← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 106

Sashe 73

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gangan ta ɗauki ruwa ta je ta zuba a matakalar don ta san tun da har Jidda bata san ta hau saman ba bayan a can turakar mai gidan take to ta san tabbas akwai wata maƙarƙashiya. Shi ya sa ta zuba tuwan domin ta san tun da Jidda ta hau samn to Aliya za ta yi ƙoƙarib kuɓuta, bayan ta zuba ne kuma ta ga Ibrahim ya dawo ga hau saman tana ta addu,ar Allah ya sa kar ya ga ruwan ko kuma ya taka, duk da ma akwai takalmi a ƙafarsa ba lallai santsin ya kwashe shi ba, bayan ya fito ne kuma sai ta ga ma yanayin yadda Aliya ta taho kaɗai ya isa ta gangaro idan ta samu kufcewar take matakala sai kuma Allah ya sa ta taka ruwan ta faɗo. Ta so a ce Jidda ta ganta sai dai kash an samu akasin lissafi.
Amsar da Aliya ta ba Jidda ya ƙara saka Saude a tarkon mamaki domin cewa ta yi

"Dama na san idan baki ganni ba sai kin tambaye ni cikina ne ya hautsina min, ganin kina banÉ—akin wancan É—akin shi ne na je na shiga na wancan É—akin" Ta faÉ—a tana Æ´ar dariya Jidda ma dariyar ta yi ta matsa kusa da Aliyar ta ce

"Ki ce rage ciki kika tafi, Allah sarki har na tuna rayuwarmu ta yarinta idan na je gidan Umma daga na ce ina jin kashi sai ke ma ki ce kina ji, in riga ki shigewa banɗaki kike ta cewa in yi sauri karki yi a wando" ,Ta faɗa tana dariya sosai, Aliya ma daeiyar take duk da hannun Jidda da ya taɓa kafaɗarta ji take tamkar an ɗora mata garwashi saboda tsantsar tsanar Jiddar da take ji amma babu halin nunawa.

Aliya ta ce

"Umma sai ta ce ku dama kamar ƴan biyu ɗaya ba zai yi abu ba sai ɗayan ma ya ce zai yi Allah na tuba kashi dai ba a matse shi ba sai a ce ana ji idan ɗaya ya ce zai yi wa ya sani ma ko da kanku kuke ƙwaƙulowa" Aliya ta maimaita maganar cikin kwaikwayar muryar Umma suke dariya.

Kan kujera suka ƙarasa har lokacin hannun Jidda rataye a wuyan Aliya kamar yadda suke dafa kuna lokacin da suke yaran, Jidda tana jin wani daɗi da farincikin ganin sauyawar rayuwarta a ƙanƙanin lokacj, wato a da ta rasa duk kulawa da soyayyar ƴan uwantaka da ta ƙawance tsakaninta da Aliyarta uwa uba tsantsar tsana daga Umma amma yanzu gashi komai ya shiga littafin tarihi.

Suna zama Jidda ta É—auke hannunta tana cewa

"Ni wai har alwala kika yi ne " Ta faɗa ta sigar wasa dariya Aliya ta yi don dama da gayya ta wanke ƙafa da fuska don ta cirewa Jidda shakku a kan cewa daga banɗaki take sai da ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce
"Kawai dai fuska tw ce na wanke"
Saude an barta da tsantsar mamaki tana tunanin makirce da ƙarya irin na Aliya hakan yansa ta ɗarsa zargin akwai wani abu da ya kai Aliya saman wanda kuma bata jin alkaiti ne don ta san dai ai Aliya bata ce zuwa ta yi kawai don ta ga saman ba idan har ganin saman take son yi ai ba sai a ɓoye ba sai dai za ta yi amfani da hankali da basira don ta gane inda Akiya ta dosa sannan ta yi alƙawarin duk wani abu da Aliya za ta yi ga uwar ɗakinta Jidda to ba za ta bari ba matuƙar tana numfashi sai dai abu wanda yake dama Allah ya rubuta a littafin Jidda wanda yake ƙaddara ne ita kuma ƙaddara duk runtsi babi mai guje mata.

Ƙaran wayar Aliya ne ya katse tana ɗago wayar ta ga sunan Kasim dimm ta ji faɗuwar gaba don bata san dalilin kiran ba, sai kuma ta maje don kar Jidda ta fahimci wani abu tun da dai ta faɗa mata baya gari duk da shi bata faɗa masa za ta fitan ba sai kuma wani tunani ya faɗo mata tana jin Allah ya sa tana ɗaga wayar ta ji muryar wani daban wato a ce mata mai wayar sun yi haɗari ya mutu, shikenan ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da ƙuda.

Tana É—agawa ta kara a kunne tare da yin shiru tana jiran jin labarin mutuwar Kasim

Sai ta ji muryar wani yana cewa

"Ai abin babu kyan gani gabaÉ—aya babu wanda ya tsira a motar duk sun mutu"

Aliya bata san lokacin da ta ce

"Alhamdulillahi ba" Don tsabar son ta ji sanarwar mutuwar Kasim bata gane cewa wani ne a gefe yake maganar ba, ba wai a wayar da aka kira ta ake maganar ba, Jidda kuma idanu ta zuba mata jin ta jero hamdala.
amma sai ta ji muryarsa rangaÉ—aÉ—au yana faÉ—in

"Hlo Aliya tawa mai aka samu ne na alkairi ake hamdala haka" ,Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare ta har sai da Jidda ta ga ɓacin rai ya bayyana a fuskarta sai kuma ta ƙirƙiri murmushi ta ce

"Kawai dai jin muryarka kana lafiya shi ya sa na yi hamdala, tun É—azu nake son kiranka in ji ya hanya sai nake sha,afa"

