← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 106

Sashe 4

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mama wai mai ya sa ba za a warware min matsalolina ba, shikanan ni a haka zan ci gaba da rayuwa? ga matsalar miji ga ta dangin miji, ƙannensa sun raina ni mahaifiyarsa bata ƙaunata wallahi Mama hatta Kalifa da babu abih da ya tare musu basa son yaron nan kamar wanda agola ne sgi ba ɗan gidan ba" A daidai nan Baba da ya dawo daga masallaci zai wuce turakarsa ya fara jin tashin magana da ya ƙarasa jikin ƙofar sai ya saurara ta haka ya gane muryar Sadiya ce sai dai ba ya iya gane mai take cewa.

A fusace ya bankaɗa labulen, sai kuwa ya fara tozali fa ruwan hawayen Sadiya, gabansa ya yanke ya faɗi, Mama kuwa sosai ta shiga ɗimuwa na ganinsa babu zato babu tsammani, Sadiya kuwa jikinta ne ya ɗauki karkarwa. Baba idanu ya ƙanƙance yana yatsina fuska ya shigo ɗakin ko takalman ƙafarsa bai cirw ba saboda tsabar ɓacin rai ya tsaya yana bin Sadiya da kallo tare da jefa mata wani mugun kallo a harzuƙe ya ce

"Uban mai kike yi a gida Sadiya? Ko Nasirun ne ya mutu?" Ya faÉ—a yana jiran jin ba'asi Sadiya a zuciyarta ta ce

"Ni da zai mutu ma da na huta da wannan halin da nake ciki, in banda rashin kwanciyar hankali a ce mace tana jin tamkar da mutuwa mijinta ya yi. A fili kuma ta buÉ—e baki cikin ladabi ta ce

"A'a Baba yana nan lafiya ƙalau, dama zuwa na yi na kawo muku wuni...

Saurin katse ta ya yi da faÉ—in

"Sadiya mai ya sa kike da tada zaune tsaye ne wai? A kan mai na siyar da akuya za ta dawo taje cinye mini danga? Har ki ɗakko ƙafa ki taho ga ke ga ɗanki wuni guda cur, " Ya faɗa yana maida kallonsa kan Mama ya jefa mata tata tambayar ta hanyar faɗin

" Kukan uban mai take yi?" Mama inda-inda take yi sai ya katse ta da faÉ—in

"Ba magana nake miki ba? Ko wani sabon munafurcin ne hallaw kika saka yarinyar nan a gaba kina mata tambayar munfurci so kike ki kashe mata aurw ta dawo ta zauna a gida na samu na kawar da ita ina ƙoƙarin kawwar da sauran ƴan uwanta amma kw kina neman jiƙa mini aiki, to wallahi duk ranar da auren yarinyar nan ya mutu ki yi kuka da kanki" Ya faɗa yana nuna Mama da yatsa. Mama kai ta sunkuyar ya ƙara kallon Sadiya ya ce

"Kukan mai kike?"

Sadiya ta ce

"Wallahi Baba ko kaÉ—an ba na jin daÉ—in gidan Nasir kawai yana ta gana mini azaba da gasa mini aya a hannu... Katse ta ya yi ta hanyar dakatar da ita.

Ya buÉ—e baki a faÉ—ace ya ce

"Ke banda rashin hankali wane shegen ya ce miki aljanna tana samuwa da sauƙi? Ko ana nemanta ta daɗi to ki buɗe kunnuwanki ki ji Nasiru ko yankan namanki zai ke yana ci ɗanye ba zan taɓa ganin laifinsa ba saboda rage mini aiki ya yi duk wanda zai auri ƴarka ya rage maka ɗawainiya da ita, to haƙiƙa ya gama maka komai a rayuwa, ki zauna a ɗakin ki duk runtsi ƴan uwanki gasu nan barkatai ban da maganin farin jini babu abin da nake ɗirka musu ko sa samu miji ma" ,Tun da ya fara magana kanta a sunkuye kuka kawai take shi kuma Kalifa sai suɗe plate ɗin da ya cinye tuwon yake.

Sai da ya numfasa ya ce

"Ki tashi a kan sawunki ki koma ɗakin mijin ki" Da toh ta amsa masa tana tashi tsaye ta ɗauki Kalifa ko hannu bata wanke masa ba a haka ta saɓa shi a baya, siyam - siyam kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta nufi bayan ƙofa ta ɗauki takalmin dakyar ta iya furta

"Na tafi Mama" Mama kuwa kai kawai ta shiga gyaɗa mata, raɓa gefen Baban ta yi ta fito duk abin nan da ake Sumy tana jin su zaune take a tsakiyar bedroom ɗin ta yi ɗai-ɗai da ƙafafu tana cin doya da ƙwai sai yankakkiyar gurasa a gefe wanda wani saurayi da ta gaɗu da shi a hanyarta ta dawowa daga makaranta, daga ya tsare ta yana tambayar sunanta da kwatancen gidansu shikenan sai ta ce ya saya mata, dama tana ta tunanin cin ɗumamen tuwon da ta ajiye. Ya siya mata ta saka a jaka bayan ta kwatanta masa gidan nasu, dama tana da abin da za ta ci amma ta kafa tijara sai da Mama ta biya ta kuɗin ɗumamen da aka ba ɗan ƴat uwarta Kalifa saboda rashin mutunci.

