Sashe 43
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tsaye ya yi a wajen yana riƙe da ƙugu ya rasa mai yake masa daɗi, ya jima a tsaye yana ta tunani don gano laifin da ya yi, sai daj a rai da rubinsa yana tunani da fatan Allah ya sa kar Meenal ɗin ta ce ta fasa aurensa. Da na sani ne ya lulluɓe shi da ya tuno ko dai don saboda abin da ya yi wa Sadiya ne Meenal ta ji haushi, a take ya ji wani haushin Sadiyar yana ta sakin tsaki a kai-a kai shi bai ma san dalilin da ya saka ya sakarwa Sadiyar fuska a gabansu ba sannan kuma ai ya rasa yaushe na Sadiya ta san cewa wai Meenal za ta zo tun da shi dai a iya saninsa bai faɗa mata ba. Ya fara tunanin ko dai wani makirci ne Sadiyar ta yi a ƙufule ya juya ya dawo, a wajen motarsa ya tsaya ya ɗakko wayarsa a aljihu ya shiga kiran Meenal har ta katse bata ɗauka ba hakan ya sa ya ƙara hawa tamfa, sake kiranta ya yi ta ɗaga yana jin yadda ta hayayyaƙo masa har sai da gabansa ya faɗi, a ransa yana raya anya wannan za a yi abin arziƙi da ita daman yana ganinta shiru -shiru ashe dai a she dai sai kuma wani sashe na zuciyarsa ya ce wataƙila ɓacin rai ne kawai ba wai halinta ba ne.
Haƙuri ya shiga bata sai dai da alama ta yi nisan da jin kira zai mata wuya, sai faɗin ya disga ta a gaban Sadiya take, har tana cewa dama ya kawo ta ne ya nuna mata iyakarta don ta ga Sadiyar ma har wani harararta take tana mata gwalo a fakaice bai gani ba. Haƙuri ya shiga bata yana faɗin zai ɗauki mataki kafin ya ƙarasa ta kashe wayar. Mota ya shiga ya bi bayansu zuwa gidansu, ko da ya je dakyar suka saurare shi ita da ƙawarta sai dai a ƙarshe ta nuna ita ba za ta zauna da kishiya ba sai dai ya zaɓa ko ita ko Sadiya!.
Nan ya shiga faɗa mata shi da a ce don ta shi ne da tuni ya daɗe da tsinke igiyar aurensa da Sadiya, don dai ita ce da ƙwawa sannan da a ce tana da zuciya da tuni abubuwan da yake mata ma ta nemi sakin auren ko da kuwa a kotu ne!. Ita dai ta nuna babu ruwanta yanzu zaɓi ya rage gare shi, tana gama faɗar hakan sula shige gidannsula barshi ita da Huzaifa. Ko da ya jima yana tunanin mafita a ƙarshe ya juya ya shiga mota ko gidan Hajiya bai je ba bare ya shawarce ta don ya san ƙarshen aleewa ƙasa ne, kuma dai ko ya shawarce ta ko dai ya ranke hukunci da kansa to tabbas ba wani abu za ta ce ba tun da ya san ita ma dai daga ita har ƴan uwansa ba ƙaunar Sadiya suke ba.
Sadiya tana haɗawa Kalifa kunu wanda ta dama masa take zuba madara don yanzu madara ma ƴar aune take siya kwata sai take musu amfani da ita, don sana'ar ta ta rufa mata asiri sosai, ana cikin hakan ta ji tsayuwar motarsa da yake ɗazu bai rufe ƙofar gidan ba shi ma yaron da ya fita bai rufe ba, don haka shigowarsa ta ji kamar an jefo shi. Sai da ya shigo ya tuna dole ya yi takatsan tsan don kar ta gane manufarsa. Fuskarsa ya gyara tare da saita yayinsa yana ƙirƙirar murmushin yaƙeyana shigowa ya zauna ya ce
"Sadiya manyan ƙasa ni kam ya aka yi kika san Meenal za ta zo ko in ce yaushe na faɗa miki da dare za su zo?" Ya faɗa a zahiri bai nuna komai ba amma a baɗini kamar ya wanke ta da mari don ta rusa masa komai, bata san cewa zaman alaƙaƙai yake da ita ba.
ÆŠan murmusawa ta yi sai kuma cike da kissa irin ta mata ta ce
"Ayya Abban Kalifa dama na yj hakan ne don kar su É—auka baka sanar da zuwansu ba, na yi haka ne don in wanke ka" Jim ya É—an yi sai kuma ya ce
"Amma kin yi dogon tunani gaskiya irinku basu da yawa a cikin mata" Tana ba Kalifa kunun ta yi dariya ba tare da ta ce komai ba amma da a farko ta ji faÉ—uwar gaba gudun kar dai laifi ne hakan. Ya jima bai ce komai ba sai Æ´ar magana da yake kiran Kalifa da ita sai kuma ya ce
"Abin nan da kika yi kin birgeni shi ya sa na ce ki tashi mu je gidan Baba mu gaishe da su" Da sauri ta ɗago fuskarta tana bayyana tsantsar mamaki, don abu ne da bai taɓa faruwa ba wai a ce ya je gaishe da iyayenta daɗin daɗawar ma har da ita. Cike da zumuɗi bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba tana cewa Kalifa sai mun dawo ka sha kunun. Shi kuwa Nasir yana mata kallon baki da hankal.
Hijabi ta saka dogo har ƙasa ta ɗauki Kalifa tana cewa gidan Baba za su je, saboda kissa har da buɗe mata mota, a take ta fara jin lallai addua,arta ta fara karɓuwa ta samun ƴanci a gidan miji!. A ƙofar gidan su ya yi parking tana ta washe baki ya ce
"Ki min sallama da Baban idan yana nan sai na gaishe da su" Ranta fari ƙal tana jin kanta ita ma kamar kowace mace, yau dai ta zo gidansu cikin kwanciyar hankali ba za a kore ta ba ko a kyare ta cewar ta koma tun da yau mai kankat aka yi wato har da mijin. Da sallama ya shiga gidan, kowa yana hada-hadarsa Baba yana zaune a kan dutsi yana alwalar magriba don wasu masallatan sun fara kira. Yana ganinta ya dangwarar da butar ya ce
"Sadiya wace jarabar ce ta kawo ki gida da gabannin magribar wannan? " Ya faɗa don tunaninsa laifi ta yi suka yi faɗa ko kuma ƙara ta kawo da sauri ta ce
"Baba tare da Abban Kalifan muke shi ya kawo mu a mota yana waje ya ce ka je ku gaisa" Wani irin washe baki Baba ya yi tuni ya tashi yana saɓa babbar rigarsa tare da gyara zaman hularsa matan gida da aka fara ƙusƙus jin abin da Sadiyar ta faɗa, Baba a zaure har tuntuɓe ya yi da wani dutse yana jin kansa wai yau shi ne sirikinsa ya zo har ƙofar gidansa gaishe da shi kuma a motar da akam ce sabuwa ce ma, ya san yau kam Nasir zai masa sha tara ta arziƙi, sai dai kash!. Yana fitowa bai ga komai ba sai sawun motar Nasir don tuni ya cikawa rigarsa iska!.