← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 106

Sashe 12

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ya san ya sauyawa gidan mukulli amma bai bani ba to mene ne nufinsa? ' Ta faɗa a zuciyarta tana saka hannu ta riƙe kwaɗon tana tunanin yadda za a yi ta buɗe ta shiga gidan, tun da babu gidan wanda take shiga a umguwar bare yanzu gidan wa ma za ka je da tsakar ranar nan, to idan ka je ma ka ce mai?. Ɗan sakin kwaɗon ta yi ya bugu jikin ƙofar yana sakin wani ɗan ƙara, kanta ta jingina a jikin bangon ƙofar daga gefe tana jin ita daj bata dace sa miji ba a gefe ɗaya zuciyarta tana faɗa mata hatta mahaifin ma bata yi dace da shi ba.

Ta jima a haka tana jin irin yadda gumi yake sartu a jikinta saboda zafin ranar da ake gabaɗaya ranar a buɗe take. Motsin da Kalifa ya yi ne ya dawo da ita daga duniyar saƙa da warwarar da take yi a zuciyarta. Ɗagowa ta yi tana ƙarewa layin nasu kallo babu kowa sai mutane da suke ficewa jefi-jefi idanu ta mayar hanyar da ta biyu ko za ta hango mashin ɗin da Nasir suka wuce amma ko alamarsa, ta daɗe a tsaye ko za ta ga ya dawo amma shiru tamkar maye ya ci shirwa!.

Zafin rana ga goyo shi kansa Kalifa so yake ta sakko shi, ganin abin ba na ƙare ba ne, don a ƙalla ta yi kusan minti talatin a wajen a tsaye amma babu alamar Nasir zai kawo mukullin. A hankali ta sakko daga matakalar gaban gidan tana jan ƙafa ga yunwa ga baƙin ciki da takaicin ɗa namiji da yake ƙunsa mata, ga rashin adalcin da iyayenta suke mata, na rashin jin damuwarta da kuma magance mata ita.

Gidan da yake kallon gidan ta, nan ta hangi inuwa da ɗan dakali a wajen, haka ta cira ƙafafu tamkar iska za ta ɗauke ta, suna zuwa inuwar ta zauna har lokacin bata sauke Kalifa daga bayanta ba. Bayan ta zauna sai ta kifa kanta a gwiwarta tana jin babu daɗi ganin duk wanda zai wuce sai ya kalle ta, har ta fara zargin ko daj sun zata mahaukaciya ce. Maganar Kalifa ta katse mata tunani jin ya ce

"Mom a sakko ni" Ya faÉ—a cikin maganrsa ta gwaranci da bata fiye fitowa raÉ—au ba, hannu ta kai ta sakko shi, sai lokacin ta lura da hannunsa da ba a wanke masa ba lokacin da ya ci tuwo. Tana sakko shi ya fara É—aga hannu yana nuna hanyar da suka baro yana faÉ—in

",Abba" Wani iri ta ji a zuciyarta don wannan maganar da ya yi hakan yana nuni da cewa ya ga mahaifinsa lokacin da suka wuce, baki ta buÉ—e cikin sanyin murya ta ce

"Abbanka yana zuwa ya ke siyo maka alewa ne, kana son shan alewa?" Kai kawai ya gyara mata.

Zuwa can tana zaune Kalifa a cinyarta jakarta ƙarama a gefenta a ajiye, ganin yara suna wucewa da uniform a jikinsu ta tabbatar yanzu ƙarfe uku ta yi.

Wani yaro ɗan maƙotanta daga can gefe ya fito sanye da unifort riga pink me ɗigo-ɗigo yayin da wandon yake purple, tun da ya hange ta yake dariya har ya ƙaraso ya ce

",Auty Sadiya" Ya faÉ—a yana cike da fara'a amsa masa ta yi ya shiga gaishe ta sai kuma ya ce

"Aunty ya kike zaune a waje?" Ya tambaya yana kallon ta da yake da É—an wayonsa don zai yi shekara tara zuwa goma, rasa ma mai za ta ce masa ta yi duk ta É—an diririce sai kuma can dabara ta faÉ—o mata sai ta ce

"Tare da Abban Kalifa muke to mukullin ne ya faɗi shi ne ya koma ya dubo?" Ta samu kanta da sharara masa ƙarya. Dariya ya yi bai ce komai ba don shi ko kaɗan ba ya son wannan mutumin bashi da kyawun hali ya yi ta korarsu idan suka je gidansa. Wasa ya yi wa Kalifa ya fito da alewa a jakar makarantarsa ya bashi yana ɗaga masa hannu yana masa bye-bye shi ma Kalifan bye-bye ya masa.

Alewar ya miƙa mata ta karɓa ta ɓare masa ya fara sha, shiru babu amo ba labarin Nasir har aka fara kiran la'asar abin ya ɗaure mata kai don ta san ko ma ina zai je ya ci a ce ya dawo tun da dai ta san ba kasuwa ya tafi ba tun da gashi nan da kasuwa zai je da wuri zai fita. Abin ya fara bata tsoro tana zaune babu sallar azahar babu ta la'asar gashi tana tsoron shiga gidajen maƙota cibi ya zama ƙari don matsawar ta shiga ya zo ya ganta tabbas akwai gagarumar matsala. Kalifa sauka ya yi daga cinyarta saboda ya gaji da zaman waje ɗaya, ya shiga kewaya wajen, yana ɗan wasa.

