Sashe 64
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai har kiran ya tsinke bai ɗauka ba dama shi ba ma,abocin ɗaukan kiran baƙuwar lamba ba ne. Tun da kiran ya katse ta zurawa wayar idanu tana ta kallin numbersa tamkar dai tana ƙidaya yawan lambobin ne duk da ta san lambobin Nigeri,a basa wuce guda goma sha ɗaya, amma sai ta ji tana tantamar ko dai ba daidai ta kwafi lambar ba, sai dai kuma tun da tana shiga daidai ce wataƙila bai ga damar ɗauka ba ne.
Kiran ta sake yi a karo na biyu, ɗan tsaki ya yi kiran yana shirin tsinkewa ya ɗauka tare da kara wayar a kaunnensa, tana tuƙi a hankali da hannu ɗayan. Sallama ya yi da kyakkyawar muryarsa mai sanyi da ratsa dodon kunnen mai sauraro musamman Aliya da take jin ta yi kewarsa tamkar wanda ta shekara bata ji muryarsa ba, domin ta saba ko da wucewa za ta yi ta ji muryarsa yana magana da Jidda, ita bata ma ƙara sanin zuciyarta ta damu da Ibrahim ba sai da ta yi nesa da shi, tabbas tana son abu guda biyu daga gare shi wanda au ne suka kai zuxiyarta ga wannan ɓigiren. Abu na farko dai dukiyarsa ita ce a farko sannan kuma sai son sa da take yi tana jin ko za a raba ta da numfashinta sai ta auri Ibrahim sai dai Jidda ta yi gawa!.
Jin muryarsa ya sa ta lumshe idanu tana jin muryar har ƙoƙon ranta, ji take dama ya yi ta magana tana sauraronsa. Shi kuma jin ba a amsa sallamar ba sai ransa ya ɓaci ya tsani a kira shi a waya kuma a yi shiru. Ita kuma ta sha,afa ma da cewar ita za ta amsa sallamar da ya yi. Ɗan gyaran murya ta yi ta amsa da wata murya da babu wanda zai gane muryarta ce.
Tana tunanin abin faÉ—i ta ji ya ce
"Wa ke magana?"
Sai lokacin ta fara tunanin faÉ—in
"Sunana Surayya dama na samu numberka ne a wayar yayana ina so za muke gaisawa" Da mamaki ya ce
"What?"
Wani yawu ta haÉ—iye jin ya yi magana cikin hargagi. Cike da sassauta murya yadda zai ji tausayinta ta ce
"Idan hakan laifi ne Allah ya baka haƙuri na yi kuskure" Ta faɗa tana jiran jin ko zai sassauto, shi kuma ba tare sa ya san wane abokin nasa ba kawai sai ta jo ya yanke kiran. Lokacin ta ƙaraso saitin gidansa ya shiga yin horn mai gadi ya buɗe masa.
Hancin motar ya danna a cikin get ɗin kafin ya ƙarasa parking space ya ajiye motar ya fito yana riƙe da ledar da ya siyo mata ice cream da wayoyinsa ya nufi ciki. Ko da ya shigo falon bata nan sai karatun qur,ani da yake tashi a wayarta sai kuma ƙamshin turare, duk ɗakunan ya duba bai ganta ba, sai kuma ya haura sama yana zuwa ya tura ƙofar ɗakinsa a can ya same ta bayan ya shiga da sallama ta amsa masa cike da fara,a tana takowa gabansa bayan ta ajiye filon hannunta da take sauya masa riga dama bedsheet ta zo canjawa a gadon.
Kallonta yake yana murmushi wanda ita ma murmushin take, hannunsa ya saƙalo a ƙugunta bayan ta karɓi ledar hannunsa, bakinn gadon suka ƙarasa ya zauna tare da ajiye wayoyinsa sannan ya zaunar da ita a kan ƙafafunsa yana lakato hancinta ya ce
"Sarkin aiki wato kece agogo sarkin aiki ko Jiddana" Ya faÉ—a yana haÉ—a hannayenta waje guda.
Tana Æ´ar dariya ta ce
"Ni babu wani aiki fa" Ya ce
"Wannan mene ne kike yi?" Ta kalli gadon da ya nuna mata tana ganin yadda ta ɗame gadon tamkar wanda ko an zauna shimfiɗar ba za ta ɓaci ba, a taƙaice ba za ma ka ce hannu ne ya yi shimfiɗar ba.
ÆŠan murmushi ta yi ta ce
"Ni fa ba na jin daɗi in zauna ba na yinw wani abu, sai ma in ke jin duk jikina babu daɗi na saba in yi aiki" Hannunsa ya kai ya haɗa leɓɓan nata waje guda ya riƙe don kar ya bata damar magana ya ce
"Nan gidan hutunki ne Jidda ba a so ki wahala ba a so ki yi komai, ni zama a cikin gidana ma da aurena da kika yi Jidda wallahi sai in ke ganin kamar alfarma kika min, kin min komai a rayuwa Jidda da kika auren wani lokacin sai innke rasa da mai zan saka miki?" Duk da bakin nata da ya rufe hakan bai hana aka ji sautin dariyar da take yi ba. Bai sakar mata bakin ba ya ce
"Kin gama min komai a rayuwa, ni kuma zan yi iya yi na don na faranta miki da kuma yaƙi da duk wanda zai baƙanta miki.. Ƙaran wayarsa ne ya katse musu magana, bai kalli wayar ba har kiran ya katse hankalinsa yana kan Jidda. Sai da wani kiran ya shigo yana waiwayawa ya ga Mummy bakin Jiddan ya saki ya ɗakko wayar ya kara a kunne tun kafin ya yi magana Mummy ta ce
"Ina Æ´ata?" Dariya ya fashe da ita sosai ya ce
"Wai Mummy ni É—in yayeni kika yi, wai kawai yanzu in kika kira waya sai ki ce ina Æ´arki gaskiya ina kishi" Ya faÉ—a lokacin da ya saka handsfree Jidda da take musu dariya ta cigaba da sauraron abin da Mummy take cewa
"Ni ai yanzu babu ruwana da kai na yi ƴa ka san idan aka yi sabon sarki mai za a yi da murabus" Baki ya zumɓura jin rana batun ya ba Jidda wayar. Miƙa mata ya yi bayan ya sakar mata hannu, tana kara wayar ta shiga gaishe da Mummy cike da girmamawa tana ɗan rusuna kai, Mummy ta amsa tana tambayarta ina wayarta sau biyu ta kira ba a ɗauka ba nan ta sanar mata ta bsr wayar a falon ƙasa.
