Sashe 22
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta daɗe tana nazarin rayuwa kafin daga bisani ta tashi ta haɗa kayan wanke-wanke ta wanke. Kalifa da ya ƙi kwanciya saboda zafin jikinsa ta ɗauke shi ta goya shi zuwa can ta ji yana mimmiƙewa alamar tana son sauka ga wani ƙananan kuka da yake tana sakko shi ta ga har ya fara kashin kamar ta yi kuka haka ta je ta gyara shi ta dawo dasho ta kwantar ganin ya kwanta ta je ta yi wanka ta fito ta shirya. Sai neman magani take amma babu na zazzaɓi babu na gudawa gashi bata da kuɗin da za ta saya masa maganin hakan ya sa take ta takaicin rashin sana'a domin sana'a makami ce kuma jigo a rayuwa in har kana yi ko yaya za ka fi ƙarfin abubuwa.
Nasir tun da ya fito ya turawa Baba wannan kuÉ—in bayan sun yi waya, gidan Hajiya ya nufa ana sauke shi a mashin ya shiga da sallama. Bayan ya zauna ya gaishe da Hajiya Husna da Hibba suka gaishe da shi, ya amsa suna ta raha abinsu.
Hajiya ta kalle shi yana cin abincin ta ce
"Gaskiya wannan matar taka an yi makirar mata wallahi, ita kullum bata da aikin sai son ta ɓanɓari kuɗi a jikin ka, ai wallahi an kusa dai yin ta ta ƙare daga ka auri Meenal ka huta yarinya mai hankali da sanin ya kamata kuma ka ga ita ko nawa ka kashe mata baka yi asara ba amma wannan ita ƴar gidan faƙirai ba wani saba kama kuɗi ta yi ba sai shegen munafurci" Ta faɗa tana yatsina fuska. Karaf Husna ta ce
"Hajiya ai daga matar nan ta Yaya sai baya wallahi sumi-sumi kamar munafuka ko kaÉ—an bata da hali" Hibba ta ce
"Ai gwara ya auri Meenal ƴar ƙwalisa ta zo gidansa ya huta ita ma ta huta"
Hajiya ta ce
"Wallahi kuwa abinsu tuwona maina"
Sai da ya kurɓi shayinsa ya ce
"Ai ni in ban da ƙaddara babu abin da zai saka na auri Sadiya, kuma yanzu ma tun da har ubanta ya nuna zaman auren yake so ta yi to za ta rayu a wahala kuwa"
Hajiya ta ce
"Ai karka saurara mata, dama mashinshi ne ta rasa ya yaɓa maka da yake kai ne mai tsautsayin"
Suna ta faɗin maganganu a kan Sadiyar har ya gama cin abincin yana faɗar ya yi daɗi sosai, Hajiya tana faɗin ai shi ya sa ta ce ake yin abincin da shi yake ci yana murmurewa tun da bakinsa ya saba da cin mai daɗi da mai maiƙo saɓanin Sadiya da dama ta saba da cin tuwo, dubu ashirin ya fiddo ya ba Hajiya dubu goma su kuma kowa dubu biyar sai wata tsohuwar ɗari biyi da Hajiyar ta ce ya bada za a siyowa Kalifan magani, daga haka ya musu sallama ya ce ya tafi kasuwa. Almajiri aka ba ya je maƙota ya siyo maganin rana da maganin kashi na gargajiya Hajiya ta ce su je su kai mata ta haɗa musu da fanadol ta ce su kai a jiƙa a ɗura masa maganin zazzaɓin, bayan ta san maganin yara ya kamata a bashi ba na manya ba.
Basu tashi tafiya ba sai da suka gama ɓata lokaci, lokacin da suka zo ƙofar gidan da ƙafa Husna ta tura ƙofar gidan har sai da ƙofar ta bugu da jikin bango da ƙarfi wanda hakan ya falkar da Kalifa daga baccin da yake a tsorace yana kuka, ko ba a faɗa ba ta san mai mata wannan ɗabi'ar don haka kawai sai ta shiga jiran zuwan su don ta san ƙannen mijinta ne.
Hibba ta ce
"Gafaranmu dai" Ta faɗa a gadarance, amsa musu ta yi domin ta san rainin hankali ne maimakon su yo sallama shi ne suka yi hakan, tana kallonsu ta window tana jijjiga Kalifa suna ƙarewa gidan kallo labule suka bankaɗo suka shigo ɗakih suna wani yatsina suka zauna.
Babu wacce ta yi magana cikinsu Sadiya ta ce
"Su Husna ne yau a gidan namu"
Hibba ta ce
"Gidanku ai yana can gidanku sai ko ki ce yau mu ne a gidan yayanmu, kuma zuwa gidan nan ai ya zama farillah saboda gidan É—an uwanmu ne sannan kuma ki sa a ranki nan ba da jimawa ba za ku zama ku biyu don yayanmu dole a gallo sabuwar amarya irin matan da ake yayi wayyayu" Ta ji ciwon maganar amma sai ta basar ta ce
"Gidansa ne kam, to Allah ya kawo ta" Daga haka babu wacce ta tambaye ta ya maia jiki Husna ta dangwarar mata da maganin a tsakar É—akin ta ce
"Saƙo daga Hajiya ta ce gashi nan in dai magani ne da na kashin da na rana har da na zazzaɓi ki jiƙa amma batun wai kike cewa Yaya za a kai shi asibiti bai taso ba" Ɗago idanu ta yi ta kalle su kowacce ta tamke fuska a gadarance amma Sadiya bata ce komai ba sai Husna ta ce
"Wato a faɗa miki saƙon uwar tamu amma ki wofintar saboda ba saƙon taki uwar ba ne" Sadiya ta ce
"Karki zageni Husna, kuma ai na ji saƙon ta ko kin ga na yi musu" Basu bata amsa ba suka ce uhm a tare suna masu tashi suka fita, tana ji suka fice daga gidan babu wacce ta yi ƙoƙari rufe mata ƙofar gidan!.
