Sashe 63
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana ganin yadda ta yi masanyan yakalmi kuma ba ƙafafun bane sai ta juya da sauri don kar a lura bata san Sadiya ta gani ba hatta Meenal ma ta gani kawai dai ta ce a zuciyarta
'Kaɗan kika gani wallahi mu zuba mu gani' Nasir kuma kafin Hajiya ta ɗakko takalmin ya juya ya fita matasan yaran nan suna biye da shi da suka fita ya basu ɗari biyu su raba, bayan motar ya buɗe ya ɗakko manyan ledojin da aka yi take away na snacks da drinks masu sanyi haka ya shigo gidan da ledojin riƙi-,riƙi.
Meenal ganin Sadiya ta baro wajen famfo sai ta aikawa Sadiya harara kuma Sadiyar ta gani amma ta yi kamar bata gani ba Meenal kuma a zuciyarta ta ce
'Ina nan zuwa kanki kema'
Hajiya kuma tana sako takalmi ta ga babu Nasir kafin ta gama tambayar kanta ina yake sai gashi ya shigo da ledojin wannan Meenal ta nufi inda yake ta tare shi tana aika masa sannu, haɗe da miƙa hannu ta maƙalo bayansa suke tafiya inda shi kuma yake ta kaucewa alamar kunyar Hajiya amma Meenal ta ƙi sakin sa har da saka ɗaya hannunta ta sumbaci hannun nata ta kai masa saman nasa bakin. Hajiya kallo ɗaya ta musu ranta ya ɓaci ga ƴanmatan nan su Safiyya a kicin sai ƙaran kwanuka take ji alamar hada-hadar girki waau suna yayyakan kabeji so take ta ce masa ya yi taka-tsan tsan da mukullinsa sannan ya matse hannu da aljihu amma kuma ta kasa tsayawa saboda yadda Meenal ta ƙaƙabe masa.
Hanyar waje ta yi tana faÉ—in
"Nasir ka zo waje ina son ganinka" Sadiya da tun da ta koma ɗaki ta laɓe a labule tana kallon dirama, komawa kan kujera ta yi ta kwanta tana ta dariya Kalifa yana taya ta duk da bai san dariyar mene ne take yi ba.
Meenal tana ganin Hajiya ta fita ra sake shi, ta karɓi kayan sai kuma ya juya ya fita don amsa kiran Hajiya, ko da ya zo ƙofar gidan ya same ta tsaye tana riƙe da ƙugu ga kuma jaka a rataye sai kai komo take bata ma san ya zo wajen ba sai da ya kira sunanta da sauri ta waigo tana faɗin
"Nasir mu shiga cikin mota maganar nan ba ƙarama ba ce akwai gagarumar matsala don da alama abubuwa sabbi za su kunno cikin rayuwarmu da muke lallaɓawa" Ta faɗa bata jira cewarsa ba ta buɗe gaban motar ta shige cike da rashin fahimta ya shiga mazaunin direba tun bai gama zama ba ta shiga faɗin ya rufe ƙofa rufewa ya yi sai kuma ta ce
"Nasir akwai matsala wallahi" Cike da faÉ—uwar gaba ya ce
"Allah ka mana maganin matsala, Hajiya matsalar mene ne?" Idanunta da suka kaɗa suka yi jawur saboda ɓacin ran abubuwan bazatan da ta ƙunsa daga Meenal ta ce
"Nasir Meenal ce matsala" Cike da rashin fahimta ya ce
"Meenal kuma?"
Hajiya a faÉ—a ce ta ce
"Meenal mana bari na faɗa maka abin da baka sani ba tana cikin hayyacinta babu wani jifanta da aka yi ta tabbatar min da hakan da bakinta da alama yarinyar nan zaɓen tumun dare muka yi Nasir wallahi bata da ƙudurin sa ya wuce ta rusa mu ta faraƙa mana dangi, ka ga kai kaɗai ne gatanmu ni da marayun Allahn nan su Husna yanzu wannan yadda daga juya zuwa yau take saka ka ɓarin kuɗi kuma Nasir ko musu baka yi duk abin da ta lissafa sai ka siyo sannan uwa uba ka ɗauki mukullin store ka bata" Ɗan dimmm ya yi sai kuma kafin ya ce wani abu ta ce
"Wallahi so take ta mallake ka ka fi ƙarfina ta mamaye gidan nan don haka dole ka tashi tsaye ka zama namiji ka matse bakin aljihu ka ƙwace mukullin store karka sake bata ita ma kake tsakura mata abincin kamar yadda kake tsakurawa Sadiya wallahi da ni take zancen dankalin ma an fasa aiko mata can za kake zuwa kana ci kamar yadda ake yi wa Sadiya kuma a gobe ba sai jibi ba Meenal za ta fara ɗora tukunyar tuwo, kuma gawayi za take hurawa wannan gas ɗin dole a kai min gidana ko ka je ka aiyar da shi amma ba a gidan ɗana ba" Tun da ta fara maganar yake kallonta ya mayar da hankali kanta yana sauraro da nazarin ta inda zai fara wannan gagarumin faɗan da take son kwasowa don ya lura Meenal ba kanwar lasa bace kuma ba za ta lamunci wannan abubuwan da aka zana ba kenan da sauran rina a kaba.