Mummy ta shiga faɗa mata ta kira ta ne don ta ji lafiyarta, inda har lokacin bakin Ibrahim a zumɓure kamar bakin jaɓa shi a dole fushi ya yi an daina sonsa sai Jidda kaɗai. Da gayya ya saka hannu ya yi wa Jidda cakulkuli a cikinta inda dariya ta so ƙwace mata ita kuma take yaƙi da dariyar don kar ta yi Mummy ta ji.
Suna yin sallama Mummy ta kashe tana batun gobe masu aiki za su zo. Tana kashe wayar ta shiga asa kalamai tana lallaɓa shi da yaƙi lallashin ta shiga masa gwalo tana tsokanarsa suka shiga kewaya ɗakin yana binta zai kamo ta, wai sai ya ga mai ƙwatarta a daren yau. Sun daɗe suna wasan cike da soyayya kafin ta ɗakko ledar ice cream ɗin ta sakko ƙasa za ta saka a frige ɗin ƙasa.
Tana tsaye gaban frige ya sakko hannunsa da wayoyi ya ce
"Sai ki bar waya take ta yi, bayan ke bakya falon bare a ce sauraron karatub kike" Sai da ta kashe karatun bayan ta rufe frige É—in, gudun kar suke magana karatun yana yi sannan ta ce
"Ai karatu ba sai mutum yana waje ba, a haka ma zai ke kore shaiÉ—anu" Yana shirin bata amsa wayarsa É—aya ta shiga ruri yana dubawa ya ga wannan number ta É—azu wani tsaki ya doka ba tare da ya É—auki wayar ba har kiran ya katse, ita kuma Jidda ko a jikinta don ita a tsarinta babu ruwanta da uzurin miji ko saka masa ido a lamuransa.
Aliya kuma tun lokacin da ya kashe sai da ta ji kamar ta yi kuka, a ranta tana raya cewa wataƙila yana tare da wannan baƙar mummunar matar tasa wacce take saka rai nan gaba kaɗan za ta maida rayuwarta a gidan ta zama tarihi ita kuma ta zama mamallakiyar gidan da mai gidan, idan ma bata jera da ita zaman kishin ba don ta gasa mata aya a hannu sannan ta mata gashin ƙuma wanda da ƙafafunta za ta bar gidan, fatan ta dai kar rabo ya shiga tsakanin Jidda da Ibrahim din ta fi so ita kaɗai ce za ta haifa masa ƴaƴa yadda za su ci gadon dukiya a daidai!.
Ko da ta ɗauki lokaci ma jira take a jima ne ta ƙara kiransa sai dai kuma rashin sa'ar da ta yi ya sa ranta ya ɓaci na ƙin ɗaga kiran da ya yi, sai dai ta yi alƙawarin da sannu zai dawo tafin hannunta ta yadda wurin zama ma sai an nuna masa zai zauna.
Washe gari ta sake gwada sa,arta amma sai bai ɗauka ba, hakan ya sa ta yanke hukuncin buɗe whatsapp ɗin da ta buɗe da sabuwar lambar ta rattaba masa sallama, da kuma gaisuwa tana masa fatan alkairi cikin kalamai na jan hankali, sai dai wuni guda curr bai mata replay ba ita kuma daga an ɗauki ƴan mintina sai ta tura mata hoton emoji na yatsa manuniya alamar tana masa nuni da saƙon da ta tura masa, ta tura masa yatsa ya fi sau goma amma Ibrahim bai mata replay ba kuma tana ganinsa online don saƙon ma ya yi tik biyu alamar an isar masa buɗewa ne kawai bai yi ba.
Ganin haka sai ta yi wa Jidda magana da sabuwar lambar ta whatsapp ta farfaɗa mata maganganu baƙaƙe.
Bayan wata guda ta rasa mafita hakan ya sa suka yi shawara da ita da Amatullahi, ai kuwa Amatullahi ta ce
"Rabu da ɗan iska in laila ta ƙiya sai a koma caca, mu zai yi wa tashin balagar tsintsaye wallahi ya yi kaɗan sai kina mallake shi ƙawata" Amatullahi ta faɗa tana nuna mata daga sun samu kan Naair sai ta kashe aurenta, ita kuma Aliya daɗin shawarar ta ji bata san cewa Amatullahi tana baƙin cikin Aliya ta yi aure ta barta tana gararamba a layi ba, so take ta kashe auren ta zama bazawara su dawo suke yawo a layin tare domin a hankalce ta san Ibrahim ba zai aure ta ba.