Sashe 38
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wannan halin ne har ta kwashe wata biyu, sai dai daga ɓangaren Nasir bata sauya zani ba don har lokacin yana nan a kan bakansa na ƙin wadata su, sai kuma ƙuntata mata da ya ci gaba da yi don a zuciyarsa burinsa damuwa ta mata katutun da zai yi sanadin zubewar cikin don shi yanzu buri da fatansa da duk wani tunaninsa yana kan amaryarsa Meenal.
A wata ranar talata da safe ta tambaye shi zuwa gidan kakarta mahaifiyar Babanta, hakan ya amince cike da zumuɗi don shi ya fi so ma take yawo amma kullum tana gida bata yawan fita, sannan ya san gidansu ba wani iya riƙe ta za su yi ba shi ya sa ko ta je da wuni uban yake koro ta, wannan ya sa yake cin karensa babu babbaka kuma yake gara Sadiyar don ya san zaman gidansa ya zame mata dole sannan kuma farilla ne tusa a cikin bacci.
Ta shirya tsaf ta shirya Kalifa ta rufe gidan duk da akwai tazara amma haka suka yi tafiyar ƙasa don bata da kuɗin napep. Da farinciki Kaka ta tate su tana ta yi wa Kalifa wasa, zama suka yi ta ɗakko fura wacce ta ji nono ishashshe ta dama musu suka sha, sannan Kalifa ya ci gaba da wasan sa. Zuwa can Kaka ta ce
"Halima" Sadiya ta amsa Kaka ta ce
"Kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa dubi yadda duk kika lalace kin yi baƙi kin rame duk kin fita hayyacin ki" Sadiya ta ce.
"Kaka ina cikin damuwa tabbas, kuma mafita ce ma bani da ita, kin san dai yadda aka yi auren nan to yanzu Abban Kalifa yana takura min ne kamar ma ya gaji da auren shi kuma Baba ko gidan na je babu wanda yake sauraron damuwar da nake ciki daga shi har Mama, da a ce suna jin damuwata kuma su ja masa kunne da abubuwan za su yi sauƙi, amma sun nuna masa bani da daraja, wataran ma Baban haka zai ce in koma ko da kuwa sun san zaluntata ake yi"
Kaka ta ce
"Sadiya tabbas Bala ba shi da hali kina gani dai ban isa in shata masa layi a kan komai ba, ni sai in manta ma ban ganshi da idanun nan nawa ba, idan ma ya zo a tsaitsaye zai gaisheni ya kama gabansa" Ta faÉ—a cike da takaici bata san mai ya sa wasu Æ´aÆ´an ko kaÉ—an basu san darajar iyayensu ba.
Sadiya ta ce
"Yanzu babu ruwansa da damuwarmu so yake ma in ke É—aukan É—awainiyar kaina tamkar wacce take zaman kanta ko kuma zaman zawarci, wallahi kwanaki har gorin sana'a ya min ni kuma bani da jari sannan shi ba tallafa min ba zai yi" Kaka ta nisa ta ce
"Dama idan mace tana gidan aure kuma take son yin sana'a ai mijinta ne zai tallafa mata ya bata jari sannan ya bata ƙwarin gwiwa amma in baka da shi ina ake so ka je ka samo? Ko sata ake son ka yi, wasu mazan basa yi wa kansu adalci suna da halin da za su wadata iyalansu da abu amma sai su hana su sannna su fita waje suna yin bajinta da birge wasu mutanen, in ba bajinta ba ke bai baki ba ya je yana ba iyayenki" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke mai nauyi kafin ta ce
"Ai lamarin Nasir sai dai addu'a amma ya fiya son kansa da yawa duk da yana samun gudummuwar mahaifiyarsa" Kaka ta ce
"Kowa ya yi na gari kansa Halima, sannan komai zai wuce ya zama kamar ba a yi ba, idan har yana sane yake yi Allah zai ƙwatar miki haƙƙin ki watarana zai gane kurensa sakayya tana nan tun da Allah ba ya yafe laifin wani a kan wani" Sadiya ta ce
"Haka ne" Kaka ta ce
"Wancan ƙatuwar akuyar tawa zan siyar dama jiya maƙocina ya saya ragon nan da na turki, to zan siyar da ita sai a cika, akwai Fauziya wancan amaryar da gidanta yake kallon gidan nan, na ji tana cigiyar wanda zai saya firjinta da yake ƙarami ne ita kuma tana siyar da pure water da kemon mango, da zuɓo sana'ar ta karɓe ta shi ne take so ta siyar ta sayi babbar freezer, sai in fansa miki nata firjin in auna miki zoɓo in bak ɗan kuɗin da za ki riƙe na siyan pure water ki je ki fara sana'ar kayan sanyin idan Allah ya saka miki albarka sai kin samu warakar wasu matsalolinki" Da sauri Sadiya ta matsa kusa da Kaka ta rungume ta idanunta har da ƙwallar farinciki cike take da murna jin Kakarta ta sama mata mafita abin da mahaifiyarta da ta san ciwonta ta kasa yi mata lallai yau tana cike da murna.
