Sashe 57
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allahu akbar!. Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai halitta yadda ya so, ka yi haƙuri wallahi ni ban san ma haka abun yake ba ka san yaran zamani duk tunanina har yanzu akwai larurar da na san haka ne ai babu dalilin da zai sa na kira ka a waya" Aliya wacce kanta yake sunkuye bata san lokacin da ta ji wasu zafafan hawayen baƙinciki suna kwaranya mata ba saboda ta ɗauka Abba zai fitittike ya ce sai an sakar masa ƴa amma sai take jin saɓanin hakan. Wannan barazana ne ga cikar burinta na auren Ibrahim kuma dai hakan ba zai sare mata gwiwa ba ko ta halin ƙaƙa sai ta aure shi sai ta tarwatsa zaman Jidda a cilkin gidansa ta maye masa gurbinta!.
Ana cikin wannan tattaunawar da ake ne Kasim wanda gabansa yake zuwa da dawowanya ƙaraso gabaɗaya a firgice yake dakyar ma yake ganin gabansa lokacin da ya shiga zaure da sallama bayan an ce ya shiga, saura kaɗan ya faɗa kan Aliya da take gefe saboda kiɗima da faɗuwar gaba, haka ya daure ya zauna tare da gaishe da su Abban.
Jin Abba ya amsa masa fuska sake ya fara tunnain wataƙila Abban ya fahimci shi kuma ya masa adalci!. Abba ya buɗe baki ya ce
"Aliya yanzu dama maijinki ba ya ɗauke da larurar an magance amma kika ɗakko ƙafa kika taho gida?" Gabanta ne ya faɗi don tabbas tana taoron Abba amma dai a yau saboda cikar buri da son zuciyarta ya zama dole ta wanke idanunta ta ƙwatarwa kanta ƴanci tun da dai ai ta san ba a sauyawa tuwo suna, ma'ana tun da har aka kira Kasim da mata maza to wannan suna ne da zai zama linzami har mutuwarsa don haka ba za ta so a ci gaban da ambaton ta a matsayin matar mata maza ba!.
Baki ta buÉ—e ta ce
"Abba ni abi ban sani ba kawai na É—auka akwai larurar har yanzu" Kasim jin ta yi magana cikin lafazi mai taushi sai da ya sauke ajiyar zuciyar da har sai da gabaÉ—aya mutanen zauren suka ji.
Abba ya ce
"To na miki uzuri don haka yanzu tun da kin ji bayanin da aka yi ki tashi ki bi mijinki tun kafin idanun mutanen unguwa ya kai ga abin da yake faruwa" Tuno da maganar Amatallahi ƙawarta ya sa ta ce
"Abba ni na haƙura da zama da shi" Ta faɗa ko gizau bata yi ba don ta gwammace ran Abban ya ɓaci a kan ta haƙura. Abba tsabar mamakin furucinta bakinsa ya ƙi rufuwa ba furucin ne kaɗai abin mamakin ba wato na komawa gidan illa yadda ta iya furta maganar a gabansa da gaban sirikinta a gefe ɗaya bga mijinta shi dai ya san ƴaƴansa ya basu tarbiya da sanin girman na gaba sannan uwa uba kunya sai dai furucin Aliya yasa ya fara tunanin lallai ta yi watsi da tarbuyar gidansa!.
Cike da mamaki ya kalleta ya ce
"Aliya ɗago fuskarki" Dakyar ta ɗago a nan ya ga abin mamaki fuska shaɓe shaɓe da hawaye, ya kalli idanunta ya ce
"Ni kike faɗawa wannan maganar?"Da sauri ta kawar da idonta daga kallonsa. Kasim kuwa furucinta kaɗan ya rage ya rafka ihu hatta mahaifinsa maganar ta girgiza shi yana ganin ya aurawa ɗansa ƴa ƴar gidan mutunci amma kuma abu yana neman kwaɓewa.
Kai ta girgiza ya ce
"Baki ji bayanin da aka miki ba kenan yanzu idan ƙaddara ta faɗawa abokin zamanki ba za ki rungumi ƙaddara ki zauna da shi ba? Shin baki san aure sadaukarwa da juna ba ne, kuma shi ɗan adam ba a gama masa galitta har sai ya bar duniya mutane nawa ne suke da idanunsu amma yau an wayi gari idanun sun salwanta ta silar afkuwar wata ƙaddara? Mutane nawa sike da ƙafafu amma sanadin wata ƙaddara an yanke musu wano ƙafa ɗaya wani kuma duka biyu. Mutane nawa suke da hannu amma yanzu wani babu hannun wani haƙuransa ya rasa sanadin haɗari ko wata ƙaddarar, wani asalinsa yana da kuɗi ƙaddarar karayar arziƙi ta faɗa masa, wani kuma shanyewar ɓarin jiki wani kuwa nan da nan ba zai iya takawa ba sai an tashe shi zaune sai an kwantar duk wannan ba ƙadsara ba ce? Kuma sai ƙaddarar da halitta ce aka haife shi da ita sannan an magance amma ke za ki ce wai kin fasa zama da shi wannan adalci ne kuwa, shin ina soyayya da ƙauna ina sadaukarwa irin sadaukarwar da take ahiga tsakanin ma,aurata ko masoya irin wacce ake kira da duk wuya duk runtsi ana tare?" Sosai ta saddar da kanta amma a zuciyarta babu alamar rusuna ko da na sani bare sauya ra,ayi a nata ganin duk matar ko mijin da ya ɗauki ƙaddarar da ta afkawa abokin zamansa shi ya ga zai iya amma ita kam sam babu wannan sadaukarwar.
