← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 106

Sashe 94

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya tana bedroom tana linke kayan da ya cire a lokacin Meenal ta faɗo falon ko sallama babu ta, Kalifa yana ganin shigowarta ya tashi yana riƙe da alrwar tsinkensa ya kama hanyar bedroom a kiɗime don shi tsoronta yake. Sadiya tana ganinsa ta hau faɗin mene ne hankali tashe don ta yi zaton Nasir ɗin ne ya dawo ya zare masa ido tun da Nasir ɗin ma da ba ya sakar masa fuska tsoronsa yake. Kafin ya bata amsa ya riƙe ta sai ta jiyo muryar Meenal tana faɗin

"Kai ina uwar taka take?" Sadiya ta gane da ita take kuma ta fahimci ita Kalifa ya gani ya gudo amma sai ta ba falon ajiyarta, hakan yansa abin ya ƙonawa Meenal rai ganin ta ƙi fitowa. Murya ta ɗage ta ce

"To baƙar munafuka idan ma wani ƙulle-ƙule kika yj kika shiga tsakanina da shi ki sani na fi ƙarfin zama bora a gidan miji" Jin haka sai Sadiya ta fito tsabar ma ta ƙonawa Meenal rai sai ta fito hannunta riƙe da gajeran wandon Nasir da take linkewa wanda ya cire ta ce

"Shiga tsakani kuma? Kin taɓa gani an shiga tsakanin mace da miji? Kenan ni da ba ya zuwa ɗakina shiga tsakanina kika yi da shi?" Tambayar rainin wayon nan ta ƙara hasala Meenal har ta fara tunanin yaushe Sadiya ta yi baki? Ganin gajeran wandonsa a hannunta ya yi wa Meenal zafi a zuciya, tana ganjn kenan har Sadiya ta fara samun ƴancin taɓa gajeran wandon Nasir bayan tin daga lokacin da ta zo gidan hatta suturarsa ta bar ɗakin nata.

Cike da kashedi ta ce

"Ki sani wannan abin da kika yi tamkar shuka ne a idon makwarwa, kuma ina sanar da ke ni da Nasir nan gani nan bari farar tumfafiya, da sannu zai dawo gareni yadda zai zamana sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai ua yi kallo"

Baki Sadiya ta taɓe ta ce

"Kanki ake ji wai mahaukaci ya faÉ—a rijiya" Tana faÉ—ar hakan ta juya ta shige É—aki, dana a can ta bar Kalifa don bai biyo ta ba, Meenal ganin Sadiya ta barta a faÉ—o wato ta mayat da ita kamar mahaukaciya, hakan ya sa ta ji takaici wata zuciyar tana raya mata cewa kamar ita wannan marar galihun za ta faÉ—awa magana ta tafi ta barta a tsaye a wajen.

Jiki babu ƙwari ta juya fuuuu ta fita suka ci karo da Nasir da shigowarsa gidan kenan ya mata kallon mamakin ganin ta daga ɗakin Sadiya ya ce

"Lafiya dai kika fito daga É—akinta a fusace ni fa ba na son gutsiri tsoma ki kama kankj" Da yatsa ta nuna kanta tana faÉ—in

"Ni kake faɗawa hakan Nasir tabbas na yarda ba a hayyacinka kake ba an fi ƙarfika" ,Bai ce mata uffan ba ya raɓa ta ya shige ɗakin ya barta shanye a wajen, baki ta dantse da haƙori idanunta suna cikowa da ruwan takaici, tana kissima sai ta turbuɗe tauraron Sadiya da ya farw haske a zuciyar Nasir sai ta san yadda ta yi ta ƙwace komai ya dawo hannun ta fiye da baya.

