← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 106

Sashe 9

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kowane ɗan adam yana da jarawarsa a rayuwa, sai dai idan ya jure watarana komai zai zama labari, komai zai zama tarihi tamkar ba a taɓa yi ba" Ta faɗa yana ruƙo hannun Mubin ta dawo da shi kusa da ita ya zamana suna zaune a tare Mamy a tsakiya su kuma kowa yana gefenta hannuwanta ta sanya ta dafo kafaɗunsu ta ce

"Ku zama masu jajircewa, ku zama masu riƙe ibada tare da jajircewa a dukkan lamuran rayuwarku, kar ku bari wani abu yale rage muku jin daɗin rayuwa, duk wanda ya riƙe Allah to tabbas ba zai yi nadama ko da na sani ba" Ta faɗa tana juyawa ɓangare Zalika ta kalle ta, ta sake juyawa ɓangare Mubin ta kalle shi, su duka har lokacin da ruwan hawaye a saman fuskar kowa.

Zalika ce ta ce

"Mamy wallahi wani lokacin sai inmke ganin kamar ba Baffa ba ne ya haife mu, to ko yana da wata matar a wani waje da wasu ƴaƴan shi ya sa su yake musu walwala mu yake ƙume mana fuska?"

Kafin Mamy ta yi magana Mubin ya yi karaf ya ce

"Ko dariya ba ya yi, sai fushi da hantararmu kamar dai ba ya son mu, ai na san idan mu kaÉ—ai ne Æ´aÆ´an nasa to zai so shi ma yake zaunawa da mu ko ya bamu kulawa"

Mamy ta ce

"Sau nawa zan faɗa muku ku yi haƙuri ne wai? Na ce muku akwai lokaci yana tafe wataranan mahaifinku zai zama kamar kowane mahaifi"

Zalika ta ce

"Allah ya sa amma dai ina ga sai bayan mun bar wannan duniyar don Baffa ba na jin akwai ranar da zai sauya, ko ya canja ra'ayi.

Mamy ce cike da harzuƙa ta ce

"Wai ya kuke so in yi ne?"

Mubin ya ce

" Mamy mun san kin yi ƙoƙari kuma kina kan yi amma dai ni na san tarbiyya ba ta uwa kaɗai ba ce. Uba yana da rawar gani mai girma a kan iyalansa idan ya nuna ƙauna da kulawa, ya saurari yaransa, zai fi sa su girma da kwanciyar hankali da ƙima, dan aka bar uwa ita kaɗai, yara za su rasa ginshikin ɓangaren uba amma ki yi haƙuri" Mubin ya faɗa yana saka hannu ya ɗauke hannun Mamy daga kafaɗarsa ya miƙewa ba tare da ya ce uffan ba ya bar falon.

*JIDDA*

Gabaɗaya jikinta karkarwa ya fara ganin Umma ta ɗaga hannu za ta sharara mata mari, saboda ta san zafin hannun Umma idan har ta mare ka sai ka gwammace kiɗa da karatu. Domin tana da zafin hannu don hannun ta tamkar hannun wani namiji babu laushi ko kaɗan . Karkarwar da jikinta ya fara kwandon yana neman suɓucewa, Umma wacce sai da hannunta ya kusa isa fuskar Jidda sannan ta hangi Abba ya taho daga hanyar ƙofar gida don alamar farin yadin jikinshi ta hango, sosai faɗuwar gaba ta ziyarce ta amma saboda kissa da kisisina da iya bariki irin na Umma a take ta shiga kokawa da ƙwaƙwalwarta, don ganin ta ƙirƙiri abin da zai gusar da wannan mugun ganin da Abban ya kusa yi.

