← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 106

Sashe 83

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wnanan maganin ne na sakawa a hanci, wannan kuma daga kin shiga gidan makokin sai ki ambaci sunan mamacin tare da fakar idanun mutane ki juye garin maganin a hannunki sai ki hura da baki ta yadda maganin zai bi iska kuma ko wani ya gani ba zai tambaya ba, kina yin haka kowa zai faɗi sumamme har ki je ki gama abin da za ki yi idan kin gama sai ki ƙara ambaton sunan mamacin kowa zai tashi kuma kowa ba zai taɓa sanin ya suma ba"

Sun karɓo sun taho Umma tana ta adana maganin, don Bokanya ta ce a tsakanin su kowa zai iya yin aikin tun da an yi maganin da sunan waɗanda ake so aikin ya ci, don haka sai Umma ta ce za ta yi ita kuma Aliya dama ta ce tsoro take ji. Aliya gida ta wuce, Umma ma ta wuce gidan don Abba bai dawo daga kasuwa ba.

Umma ta je ta ɓoye maganin a wata sabuwar samirar ta, tana zaune da magriba bayan ta idar da sallah, tana jingine da bango Abba yana masallaci lokacin sai kawai daga masallaci ta ji ana sanarwa ana cewa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un Allah ya yi wa malam kalla rasuwa, za a yi sutura da ƙarfe bakwai na safe, Allah jiƙansa ya gafarta masa" Zuruf Umma ta miƙe tsaye gabanta yana faɗuwa, don ta san lokacin aiwatar da aikinta ya yi duk da tana da mugun tsoron gawa, amma haka za ta durfafi wannn al,amari saboda malam kalla maƙocinsu ne daga can gefe!.

SADIYA

Da tsananin mamaki ta ɗago tana kallon Meenal wacce take tsaye hankali kwance take zaro baƙar magana, ta rasa mai ta tsare mata a gidan bayan ita ta zo ta samu a gidan amma tana son fitar da ita daga gidan mijinta ta ƙarfi da yaji!.

Meenal ta ƙara haɗe rai haɗe da yatsina fuska ta ce
"Ina fatan kin fahimta, ko kina kokwanto a kan hakan ne in nuna miki zahiran" Ta faɗa tana kama ƙugu da hannu ɗaya, Sadiya danne takaicin da yake ranta ta yi ta ce

"A kan mai zan yi mamaki ai shi mutum ba a gane shi a fuska sai dai ɗan adam bai isa ya zartar da abu a kan mutum ba sai abin da Allah ya rubuta a kansa, idan har ruwana ya ƙare a gidan nan dole zan bar gidan idan ruwan shana bai ƙare ba kuwa babu wanda ya isa ya dakatar da hakan" Ido ɗaya ta kanne tana bin Sadiya da kallo kawai sai ta juya tare da yin ƙwafa ta shige ɗaki.

Zuwa jimawa aka fara sallama, bayan an amsa masa ya sanar da cewa mai yin kicin ne da mai gidan ya kira, Sadiya dai ta masa iso ta ja ɗanta suka shige ɗaki. Nasir kuma yana fita da ya je ya gidan Hajiya ya same tw zaune ta duka uban tagumi duk ta yu baƙi ya rasa ma mene ne ummul aba,isin hakan ya zauna bayan ya gaishe ta ta amsa tana sakin doguwar hamma ta ce

"Nasir yanzu sai da na maka waya shi ne za ka zo? Yanzu sai ka kwana ka tashi baka ma zo inda muke ba Nasir?" Ɗan sosa ƙeya ya yi ya ce

"Wllahi Hajiya abubuwan ne suka sha kaina amma baki da lafiya ko" Ta ɗan kai hannu ta taɓa wuyanta da ya yi ƙashi ta ce

"Amma da duk abubuwan da suka maka yawa duk safiyar Allah sai ka zo gidan nan, kuma da kake maganar ko ina lafiya ai yunwa ita ce babbar rashin lafiya" ,Da mamaki ya ce
"Rashin lafiya kuma? Yunwar ce rashin lafiyar hajiya bakwa cin abinci ne" ,Ya faÉ—a lokacin da ya ga Hibba da Husna ma sun fito sun zaune su É—in ma duk sun yi rama.

Hajiya ta ce

"Yanzu Nasir har sai wani ya faɗa maka ba ma girki ai ba girki ne ba ma yi ba ƙoshi ne kawai ba ma yi, yanzu a ce yaran nan su je su yi bautar girkwa yarinyar nan Meenal abincin kari amma take tsakura mana wani ɗan mitsitsi kamar wanda muka roƙa yanzu saboda isa ma wai hatta madara da milon ta daina tsakura mana sai dai mu sha lipton kawai kp yau da suka kawo sai haƙura na yi na sha koko haba a kan mai yarinya ƙarama z ta zama ita take juya ragamar gidanka Naasir" Iska ya hurar yana kallon yadda su Hibba suke zumɓura baki ya ce

"Haba Hajiya ita fa Meenal gidanta ne su kuma yaran nan su ma idan suka je gidajensu sai su dafa abin da suke so, sannan maganar madara cewa ta yi ta kusa ƙarewa a bari ita take sha idan tana tskurawa ba zai isa ba to kin ga ba sai an saka mata rani ba, sannan maganar rashin zuwana Hajiya da fa abincin safe nake zuwa ci yanzu kuwa kin ga acan gidan ake dafawa... Tun kafin ya kai ƙarsheb maganar Hajiya ta fashe da wani kuka mai kamar jiniyar motar ƴan sanda, ta ce