Ko da ta koma ɗakinta dakyar da iya yin sallah tana ta tunanin Alhajin da ya mata alƙawarin kuɗi idan ya tura mata ma ta ina za ta gani ita ba da waya gare ta ba, duk sai ta ji ta raina kanta yau ɗaya rana da Nasir zai kwana ba a ɗakinta ba tana ganin hakan kaɓar gazawarta ne a ce mijinta ya koma hannun matar da take ganin ba ta da aji fa kimar da za ta yi gogayya da ita wajen haɗa miji, duk kuwa da cewar ita Sadiyar ita ce ta fara auren Nasir ɗin.

Sadiya wainar fulawa ya ce mata yana son ya ci haka ta masa ta kawo masa ya ci ya sha shayi mai kauri wanda Sadiyar ta haÉ—a masa da kayan shayinta da take saya.

Ganin yau a ɗakinta yake kuma bata shirya hakan ba duk da ita dama ba ta tsark da ruwan sanyi tun da ta san tsarki da ruwan zafi yana haɗe mace sannan yana hana ciwon sanyi infection samun wurin zama a wajen macen da take amfani da ruwan zafin wajen tsarki. Hakan yana sa mace ta kasance koyaushe a haɗe, saɓanin ruwan sanyj da yake buɗa mace sanann sanyi ya samu wajen zama inda shi kansa sanyi yakan saka mace ta zama a buɗe sannan ko da ta yi amfani da maganin mata ba ta ganin alfanu saboda cutar sanyin.

Yana nan zaune a falon yana danna waya Kalifa yana zaune a wajensa, ta ɗauki pure water ta shiga ɗakin da kofi da cokali ta tsakure dakan ni,ima na maman afrah ta zuba ta haɗa da madara ta ɗaga kofin ta shanye, wata ƴar roba ta ɗauka ta buɗe ta fito da ƙwallon dabino ta ɗauki guda huɗu ta rufe robar ta mayar ta fito daga ɗakin tana riƙe da kofin, kaskon turaren wuta ta ɗauka ta ɗakko gwarwashi ta haɗa kanamfari da ƙwallon dabinon ta je banɗaki ta zuba su a garwashin ta tsugunna. Sosai ta ji ya mayar da ita kamar sabuwar budurwa duk da dama Sadiya mace ce wacce tamkar ba ta haihu ba.

Bayan ya dawo daga masallacin isha,i lokacin Kalifa ya yi bacci, ya tarar ta masa shimfiɗa a falo ta ɗaura masa net, ita kuma tana sanye da wata figigiyar rigar bacci da bai taɓa ganinta da ita ba gabaɗaya rigar ta bi ilahirin jikinta ta manne kallo ɗaya ya mata ya luka duniyar ƙaunar kasancewa da ita.

Sun ƙule a ɗakin yana mata hira ƙasa ƙasa duk sai ta ji abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. A wannan lokacin ne Meenal ta zo ƙofar ɗakin da suka ryfe take bugawa tamkar za ta ɓalla, haka ya taso ya fito sanye da gajeran wando ko singlet babu ransa a matuƙar ɓace domin da kawo masa tsaiko a lamarinsa da Sadiya da yake jin tamkar yau ne ranar farko da zai kasance tare da ita ko don an daɗe ba a haɗu ba.

Ta windown ya tambaye ta ba,asin zuwanta da kiransa, ta ce magana take so ta yi da shi, shi kuma ya ce ba zai samu dama ba sai gobe, haka ta koma ranta yana ƙuna, tana kissma mummunan ƙuduri a zuciyarta.

Sosai ya ji sauyi game da Sadiya don shi kansa ya sani Sadiya ta da ban ce a cikin mata ta fita da ban ko da kuwa mata dubu ya tara!.

Washe gari ko da su Hibba suka zo girkin safe, ranar sun gama tsara yadda za a ke yi su da Hajiya cewa yanzu su daina bari sai abin da Meenal ta ɗauka musu suna zuwa suna zama da yunwa kawai suke ɗaukan dankalin a ɓoye, soai suka ji daɗin shawarar nan tun da suna ganin ai ɗan uwansu ne yake siya ba ita ba, kuma har mahaifiyarsa za a ci.

