarki ɗaki kun yi sallama amma ji zo har cikin gidan baki shiga ɗakin ba wannan ai sai wani ya ɗauka wani abu ne, kin san dai mutane ba a iya musu" Jin hakan sai Aliya ta yi tunanin kar Jidda ta yi tunanin wani abu da ban hakan ya sa ta ce za ta shiga don yanzu ba ta son wani abu da zai nuna rashin ƙaunar Jidda a tattarw da ita, duk da ta ciki na ciki, ta fi so suke basaja kamar yadda suka shirya hakan da Umma.

Ƴar uwar Abban ce ma ta kama hannunta suka nufi ciki, Aliya daga cikin laffayar ta kafe hoton Ibrahim da yake kafe a falon a take ta ji wani abu ya tsarga mata, tana tunanin da a ce ita ce yau a wannan gidan da kuma wannan mijin lallai da ƙawaye da dangi sai sun raina kansu amma dai gashi Allah ya san halin jaki da bai bashi ƙaho ba!.

Dakyar take taka ƙafafunta daurewa kawai take, a haka suka wuce ɗakin da Jidda take wanda a ƙasa yake ba a sama ba, wani sanyi da ni,imtaccen ƙamshin turarukan wuta wanda aka siya a wajen Zainab Muhammad tahir wacce take da zafafan turarukan wuta ƴan sudan kowa ya san yadda turarukan wutan sudan suke da ƙamshi nata sun sha bamban domin turarukan wutan suna kama ɗaki ƙamshin su mai daɗi da sanyaya rai 0814 209 8878 ta number wannan suka mata magana suka mallaki nasu ga duk mai buƙata zai mata magana tana siyar da ɗaya tana bada sari a farashin sauƙi siyan na gari mayar da kuɗi gida!.

Yanayin yadda kayan ɗakin suka karɓi ɗakin tamkar dama don su aka ƙera ɗakin tangameman wadataccen ɗaki, Allah ne kawai ya sa Aliya bata yanke jiki ta faɗi ba, ko da suka shiga ɗakin cikin ƙarfin hali ta furta

"Jidda!" Jidda ta ɗago kai tana kallon Aliya ta amsa kawai sai Aliya ta je gaban gadon ta rungume Jidda tana sakin kuka, a zahiri kukan rabuwa ne amma a baɗini kukan baƙin ciki ne. Jidda ma ta fashe da kukan sai da suka yi mai isar su ƴar uwar Abban tana basu haƙuri kafin Aliya ta ce

"Jidda ƴar uwata ƙawata da bani da tamkar ki, mun zauna shekara da shekaru amma yau aure zai raba tsakaninmu sai dai zumunci amma babu kwanan gida ɗaya a ɗaki ɗaya, ina roƙon ki yafe min iya zamanmu sannan ina miki fatab alkairi" Jidda jin kalaman bogin da Aliya ta yi sai zuciyarta ta yi rauni hakan ya sa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tana cewa ta yafe mata ita ma ta yafe mata, haka aka fita da Aliya rai cike damƙuna da hassada!.

Sun saka ta a mota tana ta kuka wanda kukan ya zame mata biyu, hassada babban ciwo da kuma kukan zuwa gidanta da take ganin bashi da maraba da kurkuku a wajenta ita yanzu sam Kasim ba ya birgeta. Jidda lokacin da ta ji rufowar get sai gabaÉ—aya ta fashe da kuka har da sheshsheka.

Bayan kamar minti hamsin ta ji horn da kuma ƙaran buɗe get, shigowar motoci ta ji amma dai ba za ta bambance biyu ne ko uku ba, jim kaɗan ta fara jin ƙaran rufe ƙofofin alamun fitowar wanda suke cikin motar. Hayaniya ta fara jiyowa a falon inda take jiyo muryar Ibrahim yana faɗin

"Daga na kirawo ta kun gaisa za ku fita ku tafi gwauraye su je É—akin gauranci masu aure su tafi wajen matansu" Ya faÉ—a cike da zolaya. Tana jin yadda falon ya kaure da maganganinsu amma bata iya gane mai suke cewa sai dai ta san tsiya ce suke masa don ta ji sai dariya suke yi.

Shigowarsa É—akin ya sanya gabanta faÉ—uwa, sai ta ji duk wani nauyinsa take ji tamkar dai ba wannan Ibrahim É—in nata da suke kasancewa kullum a waya suna magana ba ko idan sun haÉ—u kamar ba za su rabu ba.

Duk wata kunya ta rufe ta sai take jin dama su Salama basu tafi ba duk da ta san umarnin Abba ne hakan, amma a ganinta da suna nan za ta ji sauƙin kunyar da ta mata ƙawanya a zuciya duk da ta san dai ko suna nan dole za su tafi ba za su kwana a gidan ba. Abin mamaki lallai sai lokacin ta tabbatar maza basu da kunya ita tana jin nauyinsa da kunyarsa da ya shigo ɗakin amma shi kuma yana kusanto kansa gareta, domin bai yi wa kansa masauki a ko ina ba sai a kan gadon inda take zaune ya zauna dab da ita kafaɗarsa tana gugar tata kafaɗar, wani ƙamshin turarensa wanda take jin na yau ya sha bamban da na kowacce rana ko don kasancewar yau ranar ta musamman ce a tarihin rayuwarsu Allah masani. Yana zama sai ta ji tamkar ta nutse jin jikinsa yana gugar nata, abu ne sabo tsakaninsu da bai taɓa faruwa ba ko ta ce abu ne sabo wanda a iya rayuwarta bata taɓa kasancewa da wani ɗa namiji da kusanci kamar hakan ba, sai ta ji duk jikinta ya fara wata irin tsuma.

Tana cikin wannan tunanin sai kawai ta ji ya ɗora hannunsa a kan hannuwanta da take wasa da su, wani irin yammm ta ji tamkar an haɗa shokin bata san lokacin da ta yi saurin janye hannun ba, sai dai saurin ƙara riƙo hannun nata wannan karon hannu biyu ya saka ya riƙe nata, cikin wata murya mai sanyi da daɗin amon a kunnen mai sauraro kuma ga ma,abota soyayya ya ce

"Habibty an zo lafiya?" Bakinta bai bata haÉ—in kai ba wajen bashi amsa sai ta ji ya sake É—orawa da faÉ—in
Chapter 35 · 0% Book details