← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 106

Sashe 23

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falo cike da fara'a Momi ta tarɓi Hajiya a inda suka gaisa daga nan hirarsu ta ƙawaye ta ɓarke e tsakaninsu, Hajiyar tana faɗin cewa ƴan uwan mahaifin Nasir za su ji dangin mahaifin Meenal su kai kuɗin gaisuwa, saboda daga Baban Nasir har na Meenal basa raye.

Suna ta tattaunawa zuwa can sai gashi Meenal ta fito falo tana taku cike da nutsuwa, gaban kujerar da Hajiya take zaune ta je ta tsugunna tana mai sunkuyar da kai ƙasa ta ce

"Hajiya ina wuni" ,Hajiya cike da farinciki ta É—ora hannu a kan Meenal tana amsa gaisuwar tare da yaba hankalin Meenal É—in, tana ganin idan suka samu Meenal a family nasu sun warke.

Cike da ladabi ta tashi ta fita, Hajiya ta kalli Momi tana murmushi ta ce

"Ƙawata wallahi kin iya haihuwa sannan kin iya tarbiya, haka kawai ya je ya kwaso masa jangwam ai wallahi Nasir da Meenal ya fara aura babu dalilin da zai sa ya auri wata Sadiya kuma wallahi yanzu ma ruwanta ne bai ƙare ba daga zama ya ƙare dole ta fita ta bata waje saboda gidan Nasir na Meenal ne ita kaɗai" Dariya Momi ta yi ta ce

"Ai ƴarki ce komai kika yi daidai ne!." Dariya suke suna ci gaba da tattaunawa, a inda Meenal ta dawo ɗauke da ruwa da lemo a faranta sai kofi ta zo ta durƙusa cike da ladabi da zubawa Hajiya ruwan ta tashi ta bar wajen Hajiya tana ta yabawa Meenal ɗin bata san cewa lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi ba.

Ta jima a gidan sai la'asar liss sannan ta musu sallama ta fito za ta tafi lokacin Meenal tana ta aikin munfurci ita kuma Hajiya tana yaba mata a nata ganin taimakawa Momi take. Bayan tafiyarta suka zauna suna ta tsara yadda abubuwan za su kasance idan Meenal ta shiga cikin gidan.

Hajiya tana fita daga nan gidan da ta tari napep sai gidan Sadiya, Sadiya tana tuƙa tuwo lokacin Kalifa yana wasa saboda ya ɗan ji ƙwarin jikinsa ta jiyo Hajiya tana kwaɗa sallama, amsawa ta yi tana mai tasowa daga bayan ta rufe tukunyar dama ta gama tuƙa tuwon. Tun da ta shigo take yi wa gidan wani kallo na rainin wayo tana wani tattaɓe baki Kalifa kuwa kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai shi kuwa da yake ba wani shaƙuwa ya yi da ita ba wasan sa yake ko wajenta bai nufa ba.

Sadiya cike da ladabi ta ce

",Sannu da zuwa Hajiya" Bata amsa ba ta ce

"Ke dai Sadiya ki ji tsoron haɗuwarki da Allah"Sadiya tana kallonta tana jiran ƙarin bayani don ita bata ga abin da ta yi da za a mata wannan furucin ba a nata ganin ita ce ya dace da ta jefe su da wannan kalmar. Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora da faɗin

"In banda shegen son kuɗi kike ɗorawa yaro jinya ga yaro nan yana wasa amma har kina ikirarin kai shi asibiti wannan da maraya ne Nasir ba na raye kika aure shi da ya taɓa ya ji gabaɗaya sai kin talautashi a shegen kawo buƙatun naki!" Sadiya kai ta sunkuyar ƙasa ta rasa ma abin da za ta ce mata amma duk da haka sai ta yi ƙarfin cewa

"Wallahi bashi da lafiya ai shi Abban nasa ya...

Hannun da Hajiya ta É—aga mata ne ya saka ta haÉ—iye sauran maganar da ta guntso a bakinta. Hajiyar ta ce

"Ai komai ya kusa zuwa ƙarshe zai auro mace mai ladabi da tsoron Allah, mai tattala masa dukiya wacce ta san darajar dangin miji wacce za ta ɗaukeni tamkar ni ce silar zuwanta duniya" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalleta ta haɗiye ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarta, don ta ji ba daɗi da ta lissafa abubuwan kenan duk waɗannan abubuwan ita bata da shi, ta ce

"Hajiya ki shiga ɗaki mana baki zauna ba kina tsaye" Baki ta taɓe ta ce

"Ai tuni aka bani wurin zama a inda aka san darajata, aka bani ruwa ana girmamani ai in sha Allah shekara ba za ta rufa ba sai Meenal ta tare a gidan Nasir!" Tana faɗar hakan bata jira komai ba ta juya ta fice daga gidan ta bar Sadiya tsaye tana maimaita sunan Meenal a zuciyarta ita dai Meenal ɗaya ta sani ƴar gidan ƙawar Hajiyar don ta taɓa zuwa gidan ma ita da su Husna lokacin tana amarya suka zo.

Juyawa ta yi ta nufi wajen tukunyar tuwonta, a ranta tana mamakin mutum nawa take aure, Nasir ya ci zarafinta Æ´an uwansa ga kuma mahaifiyarsa su basu ma san auren ya fice mata a rai ba don bata da yadda za ta yi ne.

