Sashe 87
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yanzu ai na ce zan ke biya amma kuma bai san an mayar mini ba, ana zuwa neman kayan sanyin ina cewa babu kada kasuwar ta mutu shi ya sa dama na ce bari na zo na faÉ—a miki ko za ki masa magana"
Hajiya ta ce
"Sai ki ɗauki na annabawa ki jira lokacin da idan ya gama busar iska zai sa a gyara miki, abin da sana,ar da kike ta fi goma ko kin ɗauka ba sani ba ne, tun da laila ta ƙiya sai a koma caca, ai a yadda kike caskar kuɗina wannan gidan da ke matan da suke son miji ne da ko aikin hajji ne ma kin biyawa Nasir tun da ta dalilin zaman gidansa da albarkarsa kike samun kuɗi" Shiru Sadiya ta yi ta ma rasa mai za ta ce sai kuma ta daure ta ce
"Yanzu gawayina ya ƙare kuma na faɗa masa ya ce ba shi da kuɗi ita kuma ta ce babu gas ya ce zai saya mata..
Hajiya ta katse mata hanzarin wajen faÉ—in
"Ya isa Sadiya na gaji da jin ƙorafinki ai dama tun da na ga kin ɗakko ƙafafu da ciki tirtsi tirtsi ke ga kaza sarkin haihuwa san sai dai ƙorafe ƙorafen ne zai kawo ki Allah na tuba gawayin me duk neman kuɗin da kike ma ai ke ya dace kike ciyar da kanki, kuma da kike maganar gas ni baki ga da abin da nake amfani ba tun da gas ɗin ya ƙare sai kawai mai baro na gani da itace Nasir ya aiko, tun da ya haɗu da mace mai jan akala da ragamar rayuwarsa sai dai mu zuba ido"
Sadiya ta ce
"Amma ni ma ai haƙƙina ne ya saya mini, kuma duk arziƙin da mace take da shi Allah bai ɗora mata ɗawainiya da kanta ba, ko da ta fi mijin nata kuɗi haƙƙinta na komai yana wuyansa sai dai idan ita ce ta ga dama bisa kyautatawa!"
Hajiya ta ce
"Yi min wa,azi Sadiya kin san ai ni kidahuma ce babu abin da na sani"
Sadiya ta ce
"Ba haka ba ne Hajiya, wallahi jiya da na fita gidan Kaka na dawo na rasa jakata da nake saka kuÉ—aÉ—e a ciki, sannan jarkar manja na tarar da kananzir a ciki...
Tun bata kai aya ba Hajiya ta ce
"Bakya fitar da zakka ne, ai dama wanda ba sa fitarwa da dukiya zakka su asara take faÉ—awa" Kallon Hajiya kawai take sai kuma ta ce
"Ai sana,ar tawa bata kai munzalin da zan fitar mata da zakka ba, ina sadaka dai"
Hajiya ta ce
"Ke kika sani da yake matsaloli ne suka baibaye ki shi ne kika zo kina zana mini kamar mai biya mini karatun hadda, to sai ki ɗauki ƙafarki ki koma inda kika fito, ko a tunaninki zan zaɓe ki ne in ajiye ƴata Meenal a kan maganar siyan gawayi da gas ai wata kusar ta fi wata kinnga tafiyata" Hajiya tana kaiwa nan ta tashi ta shiga kicin ta ɗakko robar da za ta kwashe tuwo ta yi ajen murhu, Kalifa sai kallonta yake abin takaicin ko uffan bata ce masa ba wai yana jikanta ɗaya tal duk duniya.
Haka ta baro gidan ranta yana ƙuna, tana tafiya tana ta addu,a da karanta sunayen Allah a kan ya kawo mata mafita, ƙaran wayarta ne ya katse mata tunani ta ɗaga ganin sunan ƙawarta Noor tana ɗagawa ta ce
"Albishirin ki"
Sadiya ta ce
"Goro fari ƙal"
Noor ta ce
"Sunanmu ya fito a wannan tallafin da muka cike an ce gobe za a je a karɓi 75k "
Sadiya kawai sai ta ce
"Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai da ta faÉ—a sau uku Noor ta ce
"Wannan hamdalar fa?" Ta faÉ—a tana dariyar tsokana
Sadiya ta ce
"Wallahi kawai wata hikima ce ta ubangiji Allah maji roƙo ne, duk wanda ya dogara da shi zai kawo masa mafita, na san wannan sakamakon addu,a ta ne da na yi da yaƙi ni" Noor duk da bata san komai ba sai ta ƙara mata ƙarfin gwiwan na ta ce idan sun haɗu goben za su yi maganar.
Ko da Nasir ya dawo ta faɗa masa cewa ya saka a mayar mata da nepa za ta biya kuɗin sai ya nuna mata ba yanzu ba, ai kuwa ta ƙyale shi. Washe gari suka je suka karɓo kuɗin duk da sun samu layi, dama NIN no da BVN ne ake buƙata da aka cike aka muau hoto sai aka basu ATM mai ɗauke da kuɗin suka cire suka taho gida Sadiya ranta fari ƙal.
Lokacin da ta dawo sai ta ga ƴan nepa su biyu a ƙofar gidan wani maƙocinsu daga can gaba suna mayar masa da wutar da suka yanke, ai kuwa ta musu magana ta biya suka mayar mata da tata wutar ɓangaren nata.
