← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 106

Sashe 102

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan ƴar tsakuwar kazar fa? Haba Babban yaro kamar wanda dai baka sona ka da za ka samo ƙosasshiya" Ta karɓa tana murɗe cinyar kazar duka biyu ta cire su tana ɗagawa tana nuna masa, ta ce wallaho sai ya canjo kazar in ba haka ba ita a gado za ta kwana shi a ta saka masa katifa a ƙasa tun da bai kawo kazar amarci ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga lallaɓa ta don ba zai yarsa ranar yau ta wuce bai yi sunna ba saboda yau ma tana cikin lissafinsa don ya fara sakawa a ransa ma a yau za a aamu ƙaruwa.

Haka ya buɗe ƙofa ya fito da ledar kazar yana jin takaici ya rasa ma mai ya sa ita ko ɗan kawaicin nan ma na amare ba ta da shi, haka ya fito yana jin haushi, lokacin Mama Bilki ta fito daga banɗaki riƙe da buta ta ce

"Malam, Malam, Malam" Sainda ta kira shi sau uku sannan ya juyo, yana amsawa kamar an masa dole ta ce

"Lafiya kake ta zaryar fita daga gida ko siyan bakin ne bai kammalu ba" Ya kalle ta yana jin kamar ya wanka mata mari ya huce takaicin amaryar a kanta ya ce

"A,a siyan ƙafa ne bai ƙare ba, ba na baki ba, na ce siyan kai da ƙafa ake" Ta yanayin furucinsa ta gane a ƙufule yake ta ce

"Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Wani tsaki ya ja yana juyawa ta sake cewa
."Ango ka taho min da maganin gudawa ka ganni tun daɗewa nake zarya banɗaki kamar angon da amarya take aike" Banza ya mata ya juya ya tafi tana jin lokacin da ya banko ƙofar gidan ta sheƙe da dariya a zuciyarta tana faɗin

'KaÉ—an ma ka gani" Don ta fahimci akwai wani abun da yake faruwa duk da ba ta san mene ne ba, amma in tusa tana hura wuta za a gani.

Haka ya sake daɓawa a ƙafa domin dama a ƙafa ya je ɗazu saboda mammaƙon kuɗinsa ba zai hau mashin ba, ga shi kuma da ɗan tazara, ko da ya je mai kaza ya ce wallahi ba zai karɓi kazar da aka jawalwala ba tun da ya ga gabaɗaya ma cinyoyinta da ban suke ba sa jikinta. Kamar zai yi kuka haka ya cire naira dubu sha ɗaya ya siya kazar aka haɗa masa da waccan ya kamo hanya har ƙwallar takaici ya share.

Haka amarya ta zage ta ci kaza don ƙaramar nan sai da ta cinye tas, iyaka ta ciro ƴar ƙaramar tsoka ta saka masa a baki ya lamushe saboda ta hana shi ya saka hannunsa wai ba girmansa ba ne tana waje yake ciyar da kansa. Ita kuma sai ta yago ƙatuwar tsoka ta cika bakinta ta kalle shi ta ce

"An ce amarya in ba ta ci kaza ba ma dole a sha manta" Bai tanka mata ba illa dariyar yaƙe da yake. Haka ta ɗaure sairan wai ta ƙwayaenta ce idan sun zo gobe sai su haɗa da lemukan da zai kawo.

Haka Baba ya sha amarcinsa, yana fatan an samu ƙaruwa a ranar. Tun daga ranar yake lallaɓa amarya. Hankalinsa kwacakwam ya koma kan amarya dama shi bai damu da zuwa wajen mahaifiyarsa ba sai ya daɗe bai je ya ganta ba bai san cewa gabaɗaya albarkar rayuwarsa tana dangane da farincikin da ya saka mahaifiyarsa ba

Ranar da amarya ta cika kwana goma sha biyar a ranar ne bayan ta gama cin abinci ta fito tsakar gidan tana kelaya amai, lokacjn Baba shigowarsa kenam ya hange ta, da gudu ya yi wajenta yana zuwa ya faɗi ƙasa daga can gefenta ya yi sujada yana yi wa Allah godiya.Sai da ta gama ya bata ruwa ta wanke baki ya ce

"Sannu uwar maza, Allah raba lafiya kin gama min komai da za ki haifa min namiji" Langwaɓewa ta yi sai shi ya kama ta yana jera mata sannu. Washe gari da zai dawo daga kasuwa sai ga shi ya siyo rigunan jarirai maza guda biyar wai taro za a fara.
Amarya sai tsiyarta take tsulawa a gidan don dama tun da ta zo ba ta yi girki ba sai dai ta zaɓi abin da take so ya siyo mata. Ranar da ta cika kwana uku da yin aman tana kwance a saman doguwar kujera tana danna waya ya shigo ya ce

"Badary nah, tashi mu je za ki rakani" Haka ta yafo mayafi suka fito tare ya kulle ƙofar ɗakin nata yana faɗin da a ce yana da iko da ya hana ta ko da tafiya ce ahi zai ke yi mata tafiyar.