Lokacin da suka zo sun yi mamakin ganin yayan nasu ya fito daga ɓangaren Sadiya, sannan sai suka ga Meenal tana cika tana batsewa, ko da ta ɗauka musu ɗanyen dankalin ɗaki ta koma hakan ya sa suka samu damar ƙara ɗanyen dankalin a ɓoye suka ƙara fiƙewa suka yayyanka suka shiga kicin. Soyawa suka yi tare da soya wainar ƙwan. Ledar da Hajiya ta bayar Hibba ta fito da ita daga aljihun rigarta suka kwashi dankalin da wainar mai yawa sai ƴar dariya suke a ɓoye suna jin daɗin yau za su ci dankali ya ishe su. Bayan sun gama Husna ta je ƙofar falon Meenal ta ce sun gama ta daɗe kafin ta fito a shelaƙe tana wani taɓe baki tana shan ƙamshi.

Kicin ɗin ta je ta ɗauka musu dankalin ko waina ba ta saka musu ba haka kuma ta ƙi tsakura musu kayan shayin. Fulas ɗin ta kinkima don yau ita kaɗai za ta ci ba ta niyyar ba Nasir tun da ya kwana a ɗakin Sadiya. Sun fito za su tafi lokacin tana dab da hawa barandar ɗakin ta, kamar wanda aka ce ta juya haka ta juya sai kuwa idanunta suka sauka a kan aljihun doguwar rigar Hibba da ya yi tudu, hakan ya sa ta kafa ayar tambaya don ta san ita dai lokacin da suka zo ba ta ga wata alama ba a jikin ta.

Sai dai ba ta taɓa kawowa cewa dankali ba ne ita ta fara tunanin ko a kayan kicin ɗin ta ne suka ɗauki wani abun za su fara mata zari ɗai-ɗai. Murya ta buɗe ta ce

"Ke Hibba ku dakata!".

Cak!. Suka tsaya suna jiran tsamani domin ita Hibba har ta fara Æ´ar karkarwa don dama Æ´an magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Fulas É—in hannunta ta ajiye ta tunkaro su, tana zuwa ta ce

"Mai kika É—auka min a kicin?"

Husna ce ta yi ƙarfin halin yin magana domin ta ga Hibba tana neman bayyana lamarin ta yanayinta.

Husna ta ce

"Ɗaukan abu a kicin kuma sai ka ce wasu ɓarayi"

Meenal ta ce

"Ke Husna dakata!. Kar ki ƙara faɗa min magana garangatsai kamar wata sa,arki ni ba da ke zan yi ba, domin ni ba tsararki ba ce"

Ta faɗa ta miƙa hannu za ta taɓo aljihun Hibba ta matsa gefe tana zare ido.

Ƙiiii Meenal ta janyo rigar Hibba tana saka hannu ta ƙarfi suna kokawa ta taɓo dankali yadda ta ji shi da zafi tana leƙawa ta fito da shi ta buɗe leda sai ga dankali ba kaɗan ba da waina. Idanu ta zaro cike da mamaki ta buɗe murya ta ce

"Ihu ɓarayi, ihu ɓarayi jama,a a zo ga ɓarayi"

Nasir da yake wanka ya yi saurin ɗauro towel jikinsa duk kumfa domin ya ji wannan baƙon al,marin alama ce ta babu lafiya, Meenal ganin Hibba tana ƙoƙarin rufa tabarmar kunya da hauka ne Meenal ta ɗaga hannu ta kifa mata mari, da sauri ta dafe kunci cike da mamakin sa ya sa bakinta ya ƙi rufuwa, hatta Husna ta tsorata da matakin da Meenal ɗin ta ɗauka, a daidai lokacin ne Kusan tare Nasir suka zo da Sadiya don jin ba,asin abin da yake faruwa....

MAMAN AFRAH
09025576222

https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=hqrt1
Chapter 94 · 0% Book details