Tana fita tsakar gidan Baba ya fara sababi yana faÉ—in

"Saura in ga kin kwaso min ƙafafun ki a kwana kusa kin dawo min gidan nan, idan ba dubiya ko wani gagarumin dalili ba" Ya faɗa yana ɗaga murya, hakan ne ya ankarar da mutanen gidan zuwan Sadiya don lokacin da ta zo kowa yana ɗaki, amma yanzu kowa ya san ta zo.

Mama Bilki da take zaune a ɗakin ta tana cin garin kwaki da suga jin furucin Baba ta sheƙe da dariya ta ce.

"Wato ƴar da ake tunƙaho ta samu miji wasu basu samu ba, ita ce ake yi wa kashedin dawowa gida hummm a yi dai mu gani in tusa tana hura wuta, da yake mijin ma ɗan tijara ne ba wani mai hannu da shuni ba ne da mai kuɗi ne in sau ashirin za ta zo gidan ai ba za a gaji da ita ba saboda an san nauyi za ta rage in ta zo, amma da aka san talaka ne mijin ita ma Allah baku mu samu ce ai gashi nan da tsakar rana ana korarta" Ta faɗa tana dariya Aisha da take danna waya bata ce mata komai ba.

A can tsakar gidan Sadiya ta juyo ta ce

"Baba don Allah ka barni in an yi la'asar rana ta yi sanyi sai in tafi, amma rana a buÉ—e kuma wallahi gori yake min duk ranar da na koma gida da wuri bare yau da tsakar rana"

Baba ya ce

"Ya miki goriba ba gori ba, ba mijinki ba ne ai in baki sani ba ki sani baki da gidan da ya fi gidan mijinki"

Haka ta juya ta tsaya a zaure ta goge hawayen duk da kowa yana ganinta zai gane ta yi kuka, gashi Baba ya ƙi barin ta zauna a gidan ma bare ta yi ɗan zance nauyin zuciyarta a ragu. Baba kuwa har bayanta ta bi sai da ya zo har ƙofar gida ya tsaya ya hange ta ta kama hanyar gidanta duk da akwai tazara sosau daga gidansu zuwa gidan nata. Cikin gida ya koma ta ƙara zuwa ɗakin Mama Talatu ya ƙara kora mata kashedi sannan ya buɗe ɗakinsa, ruwa ya ɗauka tare da awararsa ya zauna ya shiga ci.

A zuciyarsa yana faÉ—in

"In banda abin Sadiya ke da Allah ya dube ki a haihuwar fari ya baki É—a namiji yanzu wannan yaron yana tasowa ba kin huta ba, zai ke É—aukan É—awainiyarki, ni ba gashi nan ba sau mata rigis nake haifa"

A ɓangaren Sadiya tun da ta kama hanya take ta zancen zuci, ta san yau sai dai ta tashe kunnuwanta don Nasir sai ya yayyanka mata baƙaƙen maganganu, ya faɗawa iyayenta maganar da take sosa mata rai kwata-kwata bai san darajar mutane ba. Gabaɗaya ta gaji a haka ta ƙaraso unguwar tasu, tana shawo kwanar gidan nata, sai ga Nasir a bayan mashin za su wuce ta, da alama daga gidan yake, amma kallo ɗaya ya musu ita da Kalifan ya ɗauke kai tamkar bai san su ba, kai tamkar ma babu wata alaƙa a tsakaninsu, a nata ganin ko da ita bai nuna ya santa ba, ai ya nuna ya san ɗansa tun da jininsa ne, duk da ta san ɗan nasa ma ba wani son sa yake ba.

Haka ta daure ta cigaba da tafiya ga zafin rana, jikinta tana jin yadda gumi yake zuba a bayanta duk rigarta ta jiƙe. Da yake a ƙofar gidan nata akwai matakala guda biyu wanda sai ka taka sannan za ka buɗe ƙofar gidan, har sai da ta taka matakalar tana tsaye a ka ta buɗe jakarta pose wacce mukulli ne kaɗai a ciki ta zaro mukullin tana shirin saka mukulli ta buɗe jamlock ɗin amma sai ta ga wani abu a jikin ƙofar wanda ya yi matuƙar bata mamaki...

MAMAN AFRAH
09025576222
[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/IQU3wL7NUTCCqrbtxkJaaz?mode=ems_wa_t

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 3️⃣

Fitowarsa kenan daga wanka jikinsa ɗaure da towel inda kansa yake tsane ruwan da yake jikin kwantaccen gashin kansa, ƙarasowa ya yi tsakiyar ɗakin har lokacin yana goge gashin kan nasa gaban madubi ya ƙarasa ya ahiga shafawa fatarsa mayukan da suka dace da ita mayukan da suke jibge da turaruka a kan madubin tamkar an buɗe shago.

Ibrahim kenan ɗa ɗaya tilo a wajen Alhaji Sule wanda yake kira da Daddy ɗa kuma a wajen Hajiya Faty wacce yake kira da Mummy. Fari ne dogo sannan ba siriri ba ne faffaɗa ne mai yalwar kwantaccen gashin kai, yana da manyan idanu wanda suka ƙawatu da zara-zaran gashin ido da gashin gira yana da ƙaramin baki pink lips, sai dai bashi da hayaniya.

Ɗan gata ne na ajin ƙarshe a wajen iyayensa mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne kuma tsohon ɗan siyasa, iyayen Ibrahim suna matuƙar son sa, basa son ɓacin ransa, sai dai bashi da mata hatta budurwa ma bashi da ita, tun da ya dawo daga ƙasar america da ya kammala karatunsa yake kula da kamfanonin mahaifinsa.
Chapter 4 · 0% Book details