Hatta mahaifin Kasim kai yake jijjigawa irinn yabawa da bayanin Abba. Kasim kuwa ji yake ai babu ma yadda za a yi ta ji wannan bayanin ta kasa cire ƙudurinta shi gani yake ma har wancan haushin nasa da take ji kafin ta ga yanayin halittarsa duk za ta zubar da makaman yaƙi, domin wannan bayanin na Abba ya haɗo komai idan ya ce komai yana nufin komai.
Amma buÉ—ar bakinta sao ta ce
"Abba ni kawai na haƙura da zama da sh... Tun kan ta kai aya Abba ya wanke fuskarta hagu da dama mahaifin Kasim yana hana shi amma ran Abba ya ɓaci dama mai haƙuri bai iya fushi ba sannan Abba tsayayyan mutum ne a kan iyalansa. Rai ɓace yake nuna ta da yatsa tana riƙe da kumatun ta shi kuma Kasim tamkar shi aka mara haka ya ji
Abba ya ce
"Na fi ƙarfin ɗiyar da na haifa ta watsa min ƙasa a ido, ba a yi ki ba Aliya wallahi idan shawara aka baki ma ko son zuciya ki sani na fi ƙarfin ƴata ta juya ni, bani da buri ko ƙudurin yi wa ƴaƴana auren dole hakan ya sa na baku dama kuka fitar da zaɓinku don haka wallahi kin yi ƙarya!." Ya faɗa lokacin da ya tashi tsaye yana ta kumfar baki hatta ƴan cikin gida suna iya jiyowa Umma kuwa tana zaune ta rafka tagumi hannu bibiyu, a ranta tana raya ta so a ce Aliya ce a gidan miji hankali kwance Jidda ce ta dawo gida ake wannan ɗauki ba daɗin sai dai abin ba haka ba ne.
Mahaifin Kasim yana ta bashi baki haka Abban ya nuna masa ya haƙura sai dai Kasim yana tsaye ya rasa abin yi don bai ga Aliya ta ji wannan maganar da aka mata ba, haka ya sa Abba cike da ƙaraji ya ce.
"Yanzu ba sai an jima ba ki tashi ki bi mijinki idan ba haka ba ki fitar mini a gida, sannan ki sauya wani uban na yafe ki a matsayin ƴata!" Gudun kukanta ne ya ƙaru Abba ya ba mahaifin Kasim hannu suka yj masabiha ya tare mashin ya hau ya tafi, shi ma Abba mashin ya hau don komawa kasuwa.
Kasim napep ya samo ya fi minti ashirin yana jiranta tana cikin gidan zuwa can sai gata wata mata ta rako ta, tana riƙe da hannun Aliyar da take rafkar kuka tana ta bata baki haka ta shiga shi ma ya shiga mai napep ya ja domin sadar da su ga gidan nasu.
Ji take kamar ta shiga bugun Kasim har sai ya daina numfashi, ranta ƙuna yake musamman da ta gansu a napep ita da shi don hassadar tata ce ta motsa a kan Jidda tana rayawa a ranta da a ce Jidda ce da Ibrahim mota sai wacce suka zaɓa za su hau amma ita gashi a napep za su tafi gidan da babu get ko keke babu bare a yi maganar mota a zuciyarta ta ce
'Allah tsinewa tsiya da kuma matsiyaci,!".
Tun da ta koma gidan sai ta ji ta ƙara tsanarsa sannan tun daga wannan ranar bata ƙara yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba, ita Amatullahi bata taɓa bata shawarar kirki kullum cikin zugata tana nuna mata ita ce ta dace da zama matar Ibrahim ba Jidda ba.
Bayan sati guda ta yi dogon tunani da nazari don cim ma burinta sai dai wani hanzari ba gudu ba ta gane cewar wannan ƙudurin ba zai cika ba har sai ta shirya tsakaninta da Kasim, wannan ne zai bata damar ta shirya da Abba sannan kuma hakan zai kaita ga cim ma nasara a kan burikan ta
Ta sauya takunta don yanzu ta sakko tana nunawa Kasim kulawa sannan bata nuna masa komai hakan ya sa ransa ya yi fari ba tare da ya zargi komai ba ya danganta hakan da addu,ar da yake yi ce ta karɓu. Bata hana shi kanta sannan komai yake so tana masa bayan kwana biyu sai ta bijiro masa da buƙatar kuɗi dubu goma amma sai ya ce bashi da shi, hakan ya sa ta nema a wajen Jidda sannan bata nuna masa ta damu da bai bata kuɗin ba.
Jidda ta tura mata kuÉ—i naira dubu hamsin tun da ita yanzu bata da matsalarsu haka kawai ma idan ta yi kwalliya ta birge Ibrahim sai dai ta ji ya ce ta kawo acc no.
Amatullahi ta turawa kuɗin ta siyo mata waya ta dubu talatin da sim sabo ta kawo mata a ɓoye ta samu waje ta ɓoye don sim ɗin mai register ne. Sai da Kasim ya fita ta saka sim a waya bayan ta mata caji ta tura whatsapp ta buɗe da sabuwar lambar, sai kuma ta saka no Ibrahim wacce ta sata a wayar Jidda tun suna gida no da ta yi haddar karatun fatiha don ko daga bacci aka tashe ta za ta iya faɗar lambar wayar Ibrahim.