Meenal ta fito daga ɗakinta sai kawai ta ga hasken ƙwan ƙofar ɗakin Sadiya ya kawo hakan ya tabbatar mata da cewa an mayarwa da Sadiya nepa ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, ta ƙufula tana jiran ya dawo don a tunaninta shi ya sa aka mayer da wutar.
Lokacin da ya dawo Sadiya ta fara jiyo hayaniya sosai ana ta tafka faÉ—a, sai dai bata san abn da suke faÉ—a ba, tana zaune tana cin farar da ta siyo sai gashi kamar an jefo shi yana shigowa ya ce
,"Wane shegen ne ya mayar miki da nepa?" ,Ya tambaya ransa a matuƙar ɓace kamar zai hau ta da duka.
Ko gizau bata yi ba ta dake ta ce
"Ni ce nan na saka aka mayar mini, saboda na ga baka da niyyar sakawa a maida, ni kuma ina da buƙatar ta, tun da dai ba ni da galihu a matsayjna na matarka da zan aamu wutar nepa a ɓangarena duk da na ce zan biya shi ya sa da na gansu a unguwar suna mayarwa da wasu na ce su zo su mayar mini na biya su kuɗinsu" Kallonta kawai yake yana kissima yaushe Sadiya ta zama haka har take mayar masa martani ko ɗarɗar babu.
Meenal da take laɓe a ƙofar ɗakin Sadiya don son jin ƙwaƙwaf domun ita bata yarda da maganarsa ba da ya ce ba shi ya sa aka mayar ba sa ga shi kunnuwanta sun jiye mata.
Da yatsa ya nuna ta ya ce
"Har ni zan saka doka a gidan ke ki ƙetara?"
Tsaye ta miƙe ta ce
"Ka sa an yanke min wuta na ce a mayar ka wofantar da maganar bayan ka san sana,a nake, na faɗa maka na rasa jakar kuɗina amma ko a jikinka, bayan fitarka daga gidan na samu jarkar manja na ɗauke da kananzir saboda na san ma ba ɗaukan maganar za kamyi da muhimmanci ba ko faɗa maka ban yi ba, na ce maka gawayi ya ƙare ka ce baka da kuɗi, na je na faɗawa mahaifiyarka amma bata goyi bayana ba, ka ga kenan ni idan na biye maka zan dawwama ne babu ƴanci shi ya sa na saka aka mayar mini saboda wannan sana,ar da ita nake tallafawa kaina" ,Tana kaiwa nan ta ɗauki ledar farar ta ta ci gaba da ci.
Rasa ma abin da zai ce ya yi sai kawai ya juya fuuu ya fita, Meenal da take laɓe bata zaci fitowarsa a lokacin ba, sai kawai ta gan shi, rai a ɓace ta sha gabansa cike da ƙaraji ta ce
"Tun wuri ka saka Æ´an nepa su zo su yanke wutar nan tun da babu yawunka wajen mayarwa, kana mai gida mace ta yi abu babu izininka kenan ka zama mijin ta ce, nan gaba duk hukuncin da ka zartar ba za ta bi ba" Shiru ya yi yana nazarin maganarta, ya juya kenan zai koma yan saukewa Sadiya ya nuna mata bata isa ba sannan ya saka a yanke mata wutar sai kawai ya ga Sadiya ta fito kamar an jefo ta rai ta haÉ—e ta kalle su ta ce
"Idan bai zama mijin ta ce ba ai ya zama mai ɗaukan zugar mace!. Wato dama ke kika saka shi aka yanke mini wutar ɓangarena, to wallahi wallahi wallahi ki fita idona na rufe don shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne, kuma wutar nan yadda aka mayat da ita ta maidu in dai kuɗin wuta ne zan ke biyan kayana, amma furucinki ya nuna ba wai a kan kuɗin wutar ba ne baƙincikin sana,ar ne kike...
Hannu Meenal ta É—aga mata tana faÉ—in
"Ahir ɗinki Sadiya!. Na fi ƙarfin na miki baƙnciki a kan wannan sana,ar da bata taka kara ta karya ba"
Sadiya tana riƙe ƙugu ta ce
"Guntun gatarinka ya fi sari ka bani," Sai kuwa Meenal ta fara masifa tana cewa ta msta gorin sana,a shi kuma yana tsaye ya kasa crwa komauɓi don Sadiya ta goge masa hadda bai zaci za ta rikice har ta ƙwatawa kanta ƴanci ba.
FaÉ—a ne ya kacame a tsakanin su amma Meenal ce take ta kumfar baki a dole sai an cirewa Sadiya nepa ita kuma Sadiya ta ce wallahi babu wanda ya isa ya cire mata nepa.
Haka ta koma É—aki tana faÉ—in
"Wallahi idan aka cire mini nepa sai na kirawo ƴan nepa sun cire wutar gidan gabaɗaya sai dai kowa ya zauna babu nepa, in kuwa har wani ɓangare na gidan nan zai zauna da nepa to dole ya kasance nawa ɓangaren ma akwai wuta, domin ni ma mutum ce kuma ni ma matar gida ce kamar yadda kike matar gida" Tana jin su suna ta bala,i ita dai gabanta ma faɗuwa yake lokacin da take yin faɗan, amma ta daure ne saboda ta lura matsawar bata ƙwatawa kanta ƴanci to tabbas shan ruwa a gidan ma sai ya gagare ta, ga shi yanzu za ta yi haihuwa ta biyu kenan ita da ƴaƴanta za su rayu babu ƴanci a cikin gidan.