",Yanzu Nasir ni kake faɗawa wannan maganar? Wato har gorin aure kake wa ƴan uwan naka saboda wanncan matar mai ƙira kamar ta barewa, to ahir ɗinka idan ma ƙarfinka aka fi zan yi maganin abin" ,Tsaye ya miƙe cikin halin ko in kula ya ce

"Ni zan wuce, dama zuwa zan yi in kira me aikin kafinta zai je can gidan ya yi aa Sadiya kicin É—in langa langa saboda Meenal ta ce bata son wannan haÉ—en kicin É—in" ,Ya faÉ—a yana tashi tare da gyara zaman hularsa da yake ji kamar bata zauna ba. Da kallo sula bi shi su duka, don yanzu babu wanna soyaya da kulawar da yake basu kawai tamkar ma hankalinsa ba a kansu yake ba, sannan ita Hajiyar ko ta tsawatar a kan rashin adalcin da ta ji za a yi wa Sadiya na yi mata kicin É—in langa-langa duk da dama abu ne da suka saba na tashin yi mata a adalci da alama Allah en ya fara kawo wacce za ta mata maganinsu.

Yana fita sai da suka ji tashin motarsa sannan Hibba ta ce

"Hajiya Yaya Nasir da tamkar ba ya cikin hayyacinsa wallahi ina jin an fi ƙarfinsa ne wato an masa asiri" Husna ta karɓe maganar da faɗin

"Ai dama daga ganin abin ma a hankalce an sana cewa Yaya ba zai aikata haka ba"

Hajiya ta goge wani hawaye mai zafi ta ce

"Ni wallahi abin nan neman fin ƙarfiba yake domin na kasa gane kai da ƙafar abin nn na yi da na sanin auren nan da ya ƙara sannan ina zargin Meenal da mahaifiyarta a kan komai duk da mahaifiyar tata tana nuna min bata ma san abin da Meenal take yi ba sai ta ce wai ita ba za ta tsawatar mata ba ai ni da ita babu bambamci zan iya tsawatar mata bayan yanzu yarinyar nan ji take kanta ɗaya da ni ta ɗauke ni tamkar sa,arta, wai har ni Hajiya Mariya ce sirija take juyawa sannan har ta bada umarni muka bi ni da ƴaƴana wai ƴaƴana ne suke zuwa suna mata girki kullum da safe sannan ta tsakura mana abincin son ranta, wallahi ko a mafarki ban taɓa tunani ba"

Hibba ta ce

"Hajiya ai wallahi yadda kika san wani tsoronta aka saka mana a rai" Haka suka ci gaba da jajantawa suna tunanin yadda za su samo mafita a shawarar da suka yanke dai zuwa wajen malami ne sai dai babu kuÉ—innzuwan don yanzu kuÉ—in da Nasir yake basu duk ya É—aure bakin aljihunsa sai na annabawa.

Naair yana fita ya bugawa me aikin waya ya sanar da shi su haɗu a gidan nasa, sai ya riga Nasir ɗin zuwa yana dawowa gidan ya nuna masa inda za a yi kicin ɗin haka suka tafi suka siyo komai na aikin mai baro ya kawo langa langa da katakon aka shiga aiki tuƙuru!.
An gama kicin tass mai aikin ya tafi don sai da ya sallame shi ya tafi kasuwa. Bayan ya tafi Meenal ta fito daga É—akinta Sadiya tana jin lokacin da ta je take cewa

"Kai amma kicin ɗin ya yi kyau ji langa langan gar sheƙi yake, amma shi ma me aikin nan da ɗaurin tsantsa yake wato gar wani wajen ɗora kwanuka ya mata to Allah kyauta, din dai dama da irin wannan kicin ɗin ta dace" Sadiya bata ce komai ba ta yi kamar ma bata san mai take cewa ba don ta san tana faɗa ne don ta ji. Ko da aka kawo nepa haka ta ƙure kiɗa a gidan don ta turaw Sadiya haushi kan rashin nepar ita kuma sai ta tishe kunnuwanta kamar ma bata san tana yi ba, domin ko da almajirinta ya zo ɗaukan talla ta ce masa firjin ya samu matsala don haka ta kwashe gabaɗaya kayan cikin ta bashi ta ce ya je ya sadakar kar su lalace!.

Meenal duk wannan abin sa ta yi wa Sadiya bata haƙura ba tun da burinta ta baƙanta mata rai ita kuma Sadiya tun da ta lura Meenal tana cikin mata masu kishin kissa da kisisina sai ta tattara kamarinta ta ajiye a gefe kuma ta saka a ranta duk runtsi za ta saka haƙuri da juriya ta san da cewa watarana sai labari kuma duk abin da ka yi haƙuri to watarana Allah zai maka sakkaya a kansa, domin wanda aka zalunta babu shamakin addu,arsa uabnagiji zai karɓe ta ko da bai yi adsu,a ba za a masa sakkaya wannan kaɗai take sakawa a ranta ta ji salama.
Chapter 83 · 0% Book details