Cike da tsantsar baki ta saki wata ƴar bazawarar dariya, hannun nan da ta yi niyyar marin Jidda da shi sai ta ƙarasa gefen fuskar Jiddar a hankali ta shafi kuncin Jidda ɗata hannun kuma sai ta riƙe haɓar Jiddar tana cewa

"Allah ya miki albarka Jidda ya baki miji na gari inda za ki huta, ubangiji ya baki ƴaƴa masu miki ɗawainiya kamar yadda kike mini, Allah jiƙan itayenki da rahma" Wannan kalaman na Umma ne ya sa Jidda wacce ta rikice take jiran saukar zazzafan marin na Umma da sauri ta buɗe idanunta tun daga lokacin da ta ji Umma ta shafa fuskarta haɗe da haɓarta amma jin kalaman na Ummar ya ankarar da ita akwai abin da yake faruwa.

Wani yawu Jidda ta haɗiye muƙut, ganin fuskarta ta tsira daga mari, Abba kuwa wanda ya yi mutuwar tsaye da ganin ɗaga hannun Umma mamaki da al'ajabi suka saukar masa ya fara tunanin mene ne halan yake shirin faruwa, sai dai lokacin guda Umma ta sauya masa akalar tunaninsa daga mummunan zaton da ya fara mata zuwa kyakkyawan zato da yake mata a kullum domin kyawawan halayenta da take nunawa a gabansa da kuma rashin nuna bambanci tsakanin Jidda yarinyar da yake riƙo da kuma ƴarta ta cikin ta wato Aliya.

Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauka tare da fata ɗaga sagaggun ƙafafunsa don tun lokacin, da ya ga Umma ta ɗaga hannu ta nufi fuskar Jidda ya ji komai ya tsaya masa cak!.

Baki ya buɗe cike da raha ya yi sallama, a lokacin Umma ta riƙe da gefen kaɗar Jidda, Jidda kuwa sai a lokacin ta gane dalilin da ya sa Umma ta fada aiwatar da ƙudurinta a kanta, yanzu ta fahimci ashe zuwan Abba ne ya dakar da Ummar daga marinta.

Umma kuma cike da nuna bata san da zaman Mai gidan nata a inda yake ba, ta juya da sauri tana ƙara faɗaɗa fara'arta ta shiga amsa masa sallama, tare da ɗauke hannu daga saman kafaɗar Jidda da ta riƙe tana mai cewa

"Maza an Jiddona a je a kai kanukan kicin" Cike da ƙarfin hali Jidda ta amsa mata da faɗin

"To" Tana nufar kicin don har lokacin bata dawo daga duniyar tsoro da fargabar marin da Umma ta yi niyyar mata ba. Umma tana sakin Jiddar ta juya da fara'arta ta irin mutanen kirki masu dattako ta nufi Abba tana ta karɓi ledojin hannunsa tana faɗin

"Sannu da zuwa sannu da zuwa, sannu da zuwa jan gwarzo, uba na gari ga ƴaƴansa miji na gari ga matarsa, Allah bada tsawon rai da kwana mai amfani, an dawo daga hidima da ƙoƙarin nemawa iyali abinci da za su ci, Allah yi jagora ya sauƙaƙa maka hanyar nema" Ta ringa jero addu'ar tana gaba yana biye da ita yana ta amsawa da

"Amin ya rabbil alamin" Ɗakinsa ya shiga, sai da ya zauna a bakin gado ta ƙara masa sannu da zuwa sannan ta fito da ledojin ta damƙawa Jidda a kan cewa komai a ajiye shi a mazauninsa, fruit ɗin kuma ta yanka. Ruwa ta kaiwa Abba banɗakinsa na ɗaki sai da ya shiga wankan ta fito, suna haɗa ido da jidda wacce take zaune da kayan fruit a gaba tana saka su a wata roba mai ruwa tana wankewa, wata gagarumar harara ta jefawa Jidda kamar idanunta za su faɗo, da sauri Jidda ta kawar da idanunta ta maida hankali ga abin da take yi. Umma wani tsaki ta doka har guda biyu tare da juyawa ta shiga kicin ɗin kayan abincin Abba ta ɗakko ta ajiye a waje guda.

