Sashe 79
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ƙawata ya ne?" Amatullahi ta faɗa tana jiran kanun labarai duk da zuciyarta tana cike da zulumiin jin labarin tana jin babu daɗi don ta ita ma ta matsu ta samu miji ta yi aure ƴan unguwa sun ishe ta da tambayar aure da kuma masu faɗa mata magana a fakaice wato gorin aure tamkar dai a kansu take ko kuma su suke ciyar da ita da ɗaukan sauran ɗawainiyarta, mutane basa tunanin cewa shi aure lokaci ne idan har mutum bai yj aure to lokaci ne bai yi shi ma ba a son ransa ba, don wasu ƴanmatan ana sakawa suke jjn tamkar su kai kansu ɗakin miji saboda yadda ake nuna musu habaici da gorin auren, bayan auren nan ba farilla ba ne sunna ne kawai me ƙarfi. Wasu kuma in suka samu miji sai ɗagawa da girman kai su dole matan aure suke nunawa wanda basu yi auren ba tamkar su suka hana kansu auren.
Aliya ta ce
"Wallahi ni kaÉ—ai na san irin farincikin da na kwana da shi, ai hatta Kasim ya dangwali albarkacin farinciki da nake ciki"
Amatullahi ta ce
"Shegiyar uwa sai bukka wato dai shi ala dole ya É—auka faranta masa aka yi bai san abin ne hawan hawa ba,, to yanzu mene ne kanun labarai?" Ta tambaya cike da fargabar jin amasar tambayarta
Aliya sai da ta yi wata dariya mai haÉ—e da shewa ta ce
"Babu tantama kuma babu wani tunani tabbas na san aiki ya kammala saura abu ya dara aiki don a yadda na fahimta mutumin mayen tuwo ne kin ga kuwa ai tuni ya antaya tuwon nan cikinsa sauran kuma ya fara fuskantar mulkin mallaka daga gareni ke hatta Jidda wallahi sai ta gane ni asalin maƙiyarta ce don sai ta gwammace kiɗa da karatu domin matsawar na samu wata dama a kan Jidda wallahi sai na gasa mata aya a hanhu sai na sa ta wulaƙanta!" Ta ƙarashe maganar tana haɗe rai tamkar dariya bata taɓa kai ziyara fuakarta ba.
Amatullahi ta ce
"Kin min daidai ai wallahi kowa ya samu dama kar ya yi wasa da damarsa"
Aliya ta ce
"Ke dai bari ai abin yana min cuwo a ce Jidda ta mallaki abubuwan rayuwa ban mallaka ba wai har ni ce zan koma tamkar ƴar maula a wajenta wato tana ɗakko kuɗi ta bani wai ni Aliya kyakkyawa me aji da jiji da kai ni ce Jidda ta bani kuɗi wai da kuɗin Jidda na saya waya taɓɗi!".
Sun jima suna tattaunawa suka yi sallama ta ce duk yadda ake ciki za ta sanar da ita. Tana kashe kiran sai kiran Umma da shigo ta ɗaga Umma jin muryar Aliya fess cikin shauƙi tun bata gama jin kanun labaran ba ta carara guɗa, ita ma Aliyar guɗar ta ɗauka kafin daga bisani suka ɗauki shewa kamar wasu sa,annin juna ba uwa da ƴa ba.
Umma tana gyara É—aurin É—ankwali ta maido da shi gaban goshi ta ce
"Wallahi ba ke kaɗai ba Aliya hatta ni zan tsula tsiyata musamman idan aka rufe baki da ƙwaƙwalwar wanann uban naki, dama shi yake taka min birki yana hana ruwa gudu"
Aliya ta ce
"Bari dai Umma sirikar Ibrahim ai an buga an barki sai kin zama zakaran gwajin dafi a cikin sirikan masu kuÉ—i" Suna ta tattunawa suka yi sallama Aliyar tana faÉ—in bari ta kira Jiddar ta ji za ta zo ta kira Umma ta faÉ—a mata yadda ake ciki.
Sunan Jidda ta kamo ta shiga kiranta, lokacin Jidda tana tsakiyar falon ƙasa tana sanya hijabin ta za ta tafi asibiti don har ta faɗawa direba kuma ta ji ya fito da motar jiran fitowarta yake, duk da sun yi waya da Ibrahim ya ce Daddy ya farfaɗo sai dai rashin ƙarfin jiki da kuma gefen bakinsa ma da ya ɗan karkace don yana da hawan jini. Sai ta ce za ta taho asibitin ya mata na,am don yana ta so ma ya koma gidan ya yi wanka amma ya kasa tafiya duk da damuwar Mummyn ma ta ragu.
Saude ce sunkuye a gabanta tana jera kwanukan a cikin kwandon da za a tafi da abincin asibitin, Saude tana É—auke da kwandon tana biye da ita sai ga Baba Kulu ta fito tana cewa ta yi wa mai jikin sannu amsawa ta yi cikin girmamawa domin tana ganin Baba Kulu tamkar uwa a gare ta saboda Jidda ta san muhimmacin furfura.