Ta buga uban tagumi ta yi nisa cikin tunanin lamuran gidan aurenta, tana tuna irin wulaƙanci da tozarcin da Nasir yake mata, ƙaran wani birki da mai mashin ya ja shi ne ya dawo da ita hayyacinsa, a kiɗime ta tashi ta je gaban mashin ɗin da ta hangi Kalifa kwance a wajen, mai mashin ɗin wanda yake ɗauke da ƴan makarantar islamiya da ya ɗakko, kanta a take ya shiga juyawa ta yi kan Kalifan da gudu ƙirjinta yana bugu tamkar zuciyarta za ta fasa ƙirjin ta fito tana faɗin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

*JIDDA*

Idanunta cike da hawaye ya cigaba da magana don don duk abin da take faɗa iya gaskiyarta take faɗa komai daga ƙasan zuciyarta yake ta ci gaba da faɗin

"Ni ba damuwata rashin mijin ba damuwata É—aya yadda Umma za ta takura min idan aka yi auren Aliya ba a haÉ—a da nawa ba, kuma kin ga Abba ba zaman gidan yake ba, sai na gwammace kiÉ—a da karatu in ma bata kore ni ba, don ba gori ba har goriba sai ta min a kan rashin auren"

Shiru Salama ta yi tana nazari da tunanin maganganun ƙawar tata a lokaci guda tausayin Jidda yana mamaye mata zuciya da ruhi.

Ibrahim wanda ya cika da zufa tun furucin Jidda na farko wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwa, kuma shi har ga Allah a yadda yake jin Jidda ta gama bin jijiyoyin da jinin jikinsa ba zai iya rayuwa ba sai dai ita sai dai furucin ta ya nuna masa da sauran rina a kaba, domin kuwa da wuya wai gurguwa da auren ne, shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa tana tuno masa haɗe da dawo masa da tunanin abin da ta furta wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwar da yake ganin dab yake da ya rasa Jidda wanda hakan kuma babban ƙalubale ne a rayuwarsa.

'Salama damuwar yawancin ƴanmtan yanzu shi ne auren namiji mai kuɗi kuma kyakyawa, yawancin kowacce burinta ne wannan, ni kuma inda muka sha bamban da saura kenan tunanina burina haɗe da ƙudurina basa kan namiji kyakkyawa kuma ba wai don hakan ya haɗa nasaba da munin da nake da shi ba, uwa uba dukiya basa gabana don ni a ra'ayina in auri talaka kuma mummuna in da zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta yadda kyawunsa ba zai ruɗi ruɗaɗɗun ƴanmata ba, sannan dukiyarsa ma ba za ta tsone musu idanu ba, kin ga burin Aliya ne wannan ni kuma bani da ra,ayi a kan hakan, amma zan ci gaba da addu'a Allah ya bani miji na gari daidai ni' Wannan su ne furucin da ya hargitsa tunanin Ibrahim da sauri ya saita madubin motarsa ƙan ƙarami na ciki wanda yake maƙale fuskarsa ya kalla a ciki, ganin irin kyawun da Allah ya yi masa sai da ya ƙara jin gabansa ya faɗi tamkar dai a yau ne ya taɓa ganin kyawun fuskarsa.

Zuwa yanzu duk ba ya fahimtar maganganun da suke tattunawa, hankalinsa ya yi bala'in tashi yana ta tunanin ya zai yi ya mallaki Jidda, tun da gashi ba ya ma cikin mazan da take da burin aurr, na farko dai shi yana da kuɗi sannan uwa uba Allah ya hore masa kyau shi kyakkyawa ne ajin ƙarshe, zai iya tabbatarwa ya cika dukkan abin da ta lissafa zai samar mata na kwanciyar hankali a gidan aure sai dai kash! Bai sani ba ko za ta karɓe shi a matsayin kyakkyawa kuma mai kuɗi don ya tabbata shi dai sai dai a saka shi cikin masu kuɗi pan ajin farko ba ma ajin ƙarshe ba.

A fili ya furta

"Ya zan yi?" Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsar ta bare kuma mafita. Yana cikin wannan tunanin kamar an ce ya ɗago sai ya ga wayam babu kowa a jikin motar, dama ya ji ba ya jin maganarsu kasancewar a ruɗe yake bai yi tunanin dajna jin muryarsu da ya yi ba. Idanu ya hanga sai kuwa ya ga Jiddan za ta shige gida ta juyo tana yin bye-bye kasancewar ita yake kallo sai ya ga tamkar shi take ɗagowa hannun bai san lokacin da ya ɗaga nasa hannun ba yana mata bye-bye tamkar wani soko. Ganin ta shige gidan ya dawo hayyacinsa sai a lokacin ya yi tunanin ashe ma bata ganinsa kasancewar baƙin gilashin motar, sannan ma shi da ba saninsa ta yi ba shi kaɗai ne ya san ta ya san matsayinta a zuciyarsa. Can da ya hanga sai ya ga ashe Salama ƙawarta ta ɗagawa hannun, huci ya busar mai zafi daga bakinsa ya ɗan kwantar da kujerar tare da mayar da bayansa ya kwanta ya rufe idanunsa kawai ita yake hangowa lokacin da take yi wa ƙawarta bayani, yadda take bayani cike da damuwa shi ne abin da ya fi tsaya masa a rai.

Idanun ya runtse da ƙarfi a fili ya furta
Chapter 12 · 0% Book details