Abba sai da ya yi alwala ya fito daga banɗakin jallabiya ya saka ya fesa turare ya ɗakko carbinsa ya fito, lokacin ana ta kira magriba, Jidda lokacin ta gama zubawa Abba kayan fruit ɗinsa a plate ta rufe ta ajiye a kusa da abincinsa da Umma ta ajiye, sai kuma na Ummar a wani plate ɗin sai nasu ita da Aliya a plate ɗaya, ta san wannan ƙa'ida ce in dai Abba yana nan tare suke cin abu.

Umma da ta gama alwala ta buÉ—e baki ta ce

"Jidda maza ki ajiye wannan kayan ki yi alwala ki yi salla, Æ´ar uwat taki ma ki musu magana su fito an kira sallah" Da to ta amsa ta shiga É—aki za ta É—akko abin sallah.

Abba ya ce

"Jidda sarkin aiki" Ya faÉ—a cike da kulawa yana Æ´ar dariya. Murmushi ta yi ta ce

"Ina jin daÉ—in in ga ina aiki" Murmushi ya yi ya ce

"To ai sai a je a gaishe da ubangiji kin dai ji abin da Ummarku ta ce" Da to ta amsa masa tana jin wani farin ciki don Abba shi kaɗai ne mai ƙaunarta tana jin daɗin yadda yake ƙaunarta. Yana fita sai ga Aliya da Amatullahi sun fito kallo ɗaya suka yi wa Jidda da take shimfiɗa tabarmi a tsakar gidan, tun da ita tana fashin sallah, waje suka fita Aliya za ta takawa Amatullahi, a ƙofar gidan suka yj sallama don ta san Abba ya dawo dama magana ce a kan saurayin da ta gani kyakkyawa tana cewa burinta ya zo gare ta ya bayyana kalmar so a gare ta ita kuwa dole ta yi watsi da Kasim saurayinta da yake mata wahala duk da bashi da wani ƙarfi sai don ƙaunar da yake mata kuma yana son ya faranta mata ganin tana son a bata.

Aliya sallah ta yi haka ma Umma suka zauna, Jidda tana ɗaki gudun kar a mata wani abun. Abba sai da aka yi sallar isha'i ya shigo gidan, yana shigowa da sallama vayan an amsa ya nufi tabarmarsa ya zauna, Aliya ta masa sannu da zuwa Umma ta shiga ƙwalawa Jidda kira tana faɗin mai take a ɗakin. Jidda tana fitowa ta je ta durƙusa ta gaishe da Abba tare da masa sannu da dawowa. Ya amsa cikin fara'a yana musu addu'a

Abincin da Aliya ta zubo musu a plate É—aya suka shiga ci, Aliya tana wani jan Jidda da hirar tana ta Æ´ar dariya, haka ma Jiddar ta É—an saki jiki duk da ta san kawai na ganin Abba ne. Sai da suka gama suka shiga shan fruit É—in. Bayan kowa ya gama aka shiga hira tamkar dai babu Æ´ar tsama tsakanin Jidda da Umma da Aliya. Abba yana ta musu murnar kammala jarabawa da gama makarantar buÉ—ar bakin Umma sai ta ce

"An kammala karatu kam sai shafa lalle" Ta faÉ—a tana Æ´ar dariya tare da fakar idanun Abba ta yi wa Jidda wani kallo irin na za mu ga da wanda za a É—aura miki aure.

Abba gyaran murya ya yi ya ce

"Tabbas dama wannan ne burina duk wacce take son É—ora karatu sai dai ta É—ora a É—akin mijin ta" Jidda gabaÉ—aya ta ji hankalin ta ya tashi saboda ta san Abba bashi da burin da ya wuce ya aurar da su rana É—aya da ita da Aliya, gashi ita ko tsayayyan saurayi bata da shi bare kuma a yi zancen aure.
Chapter 9 · 0% Book details