Baki ya buɗe zai yi magana sai dai ƙaran ƙwanƙwasa ƙofa da aka yi shi ya dakatar da shi daga furta komai, daga shi har Hajiya suka juyo don ganin mai bugawa sai dai wanda suka gani tsaye ya basu mamaki ba kowa ba ne illa Meenal da take tsaye riƙe da tsantsa hannunta ɗaya riƙe da wani ƙaton kwando, ganin sun maido da kallonsu kanta ta saka hannu ta buɗe ɓangaren da Hajiya take haɗe rai ta yi ta ce
"Na gama jin duk abin da kuka ce dama tun da na ga kin ce ku je wajw kuma na san halinki shi ya sa ban yi ƙasa a gwiwa ba na biyo bayanku na laɓe a zaure ina kallonku ta jikin tular ƙofa, kuna shigewa na zo jikin ƙofar na tsaya amma kasancewar hankalinku ba ya wajena babu wanda ya ganni har na koma na ɗakko kwando na dawo, don haka abin da nake so da ke Hajiya ki dakata da wannan faɗan don wallahi ba za ki iya ba, kuma ba za ki ci gabala ba kawai ki sakar mini" Hajiya baki sake take kallon Nasir ganin bai yi kataɓus ba wajen tsawatarwa Meenal a zafafe ta ce
"Nasir ya ka tsaya kamar sauna kana jin abin da ta ce?" Kafin Nasir ya ce wani abu Meenal ta ce
"Ina shawartarki Hajiya da ki cire ido da hannunki a gidan ɗanki shi ne kima da mutuncinki don wallahi ko ana mutuwa ana falkowa ba zan taɓa ɗora girki a gawayi ba, sannan mukullin store daga yau ya bar hannun Nasir in kin ga ya taɓa mukullin store to tabbas kayan abinci ya siyo za a saka a ciki, abu na gaba ba uwar miji yanzu babu ruwanki da aljihun ɗanki a kan lamarin gidansa tun da matar mutum ita take ɗauke ɗawainiyarsa ta cikin dare don haka ta cancanci a mata komai shin in ba matarsa ba waye zai ɗauke masa wannan ɗawainiyar? Don haka ni nake kwana da miji kuma ni zan yi iko da abina ba wai a mini iko da shi ba ikonki ya tsaya iya ke da shi...
Hajiya ta hankaɗa ƙofar ta sako ƙafa waje tana nuna Meenal da yatsa ta ce
"Wallahi ƙaryar rashin kunya kike da a ce na san haka kike da Nasir bai aure ki ba"
Meenal ta ce
"Daga baya kenan wai an yi sadaka da karuwa, to ai duk ɗaya an ce da karuwa hayo gado yanzu ma lokaci bai ƙurw miki ba za ki iya saka ya warware igiyar" Nasir da ya buɗe baki zai yi magana sai ya ji kansa ya sara hakan ta sa ya zuba musu na mujiya, domin cikin maganin da ta saka da dare har da mallaka ciki.
Hajiya ta ce
"Daga na gidan uwarki zan je, in mata bayanin yadda kika sauya halinki a kwana ɗaya, ai ni ƙawar uwarki ce ko wannan kaɗai kya duba"
Meenak ta ce
"Ai in dai tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ke baki duba dangantakar ba kike mini taka haye?"
Tsaki kawai Hajiya ta yi don ta hango yadda za ta magance wannan matsalar
Meenal kuma ta rausayar da kai tare da zumɓura baki tana wani shagwaɓe fuska cikin muryar ɓaci ta ce
"Zumana wannan kwandon gidan Hajiya za ka kaini zan kwaso dankali, su Safiyya suna son sakawa a miya ƙwan ma za su yi amfani da shi, ka ga sai a kwaso kayan duka in ya so gobe in za a yi break fast ɗin sai su Husna su zo su yi in ɗauka musu na Hajiya ka ga ni ba zan iya aiki ba jikina ciwo yake" Ta faɗa tana yin farrr da idanu, Hajiya tsabar mamaki na ganin Meenal ko kunyarta bata ji ya sa ta kasa magana, da sauri ta juya don ta ga abin da Nasir ya yi kawai sai ta ga ya saki baki yana murmusawa.
Kafin ta ce wani abu Meenal ta ce
"Hajiya ɗan koma baya ni sai na shiga gaban, kin san masoya sabbin ma,aurata, ko kuma ya tare miki napep" Kakaraf Hajiya ta ƙarasa hankaɗa ƙofar har ra buga jikin kwandon hannun Meenal don ta ga kamar kare ya ɗauke zuciyar Nasir hakan na tavbatar mata da cewa za su shiga tsaka mai wuya dole ta magance matsalar nan da kanta don ita bata taɓa jin amarya a ranar farko tana fita daga gidan miji ba.
Tana fitowa daga motar ta ce
"Allah tsine soyayya, ni za ki gwadawa bariki, tattabaru kuke ƙarewa aure" Ta faɗa tana ɗaga hannu za ta zabgawa Meenal mari.
ALIYA
Aliya gabanta yana faɗuwa a lokacin da kiran yake shiga tana fatan ya ɗauka kar ya kawo mata matsala domin zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin muryarsa, ta yi kewar ganinsa bata san ma haka take ƙaunarsa ba sai yanzu da suka yi nesa da juna, tun da ta san tun da ya fara zuwa wajen Jidda in har ya zo tana ganinsa amma yanzu tun da ya ɗauke Jidda ai kuma babu inda za take ganinsa abin haushin ma ko hotonsa bata da shi, rabon da ta sanya shi a ido tun ranar da suka kai Jidda gidanta da ta yi ido huɗu da hotonsa a falo.