*GIDAN BABA*

Wajen ƙarfe goma na safe Baba ya fito daga ɗaki yana gyara zaman babbar rigarsa ya janyo ƙofar ɗakinsa ya rufe ya kalli Mama Habiba da take wanki ya washe baki ya ce

"To mu fa Allah ya yi aure da marar kwabo za mu tafi na san yau dai É—ari biyar É—ina da nake sayan awarar rana ta huta" ÆŠagowa ta yi daga wankin da take tana masa kallon rashin fahimta ta ce

"Yau ɗumaman tuwon safen ne ya ƙosarka sosai da gar ba za ka buƙaci abincin rana ba?" Wata dariya ya yi irin ta ba za ki gane ba ne ya ce

"Ana ga yaƙi ke kina ga ƙura!. To Baban abokin abokina ne ya rasu kuma gidansu masu mugun kuɗi ne wato uban ya bar tarin dukiya kin san kuwa wajen zaman makokin za a ci jar miya, ni ban ma taɓa ganin wanda Baban nasa ya mutun ba kawai dai labari abokina ya bani cewa jiya sun yi ciye-viye da suka je gaisuwa shi ne na masa Allah annabi ya rakani in yi gaisuwa, kin ga gwara mu tafi tun da wuri da zafi -zafi ake bugun ƙarfe sannan da sanyin safiya ake kama fara" Duk abin da yake faɗa matan gidan da suke cikin ɗaki kowa yana jinsa kasancewar shi ba ya magana a hankali, fitowar Sumy daga ɗaki ne ya dakatar da Mama Habiba daga maganar da take son yi ta ce

"Baba don Allah ka bani kuÉ—i zan saya maganin guduwa kwana na yi ina yi" Kamar wanda ta watsa masa wuta a take ya fitittike yake masifa annurin fuskarsa ya dishe ya ce

"Ah uban gudawa kike ba gudawa ba Sumayya, ku babu dama ku ga mutum sai ku ringa jero masa buƙatunku, shin ina uwarki ma take ko ni kaɗai na haife ki? Wallahi shi ya sa kullum nake fatan Allah ya bani ɗa namiji ko kangararre ne duk tsiya ya taimaka mini amma a ce ƴaƴa mata kitika-kitika sun cika mini gida har baba gane su tsakaninsu da iyayensu mata to duk sun girma sun yi kwantai kowa sai dai ya kawo maka buƙatu ba zai taimaka maka ba...

Mama Habiba ta ce

"Haba dan Allah, yanzu ina amfanin wannan maganganun da kake" Baki sake yake kallon Mama Habiba kafin ya juyo bayansa cike da gatse ya ce

"To uwata Habiba ai sai ki min hukuncin duka" ÆŠan baya ta ja tana faÉ—in

"Ni ban ce zan dake ka ba amma dai wasu maganganun basu da amfanin faɗa ƴaƴa mata ai rahma ne" Wata harara ya jefa mata ita kuma ta ɗauki ƙaramar jakarta da take ajiye a gefe ta buɗe ta ɗakko naira ɗari ta ba Sumy ta ce ta je ta saya maganin.

Juyawa Sumy ta yi tana wani taɓe baki a ɓoye tana aikawa Baba harar ƙasan ido ta koma ɗakin. Malika ce ta fito daga ɗaki sanyi cikin doguwar rigar dakakken leshi mai tsada sai ƙaramin mayafi da ƴar jaka ta yi kyau abinta ganin Baba sai da gabanta ya faɗi don ita da ta jiyo muryarsa lokacin tana shiryawa tunaninta fita ma ya yi dab gidan. Gabanta yana faɗuwa amma sai ta ji ya ce

"Ke ina za ki je haka?" Ya faÉ—a yana kallon shigar jikinta duk da ya san mahaifiyarta bata da kuÉ—in da za ta saya mata kayan sannan iya ma yarinyar haka amma ba zai tuhume su inda suke samun komai ba shi dai É—awainiyarsu ce ba zai É—auka ba in ya suke samu ma wannan ba damuwarsa ba ce

Cike da É—an jin kunya ta ce

"Wani Alhaji ne yake jirana a waje" Wani irin washe baki ya yi ya ce

"Allah sa ya miki maganar aure" ÆŠan shiru ta yi sai kuma ta ce

"Eh ya ce aure lokaci ne amma dai da shirin aure ya zo"

Baba ya ce

"Haka nake so, akwai kati a wayarki? Ina so na yi waya bani da kati" Kai ta gyaɗa masa tana mai cire pswrd ɗin cikin hanzari ta yi saurin fita daga wtsapp ɗin don ta ga tana ma cikin acc ɗin Alhajin inda suka gama hirar banza da ture-turen hotunan banza, tana fitowa ta bashi wayar ya karɓa ya fito da tasho wayar ya kwafi lambobi ya danna kira ya kara a kunne, abokinsa ya kira yana faɗa masa ya shirya shi kuma ya faɗa masa inda za su haɗu su wuce gidan makokin. Wayar ya kashe zai miƙa mata sai ya ga hoton kan wayar hoton ta ne da wani mutumi Babban mutum suna cikin mota a zaune ta ɗora kanta a gefen kafaɗarsa suna dariya, jim kaɗan ya yi yana kallon hoton ita kuma gabanta yana dukan uku-uku sai dai kuma sai ya ga hakan ba komai ba ne tun da ba wani abu ya gani ba sannan ya tuna ta ce zai aure ta don yana tunanin shi ne Alhajin da ta ce yana jiranta a waje.

Yana bata wayar ta juya ta fita, Mama Habiba tana jifansa da kallon Allah wadaran naka ya lalace, a ce wai kai baka sayawa yaro sutura ba baka saya masa waya ba amma kana ganinsa da abubuwan da sun fi ƙarfin ya mallake su ba za ka tsawatar ba ko ka tuhume shi a kan abun.

Yana baza babbar riga ya juya yana nufar hanyar ƙofar gidan ba tare da ya yi wa sauran matan sallama ba ya ce

"To mu sai Allah ya dawo da mu" Mama Habiba ta ce
Chapter 23 · 0% Book details