Baba kulu ta juya ta koma tana ci gaba da abin da take yayin da wayar Jidda ta shiga ruri tana dubawa ta ga sunan Aliya É—agawa ta yi tana faÉ—in
"Barka da safiya ƴar uwa rabin jiki fatan kin je gida lafiya" Aliya da ta koma ta kwanta a doguwar kujera haɗe da ɗaga ƙafafu sama ta ɗora daga can saman kujerar, hannunta ɗaya yana tallafe da wuyanta tana yatsina fuska ta ce
"Lafiya" Ta faɗa a takaice don har ta fara wulaƙancin da za ta gara Jidda tun daga yanzu, don duk tunanin magani ya ci
Bayan sun gaisa Jidda take faÉ—a mata Baban Ibrahim ne ba lafiya a asibiti ma ya kwana yanzu ma can za ta tafi, Aliya ta ce
"Amma jiya baki faÉ—a min ba"
Jidda ta ce
"Ai rashin lafiyar jiya da dare ne" Aliya ta yi shiru tana son jin kanun labarin yadda aka ci abinci da cokali sai dai ta rasa ta ina za ta fara zuwa can wani tunani ya faÉ—o mata hakan ya sa ta ce
"Allah bashi lafiya, ki masa sannu sannan ki wa Ibrahim É—in ya mai jiki"
Jidda ta ce
"Zai ji in sha Allah ai a can asibitin ma ya kwana"
Aliya ta ce
"Ayya bawan Allah sarkin son tuwo" Ta faɗa haɗe da sakin kunnuwa don jin abin da Jiddar za ta ce, ƙirjin Aliya yana sama yana ƙasa duk da ta san ba za ta ji wani labari makamacin wanda take tunani ba, amma dai sai ta ji tan fargabar jin amsar, domin ta san tabbas ta yi furucin da za ta samu amsar tambayarta.
Jidda ta ce
"Wallahi kuwa ke dai bari ai duk ƙaunarsa da tuwon nan jiya sai da ya gutsura zai kai bakinsa aka sanar da shi rashin lafiyar Daddyn wallahi tsabar ruɗu bai san ya saki cokali mai ɗauke da tuwon ba, tuwon da ko a bakinsa bai ɗanɗana ba jiyan"
Dummm dududummmmm gaban Aliya ya buga da ƙarfi a take ta ji numfashinta yana neman barin gangar jikinta, bata san ya aka yi furucin ya fito ba ta dai ji bakinta ya furta
"Bai ci tuwon ba? Ko a bakinsa bai ci ba kika ce Jidda?" Ta taɓbaya a ruɗe tana tashi zaune cike da firgici, Saude kasancewar wayar ana iya jiyo maganar kuma tana tsaye ne daga gefen Jidda tana riƙe da kwandon a kan kunnenta ta ji maganar Aliya da take yi a gigice cikin diriricewa fakar idanun Jidda ta yi ta kauda kai gefe tana sakin dariyar gefen baki tana danne dariya mai ƙarfi da take son ƙwace mata, domin ta gama harbo jirgij Akiya ai dama ta san Aliya ba za a yi abin kirki da ita ba ta gama fahimtar cin duduniyar Jidda take.
Jidda kuwa duk da ta ji yanayin da Aliya ta mata tambayar sai bata kawo komai ba, tunanin ta ko yadda ta ji an ce yana son tuwon kuma bai ci ba shi ne take jimantawa, amma ai a ganin Jidda lafiyar mahaifi ta fi komai.
Baki ta buÉ—e ta ce
"Wllahi ko ɗanɗanawa bai yi ba ai tuwon ma ya lalace an zubar an wanke kwanon" Aliya bata ce komai ba illa sakin wayar da ta yi ba tare da ta sani ba, taimakon ta da Allah ya yi a kan kujera ta faɗi tsaye Aliya ta miƙe cike da tashin hankali tana tunanin abin da Jidda ta faɗa mata. Jidda kuwa da ta gaji da faɗin hello hello sai kawai ta datse kiran ta shiga mota Saude ta ba direban kwandon ya saka a a motar aka wangale musu get suka fita daga gidan.
Tsaye Aliya ta tashi hannu biyu a kanta, hatta ɗankwalin kanta tuje shi ta yi tamkar mahaukaciya sabon kamu haka ta koma, tana tuna irin tarar aradu da ka da ta yi wajen isar da cikalin wannan sannan yanzu ita idan har an kwatsa cokalin a cikin ƴan uwansa cokula ba za ta taɓa sheda shi ba wataƙila ma asirin jikin ya karye, tunanin ta ɗaya idan ta je ta sanar da bokanya abun da ya faru kar ta ɗakko mata jan aikin da ba za ta iya ba, tun da a ranta tana raya babu gudu babu ja da baya!
BABA
Ya yi baƙincikn rasa gutsuren tsumman rigar da ya gutsure a jikinnrigar ɓarawo da a tunaninsa da ita zai riƙe matsayin sheda ko wataran za a ga wanda ya saka yagaggen kayan sai ya gane amma dai ya sanya a ransa idan kere yana yawo zabo yana yawo watarana za a haɗu. Bai san cewa ƴaƴansa ne suka ɗauke yadin ba sannan aka haɗa aka ƙone da wanda ya gutsure ɗin da kuma gutsuren saboda tsaro ba don tsoro ba.
Zaune yake da kwanon tuwonsa a gabansa yau a tsakar gidan yake a zaune tun da ya kai lomar tuwon farko ko taunewa bai yi ba bare a samu damar haɗiyewa da sauri ya dawo da ita yana tofara kamar wanda ya ci kashi. Hannunsa ya tsame ya shiga ƙwalawa Mama Bilki da ta yi zaman dirshan a tsakiyar ɗakinta tana cin tuwonta bayan ta barbaɗa masa maggi dunƙule jin kiran ya ƙi ƙarewa ta fito tana suɗe hannu ta ce
"Haba Malam kira sai ka ce makaho ai ya kamata kake numfasawa"
Baba ya ce
"Abin da ya fi numfasawa zan yi, ke yanzu wannan ba abin kunya ba ne ki ɗauki wannan tuwon naki ci karka mutu ki kaiwa miji, ban da rashin tunani kina zaune gidan kishiyoyi uku ke ta huɗu amma baki iya tattalin miji ba? Bari ki ji mata wanda suka gama karantar hakayyar maza a kwanon mazan suke samun gurbi a zuciyar miji" Kallon sheƙe ta masa ta ce