Ledar ta ɗauka ta duba abubuwan da suke ciki tana jin babu daɗi a zuciyarta tabbas duk macen da bata yi dacen miji ba kuma vata dace da uwar miji ba, sannan dangin miji basa ƙaunarta lallai ba za take jin daɗin zaman gidan aurenta ba.
Nasir soyayya suke shi da Meenal kamar su haɗiye juna, sai dai yanayin yadda take zuwar masa da buƙatar kuɗi abin yana damunsa sai dai da ya faɗawa Hajiya sai ta ce wuyarta a yi auren za ta daina wataƙila da yarinta duk da yarinyar tana da tunani da hangen nesa in ji Hajiya.
Yau ya kama talata inda Hajiya ta sanar da ƙawarta mahaifiyar Meenal za ta kai musu ziyara. Da yammacin ne Meemal da mahaifiyarta suna zaune a falo suna hirar bikin da ake son saka rana Meenal ta ce
"Ni wallahi Momi ba don dai saboda ke ba da babu yadda zan yi in aure wannan Nasir ɗin" Ta faɗa tana jan dogon tsaki, baki Momi ta taɓe ta ce
"To ya za a yi tun da ya nuna yana son ki kuma mahaifiyarsa ma ta nuna tana ƙaunar wannan haɗin, ai sai a yi tuwona maina" Ta faɗa tana wata ƴar bazawarar dariya.
Ƙwafa Meenal ta yi ta ce
"Hummm!. Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ni wallahi ba zan ɗauki raini da cin kashin da suke yi wa wannan Sadiyar ba, tsaf za mu raba raini don wallahi ko ita Hajiyar ba saurara mata zan yi ba bare wannan riƙaƙun ƴanmatan ƙannen nasa duk sai na gasa musu ƙasa a hannu, shi kuma Nasir hummm sai ya zama mijin ta ce"
Momi ta dara har da Æ´ar shewa ta ce
"To Meenal idan baki yi wannan abubuwan da kika zayyano ba kenan ma baki cika ƴar halak ba, ai ba baiwa na kai musu ba ki ƙwatawa kanki ƴanci a gidan miji karki yarda da rainin kowane shege" A daidai nan kiran wayar Nasir ya shigo a inda hakan ya yi daidai da tsayawar napep ɗin da ya ɗakko Hajiya a ƙofar gidan su Meenal ɗin. Da sallama ta shigo gidan Momi ta amsa tana mata maraba tare da cewa ta shiga, ita kuma Meenal da sauri ta tashi ta shige bedroom tana kashe murya suka fara magana da Nasiri.
Nasir ya ce
"My love na matsu mu yi aure ko ma zama tsintsiya maɗauri ɗaya, ke ce taurauwa a gidana ke za kike murza kambunki wancan ta cikin gidan ma karki ba kanki wahala wajen sakata a layin kishiyarki don daga kin zo gidan komai ya dawo hannunki" Ya faɗa yana jin tamkar ya janyo ranar auren nasu da ba a saka ba duk da ana dab da sakawa. Wannan dariyar tata mai ƙaramib sauti wacce take nuni da tana jin kunya ita ta sakar masa tare da cewa
"Ni ka sa ina rufe fuska kunya nake ji Allah" Wani daɗi ne ya lulluɓe shi ya ji tamkar ya yi ihun daɗi don yana mugun son mace mai kunya duk da ya san Sadiya tana da kunya da kawaici amma dai shi yanzu hankalinsa yana kan Meenal ɗinsa wacce yake ji ɗaya tamkar goma, wacce kuma yake riritawa kamar ƙwai.
Hira suka ci gaba da yi tana ta nuna masa tana jin nauyinsa a inda shi kuma yake ji babu ya shi don yadda Meenal take bashi girma sai yake jin ladabin Sadiya kamar dai ma ba wata biyayya ce take masa ba, sun jima suna hirar daga bisani suka yi sallama ya kashe wayar yana sauke nannuyar ajiyar zuciya a inda a wani ɓangaren na zuciyarsa yana jin daɗi yau har sun yi waya sun gama bata buƙaci wani kuɗi daga gare shi ba, saboda ya lura ita bata san yawan tambayar abu kima yake zubarwa da mace!.Don roƙo yana taka muhimmiyar rawa wajen daƙile mutucin wanda yake roƙon, shi ya sa ma wani ya tambayi manzo S.A.W shin mai zai yi Allah ya so shi sannan mai zai yi mutane ma su so shi. Manzon Allah S.A.W ya cewa mutumin ka guji duniya Allah zai so ka, sannan ka guji abin hannun mutane mutane ma za su so ka, kenan duk wanda kake son abin hannunsa yau da gobe kimarka raguwa take a wajensa.
Suna yin sallama ta saki wani gajeran ɓoyayyan tsaki ta ture wayar gefe tare da kwantawa male-male a kan gadon a fili ta ce
"Wahalalle kawai, mutum kai baka son ka ɓamɓaru wato ka ji yau ban roƙi kuɗinka ba shi ne gudun kar na roƙa har wani saurin yi min sallama kake, ai zan shigo cikin gidan" Ta faɗa tana janyo wayat ta shiga wtsapp take ta chart ɗinta.