Sashe 61
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Muryar Meenal ce ta katse ta da ta c
"Hajiya ina jinki" Ta faɗa wani gatsal babu sakayawa irin na girmamawar da ta saba tana mata, tana maida kallonta kan Meenal sai ta ga tana riƙe da ƙugu. Hajiya ta sassauta murya ta ce
"Ƴata Meenal" Sai Meenal ta ce
"Ashe dai arziƙi ne ya kawo ki ba tsiya ba ni wallahi na ɗauka maganar dankali ce ta kawo ki har na fara tanadar kalaman da zan mayar da martani, ah to in ce Hajiya an faɗi babu nauyi yanzu a ce a kan dankali ki taso tun daga gida" Ta faɗa tana ƴar dariya kamar a wasa. Abin ya baƙantawa Hajiya rai duk da tana tunanin ba cikin hayyacinta take ba.
Danne zuciya ta yi ta ce
"Ba wannan ya kawo ni ba Meenala" Ta faɗa tana buɗe jakarta ta ɗakko wani ƙullin magani a leda fara da baƙa. Ta ce
"Wannan na farar ledar ki jiƙa a ruwa ki yi wanka, shi kuma na baƙar ledar sai ki sha a shayi" Ta faɗa tana bata amma bata karɓa ba ta jefe mata tamabayr
"Maganin mene ne?" Hajiya sai da ta ɗan waiwaiya gudun kar wata ta taho daga cikin ƙawayen ta ji ta juya tana fuskantar Meenal tana sassauta murya gudun ma kar Sadiya ta musu laɓe ta waje ta ce
"Maganin karayar asiri ne, da alama jifanji aka yi Meenal tun da safe bakya cikin hayyacinki" Wata bazawarar dariya Meenal ta yi ta ce
"A hayyacin wa nake to? Mai ma na yi?"
Hajiya ta ce
"Meenal maganganu karazube kike yi babu taunawa bayan ba haka kike ba duk kin sauya ko ni kina min magana kamar sa,arki, haka su Hibba da suka zo da safe ma kika ƙi ganinsu ina jin ma baki san sun zo ba saboda bakya cikin hayyacinki, dama zama da kishiya sai da takatsantsan babu abin da ba za ta yi ba din ganin ta dusashe haskenki a idanun mutane da na dangin miji, jin an ce kina da ladabi da biyayya da girmama na gaba da ke ta shiga ta fita za ta ɓata miki asali"
Meenal ta É—an lunshe idanu ta buÉ—e ta ce
"Bari ki ji in faɗa miki rasss nake, ke baki san a zamanin da ake ba ne yanzu? Ya za a yi kyakkyawa da ni yarinya ɗanya sharaf ƴar zamani in zauna miji ko uwar miji suna juyani kamar wata waina? Idan ma za ki ɗauke idanunki daga sabgar gidan ɗanki to ki kauda idanunki ki bar mu mu shaƙata mu more amma in kika ce za kike shiga sabgar da ba ruwanki ki yi uwa da makarɓiya wallahi hawan jini fa ciwon zuciya zai kashe ki" Meenal ta faɗa cikin halin ko in kula tana cikin faɗa wayarta ta yi ƙara ta duba ta ga Nasir ne sai da ta shawaɓe fuska alamar shagwaɓa ta kara wayar a kunne tana wani buga ƙafa kaɗan a ƙasa ta ce
"Baby ka je ka zauna ka barni da kewa" Hajiya neman mai Jijjigata take yi don ta tashi daga mafarkin da take don abin ya shallake tunaninta an barta riƙe da ledojin maganin da sai da ta zare naira na gugan naira har naira dubu goma aka bata, duk don a dakatar da rawar kan Meenal a dawo da ita hayyacinta take mata biyayya ya zamana ita take jan ragamar gidan ɗanta amma sai gashi Meenal tana tababtar mata cikin hayyacinta take da alama ma inda kunya take Meenal ko ta wajen bata bi ba.
Daga ɗaya ɓangaren Nasir ya ji wani daɗi da ta masa magana shi dama ba ya son wannan gadarar da take masa hakan ya sa ya washe baki daidai nan Meenal ta danna handsfree Hajiya ta jiyo muryarsa yana faɗin
"An ciko gas ɗin taɓ kuwa amma ya ci kuɗi ko dama tsada yake ko don na daɗe ban saya ba na saba siyan buhun gawayi kuma Sadiya da adani sai ki ga ya daɗe tana amfani da shi" Hajiya jin an ce gas ya ci kuɗi ranta ya ɓaci ta fara tunanin yawan kuɗin kamar a aljihunta aka fitar tana tunanin yanzu idan hsr haka gidan Nasir zai ci gaba da kasancewa a hannun ƴan sari to ya za a yi da auren Hibba da Husna bayan shi ne komai nasu.