Kaka tana ta dariya tare da faɗin kar ta karyata, Kalifa ma ganin abin da yake faruwa ya taho ya zo ya tsaya yana kallonsu yana dariya duk da bai san musabbabin farincikin ba. Ta yi ta godiya ta kuma yi wa Kaka addu'a daga ƙarshe Kaka ta ce mata za ta kira ta a waya idan ana kammala cinikin sai a ba mai baro ya kai mata. Sai da ta yi magriba ta baro gidan Kaka zuciyarta washe.
Ko da suka dawo gidan ƙofar babu mukulli da alama mai gidan yana ciki, da sallama ta shigo ya amsa ciki ciki ta masa barka da gida, zaune yake yana cin doya da ƙwai da kuma naman balangu sai lemonsa fanta a gefe doyar ya ɗaukamda naman yanka biyu ya miƙawa Kalifa amma abin mamaki sai Kalifan bai karɓa ba, shi kansa Nasir ya yi mamaki sai ya ɗauki kofi ya tsiyaya lemon ya bashi sai ya karɓa ya sha ya miƙa masa kofin. Tana shirin shiga ɗaki ta ji ya ce
"Yau har aka kai dare lallai ko don gidan Kaka ne shi dama Baba ai ba ya ma bari a zauna a gidansa" Bata ce masa komai ba don ta san magana ya yaɓa mata, haka ta shige bedroom ɗin.
Da dare bayan ta kwanta, bacci ya kasa É—aukarta, saboda farincikij da take ciki, ko da ya hayo gadon sai bai mata magana ba ya shiga latsa waya, yau a falo ta yi wa Kalifa shimfiÉ—a don ra ga ya fara wayo kar wani lokacin ya je ya falka suna wani abin wannan dama lallata tarbiya ne wato kwanciya da yara masu wayo É—aki É—aya.
Sai da ya gama danne -dannensa ya ajiye wayar ya juyo yana fuskantar ta dama bai kai ga kashe fitilar É—akin ba ya ce
"Sadiya an Baba" Furucinsa kaɗai ya tabbatar mata da cewa lokacin amfaninta ya yi wato lokacin da zai nemi biyan buƙatarsa, tun da a wannan lokacin ne take iya ganin farin haƙorinsa ko mata magana babu hantara.
"Uhmm" Ta ce ba tare da ta kalli shi ba.
Ya ce
"Haƙƙina nake so yau kwana nake so in yi ina aiki" Cike da tsoro ta yi saurin kallonsa ya ɗage gira ɗaya ya ce
"Yes" ,Ta marairaice fuska ta ce
"Ka ga dai ƙaramin ciki ne da ni amma ya za a yi ka kwana kana abu ɗaya?" ,Ya ce
",Oh wato ke har wani lissafi kike da ban, to ni wannan cikin ma na manta da shi kuma ba na saka shi cikin lissafi" Maganar ta mata ciwo amma ta ƙyale shi, tare da bashi haƙƙinsa sai danya gaji don kansa ya barta, bayan komai ya lafa ta yi wanka ta zo yana zaune yana goge ruwan kansa ta ce
"Ina so za mu yi magana" A taƙaice ya ce
"Ina jinki" Ya faɗa yana ɗaure fuska dama ta san ƙarshen maganar tun da da ta gama masa amfani.
Cike da fargabar amsar sa ta ce
"Kaka za ta siya min frige in fara sana'ar siyar da ruwa da zoɓo ina ga har ƙanƙarar yara zan ke siyarwa... Tun bata ƙare maganar ba yake aika mata mugun kallo wani tsoronsa ne ya ɗarsu a ranta don ita bata buƙatar ko kaɗan ya ci mata zarafi baƙaƙen maganganunsa rai suke ɓata mata sai dai ta san akwai lokacin da Allah zai ganar da shi shayi ruwa ne!.
Cike da gadara ya hau faÉ—in
"Wato saboda tona min asiri roƙo kika je kika yi don ki zubar mini da mutunci ko Sadiya, to da na ce ki yi sana'a ai ba sanar kayan ruwa za ki yi ba don babu wani ƙato da zii shigo min gida sayen wani abu" Yadda yake rada jijiyoyin wuya kamar dai ba shi ne ya gama samun buƙatarsa yanzu daga gareta ba. Kamar za ta yi kuka ganin tana farincikin samun mafita amma yana neman daƙilewa saboda cuta, tana sassaita kalamanta ta ce
"Don Allah karka hanani sana,ar nan kuma ai kakata ce ba wai na tona maka asiri ba ne, ta ce za ta siya min ne ganin Baba bai siya min ba sannan na maka alƙawarin babu wani namiji da zai shigo gidan nan sayen abu" Tun da ta faɗa masa take ta karanto sunayen Allah a zuciyarta a kan Allah ya ɗora ta a kansa, maimakon ya ce wani abu sai ya ce sai ya yi shawara, haka ya kwanta ita ma ta kwanta ranta duk babu daɗi tana taraddadin ko zai amince?.
Da safe yana zaune Kalifa ya je wajen ƴar yawo zai taɓa wayar jiki, ai da ya masa wata tsawa take yaron ya kiɗime ya yi wajenta da gudu yana ƙanƙame ta tare da sakin kuka, wani abu ta ji ya soke ta a zuciyarta, ganin Nasir bai san jan yaro a jiki ba bai san nunawa yaro soyayya ko kulawa ba kawai dai ya haifi yaron ne amma babu wani jin ƙai irin na mahaifa a tattare da shi.