Napep É—in da ya kira suka tarar yana jiransu suka shiga baya ya ja suka fara tafiya kanta ta kwantar a kafaÉ—arsa ta ce

"Wajen shaƙatawa za ka kaini Babban yaro?" Mai napep da sauri ya juyo jin furucinta ya kallesu shi ya ɗauka ƴarsa ce sai ya ji banbarakwai wai namiji da suna hajara ana kiransa da babban yaro.

Baba ya kalli mai adaidaita sahu ya ce

"Sanan,a ka fito ko kallon matan mutane?" Bai tankawa Baban ba ya ƙyale sai Baban ya ce

"Haba Badary nah ina na samu sukunin zuwa wajen shaƙadawa ni fa hankalina yana kan ki nan da abin da za ki haifa ai daga yanzu har zuwa lokacin haihiwarki ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo"

A ƙofar wajen scanning aka ajiye su, Baban ya ce
"Mu shiga"
Ta kalle shi za ta yi magana ya ja hannunta suka shiga sai da layi ya zo kansu Baban ya ce scanning za a mata a gano masa mai za ta haifa, ko da aka tambaya cikin watansa nawa sai Baba ya ce ai ba a yi sati uku ma da auren ba. Nana aka sanar da shi ba yanzu za a gane cewa ga abin da yake cikin ba saboda abin da yake cikin bai gama zama halitta ba har yanzu yana gidan jini.

Ko da aka faÉ—i haka Baba ya ce su tafi suna hanya yana ta mita yana faÉ—in ai dama ya san mai za a haifa namiji sai dai yana son a gani biyu ne ko É—aya ne.

Amarya ta tsiro da rashin mutuncin cewa sai Baba ya aurar da duka ƴaƴansa tun da dai duka mata ne wai kakarta ta taɓa cewa idan mace mai ciki tana kallon abu to abun yana washe ta, wato tun da su mata ne za su washe ta ta haifi ƴa mace. Tun da Baba ya ji wannan batu hankalinsa ya tashi saboda shi kansa ya san ana cewa mace mai ciki ana wasar ta, amma dai bai san cewa gaske ba me ko kuma camfi ne, don haka maganin kar a yi kar a fara.

Haka ya tara gabaɗaya ƴaƴan masa ya ce su fito da miji ya basu sati guda. Kowacce jikinta ya yi sanyi dimin sun san ba su da wani tsayayye babu wani wanda za ka fitar ya aure ka tun da dama ba don aure suke son su ba kawai ana sheƙe aya ne.

Ko da sati ya cika babu wacce ta fito da miji kowacce sai ta ce saurayin bai shirya ba ita kuma amarya abu ya ci tura don har ƙin fitowa tsakar gidan take, kuma ba komai ya sa ta musu haka ba sai Arfat da ta ga tana mata wani kallon raini gabaɗaya ma ƴanmatan gidan suna mata gani-gani. Shi ya sa take so ta nuna musu ta isa da ubansu.
Yau ta kama alhamis Baba ya shigo da dare ya tattara su cike da masifa ya ce

"Na gaji da zamanku a gidan nan na ce ku fitar da miji kun ƙi kun zauna za ku washi Badary ta haifi mace, kun fi so na ƙare a wahale babu mai taimaka mini amma in ta haifa mini namiji ai shikenan na huta, tun ina siyan maganin farin jinin har na gaji saboda kamar ma baƙin jini nake ƙara muku, ku ba muni ba amma a ce gabaɗayanku babi wacce take da mijin aure yau na yanke hukunci kowacce ni zan zaɓa mata miji ba za ku rufa sati a gidan nan ba sai dai a gidan mazajenku"

Yana gama faÉ—ar hakan fuuu ya yi hanyar waje. Washe gari da asuba aka ji sanarwa a masallaci cewa Malam Bala ya ce tun daga kan liman har ladan da sauran dattijan unguwa mai son Æ´aÆ´ansa da aure zai aura masa!.

Matan gidan sun yi takaicin wannan hukunci da Baba ya yanke sai ka ce mai neman kai da ƴaƴan. Babu wanda ya tanka masa don sun san babu wanda zai zo ya ce zai aure su. Amarya sai dariyar ƙeta take tana yada magana a tsakar gida wai gwara dai kowacce ta san na yi kar a saka ta haifi mace.

Da yamma sai ga shi ya zo ya tara su ya ce

"Kowacce ta samu wanda zai aure ta wallahi har raina ya yi fari sai na ji gabaÉ—aya zuciyata kamar an sauke mini dutse zan aurar da ku in huta da wahala" Ya faÉ—a tare da fara lissafo sunayen mutanen da suka sani a unguwar wanda manya ne ciki kuwa har d liman ko da ya zo kan Arfat ya ce

"Arfat ke Ayodele nw ya ce zai aure ki" Cike da mamaki kowa na gidan ya fito wanda suke ɗaki su kuma ƴanmatan sai suka fara kallon kallo, amarya kuma tana ƙofar ɗakinta ta kama tsantsa tana sakin murmushin ƙeta.

Arfat idanunta taf da hawaye ta ce

"Baba Ayodele fa ka ce wane Ayodelen?"

Cike sa masifa ya ce

"Ayodele nawa kika sani a unguwar nan? To Ayodele shugaban coci"
Mama Sa,ade ta ce

"Wallahi babu wanda ya isa ya aurawa Æ´ata arne" Baba cike da nuna isa ya ce
Chapter 102 · 0% Book details