Meenal bata amsa masa maganar wancan ba ta ce
"Sweet heart lemukan nan fa ba kala ɗaya za ka siyo ba ka haɗo kaloli, sannan ka ƙaro da mararsa sanyi kamar katan biyar sai a saka a frige saboda baƙi" Da to ya amsa mata sai da ta saci kallon Hajiya da take cike kamar za ta yi bindiga ta sassauta murya ta ce
"Ka taho min da fanadol jikina duk ya É—au zafi saboda aikin da ka kwana kana yi
Shi kuma ya ce
Ai kam jiya na... Kafin Hajiya ta gama jin mai zai ce ta juya har tana haÉ—awa da gudu ta yi hanyar falo....
MAMAN AFRAH
09025576222
[11/19, 6:12 PM] ðŸ˜: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 2ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
*HAJIYA*
Har tana tuntuɓe a ɗan tudun ƙofar da ya raba falo da bedroom sai da ta zo falon ta ja birki kamar wacce aka biyo da gudu ko kuma wacce aka saka tsere. Mutanen falon da kallo suka bita suna tunanin dalilin gudn nata don duk a firgice take, sai da ta ga sun zuba mata ido ta gane ashe dai a guje ta fito. Wani takaici da haushin Meenal ne ya turnuƙe mata zuciya tana ganin ta yaya ma za a yi a ce tana surukarta take maganar kwana da miji, ba ma wannan ma ko da an ɗauke matsayinta na suruka ai tana matsayin uwa a wajenta tun da ƙawar uwarta ce.
Meenal kuma tana ganin abin da ya faru sai ta fara danne dariyarta marar sauti don abin ya bata dariya ta tabbatar duk tijarar hajia matsayinta na uwar miji ba za ta so jin yadda daren farkon É—anta ya kasance ba kuma ma a kan kunnen nata É—anta ne zai ja ragamar bayanin. ÆŠan wayincewa ta yi tana faÉ—a masa ya taho da panadol É—in kafin ta yanke kira a fili tana furta
"Wallahi in dai ni ce mu zuba ni da ku É—an halak ka fasa don wallahi ba zan É—auki rajnin hankali ba sai dai mu yi ta bugawa ni da ku muna fafatawa domin idanuna a buÉ—e suke rasss."
Hajiya ɗan wayuncewa ta yi ta nemi waje daga can ƙaramar kujera ta zauna tana jiran Meenal ɗin ta gama wayar don ta fara tunanin ba hayyacinta take ba har yanzu domin da a hayyacinta take yarinya me kunyar kamar Meenal ba za ta yi magana da mijinta irin wannan a gabanta ba, shi ya sa har yanzu take ƙarfafa cewa bata san ina kanta yake ba.
Abu na gaba tana tsoron ta fita tsakar gidan ta ci karo da abin da aka ɗakko a store ɗin ɗanta gani take zuciyarta bindiga za ta yi, in akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce a ce wani abu da zai taɓa lafiyar kuɗin Nasir ba shi kaɗai ta haifa namiji kuma shi ne nauyin dukkan ɗawainiyarsu idan har ya haɗu da kangararriyar mata ta san shikenan sun shiga uku a yadda ta fara ganin take-taken Meenal in har a zahiri ne daidai take gani ba wai jifanta aka yi ba wato ba asiri ba ne gaskiya babu tantama sun faɗa hannun ƴan sari!.
Meenal tana gama wayar ta zauna ta ɗora waya da dadironta suna ta shan soyayyarsu don tana ƙara tabbatar masa babu rabuwa tsakaninta da duk wani abokin holewarta don ta yi wani aure, babu abin da za a fasa. Zaman da ta yi ta san duk ƙwawar hajia dole ta gaji ta haƙura domin ta san za take ta tunanin bata gama wayar ba.
Hajiya kuma sai jera hamma take don da yanzu a gida ne da ta fara haramar cin abincin rana amma yanzu babu hali bata ma cikin nutsuwa da kwanciyar hankali an barta tana ta tangaririya a titi tun da sanyin safiya tana zuwa wajen malami tare da kashe naira dubu gomar magani bayan gashi shi kansa maganin ba a karɓa ba bare ta saka ran Meenal ɗin za ta yi amfani da shi.
Suna gama wayar sai kiran Mominta ya shigo hakan ya sa ta É—auka cike da farinciki suke waya Momi ta ce
"Ta gaban goshi fatan dai babu matsala" Meenal ta ce
"Momi ki bar batun matsala ko a mafarki ai tun da dai ni ce ƴarki to kin yi bakwana da matsalar damuwar ƴa mace a gidan aurenta don kin san babu wanda zan yarda ya yi awon gaba da ƴancina a gidan miji" Momi ta jinjinawa ƴarta tana ƙara bata ƙarfin gwiwa da jaddada mata kar ta kuskura ta bada fuskar da za a rainata a gidan aure!.
Meenal ta ce