Kasim ya ce

"Hanya Alhamdulillahi ai gamu nan mun kusa zuwa ma ashe ma garin ba wani nisa ne da shi sosai ba kuma mun samu lafiyayar mota don ana É—aurawa ma muka juyo ki dafa min jallof na taliya mai ruwa ruwa"

Aliya ta amsa da to ba don ranta ya so ba kuma gashi a kan kunnen Jidda ya ce ta masa girki, gashi tana son cikar burinta wato ganin Ibrahim ya ci abinci da cokalin da bokanya ta gama asircewa.
Tana sauke wayar ta ce
"Kin ji wai ya taho ma yana faÉ—in in masa girki gashi la,asar lis ma ta yi" Jidda ta ce
"Ya fasa kwanan kenan" Aliya ta ce

"Eh ya fasa kawai ina hira da Æ´ar uwata zai katse min " Ta faÉ—a cikin kissa Jidda tw ce.

"Ai ni ma zan kawo miki wuni" Aliya a fili ta ce

"Amma ranar da na ji daÉ—i"

Ji

A zuciyarta ta ce

'Yarinya daga yau za ki yi bankwana da kwanciyar hankali da nutsuwar da har za ki yi tunanin kai wa wani ziyara"

Jidda ta ce

"In sha Allah"

Ɗan ƙaran ƙofar kicin ne da Saude ta buɗe ta fito don dama a karawa ta yi take tsegumin da take yi shi ya ankarar da su da akwai mutum Jidda ta juya ta ce

"Saude dama kina kicin?" Saude ta.ce

"Eh ina ciki ina ware kayan saman kanta da suka yi ƙura ina gogewa ina jera su" Gaban Aliya ne ya faɗi ta fara tunanin shin tun yaushe Sauden take kicin? Ba dai tana kicin ta faɗo daga saman bene be? Ko dai lokacin da ta shige ɗaki ta shiga bamɗaki tana wanke fuska ta zo ta shiga, gaban Aliya ne ya faɗi don ta ji yanayin yadda aka buɗe ƙofar kicin ɗin bai yi kama da cewa ƙofar a rufe take ba ya fi alama da dama ƙofar ba a rufe take duka ba.

Kallon tuhuma ta fara jifan Saude da shi bayan ta fakaici idanun Jidda, ita dama ta tsani Sauden nan don ta lura ruwan munafukai ne da it, ita kuma Saude sai ta ɗauke idanunta ta fara takawa za ta bar falon don ko alama bata ma nuna ta san Aliya tana aika mata saƙon harara ba.
Ta kama hanyar fita sai ta ji Jidda ta ce

"Saude zo ki bamu kunun gyaɗa" Da to ta amsa ta juya ta shiga kicin ɗin, ita kuma Jidda sai ta ce tana zuwa ta tashi ta shiga ɗaki jin wayarta tana ƙara, tana shiga ta ga Salama ce suka ɓige da hira.

A falo Aliya ta tashi sai ta sunkuya za ta ɗauki jakarta, a daidai nan Saude da take ɗauke da kofuna biyu da cokali a cikin kowanne ta zo za ta ajiye kawai sai idanunta ya sauke a ƙirjin Aliya nan ta hangi cokali kane-kane a cikin bireziyar Aliya, idanu ta zaro gabanta yana faɗuwa da sauri ta kawar da idanunta ta ajiye kufunan ta juya za ta bar wajen daidai nan Aliya da ta ɗauki jakar tata ta ɗago cikin kaushin murya ta ce

"Keee!" Amma Saude ko gizau bata yi ba bare ta juyo ma ko nunawa bata yi akwai wata halitta a wajenta ba ta yi tafiyar ta tana dab da shiga kicin Aliya ta sake cewa

"Ke Saude aba da ke nake magana ba" Juyowa ta yi cike da nuna rainin hankali ta ce

"Au wai dama da ni kike? Ai na ji kin ce kee ni kuma da aka yanka rago Saude aka raɗa mini" Ran Aliya ne ya ɓaci hakan yansa ta yi jifa da jakar a kan kujera ta nufi Saude a fusace tana zuwa ta damƙi rigar Saude daga kafaɗa ta ce

"Ke ni kike faɗawa hakan?" Saude ta yi shiru batance komai ba don dama fitsararriya ce ta ajin ƙrshe don ta ga aiki take shi ya sa bata zaƙewa. Aliya ta kalle ta cike da tuhuma ta ce

"Tun yaushe kike cikin kicin" A fili ta ce

"Lokacin da Aunty Jidda ta dafa kafaÉ—arki kuna tsaye a can lokacin ne na zo na shiga" Ta faÉ—a tana nunawa Aliya inda suka tsaya É—azu sai Aliya ta ji daÉ—i don hakan ya nuna bata ganta ba a zuciyarta ta ce

'Tun lokacin da kika haye sama'

A daidai nan Jidda ta fito daga ɗaki sai Aliya ta ƙirƙiri dariya tare da sakin riƙon da ta yi wa Saude ta ɗan buga kafaɗar Sauden da wasa tana cewa

"Kina birgeni Saude" Saude ganin barikin da Aliya ta yi sai ita ma ta yj dariya tana cewa

"Na kuwa gode Aunty Aliya bari na kawo muku sugar" Juyowa ta yi ta dawo falon Jidsa tana riƙe da wayarta tana dariya don ita sai ta ga sun birgeta tana ta mamakin sakkowar Aliya yanzu ta zama mai sauƙin kai sai take ganin hakan ne ya dace domin dama duniyar kanta nawa take da mutum zai ke ɗagawa da girman kai.
Chapter 73 · 0% Book details