Sashe 70
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai uban mene ne kike diddiftu a kicin É—in nan?" Saude ta ce
Dama Baba Kuluwa ce ta ce mura take ba za ta iya shan ruwa mai sanyi ba na canjo mata" Aliya ta ce
"Aikin banza da wofi duk samun wuri kuka yi wallahi da wasu Æ´an aiki ne za a ba ruwan roba in ban da asarar abu bakwa shan ruwan famfo, ai duk laifin Jidda ne ni akwai wani É—an aiki da zai saki jiki in na dawo gidan nan" Sai da ta yi furucin ta gane wautar da ta yi don dama tana nufin idan ta dawo gidan da aure wato bayan ta auri Ibrahim, ita kum Saude sai ta fara tunanin in ta dawo gidan yaushe? Maganar da Aliya ta yi ta cire mata shakkun tunani ta hanyar faÉ—in
,"Idan na dawo gidan nan watarana in Jidda ta haihu na zo zaman wanka" Tana faÉ—ar hakan Saude ta mayar da ruwan ta É—auki marar sanyi ta yi tafiyar ta ita kuma Aliya ta fito da sauri ta dawo falon ta bule jakarta ta saka cokalin.
Ranta fari ƙal har ta fara hango ta a wannan haɗaɗɗan gidan tana baza capacity tana zuba tashin mutunci don daga dangi har sangin dangiro sai sun san bata da mutunci musamman mutane makwaɗaita za su ɗanɗana kuɗarsu.
Jiida kuwa dakyar ta samu ya yi cokali biyu ta bashi maganin da ya sha sai bacci ya ɗauke shi plates ɗin abincin ta ɗakko ta fito ta rufe masa ƙofa ta sauko ƙasa. Nan suka zauna suna hira sai Aliya take cewa Umma ta kira a waya ta ce a bata lokacin tana sama, kiran Ummar Jidda ta yi Umma cike da fara,a amma ta ciki na ciki ya hau magana da Jidda cike da nuna soyayya ta ƙarya. Bayan sun gama ta ce ta gaishe da Abba suka yj samma Umma tana jin kamar ta shaƙo Jiddar daba cikin wayar.
Wajen ƙarfe biyu da wani abu Aliya ta ce tafiya za ta yi Jidda ta ce ta bari a yi la,asar amma ta ce tana so ta je ta yi girki saboda Kasim ya kira ta ya ce da wuri zai zo nan Jidda ta ma rasa mai za ta bata don daɗi haka ta je ta samu lece da atamfa ta zuba mata a leda Aliya sai godiya take haka ta rako ta bakin ƙofa sai Aliya ta ce
"Kai jama,a talaka ya shiga uku wallahi aka bar mutum da kuÉ—in adaidaita sahu kaÉ—ai ma sai ya kashewa mutum gwiwar zumunci" Jidda cike da tausayawa ta ce
"Ayya karki karaya ai shi zumunci hanya ce ra shiga aljanna sannan duk wanda ya yanke shi Allah zai yanke shi daga rahmarsa, bari na saka direba ya kaiki gidan...
Tun kafin ta kai ƙarshen zancen Aliya ta ce
"Lah ki bari kawai na biya adaidaitan" Ta faÉ—a tana juyawa za ta tafi sai Jidda ta ce
"Bari na saka miki a acc sai ki biya shi" Ta faɗa tana komawa ta ɗakko wayar sai ta tura mata dubu ashirin ta ce ta yi wani abu da canjin tun da ko jiya Mummy dubu ɗari biyu ta turo mata. Godiya Aliya ta yi suka yi sallama ta zo ta wuce mai gadi yana mata a sauka lafiya ko kallonsa bata yi ba ta buɗe ƙofa ta fice a zuciyarta ta ce
'Duk ranar da na auri Ibrahim ka tabbata ruwan shanka ya ƙare!' Ta faɗa tana duba alert ɗin da Jidda ta mata na dubu ashirin tana cewa a fili
"Matsiyaciya kin biya kuÉ—in aikin da za a yi a fatattka tsakaninki da mijin naki a sama mini gurbin zama"
Ko da ta dawo gida ta shiga kiran Amatullahi tana bata labari sai dai Amatullahi ta ce gobe su je su kai cokalin amma kuma ba a gobe za a kai cokalin gidan Jiddar ba saboda kar ta zargin wani abu na zuwa gidan a jere a kwana kusa. Bayan sun gama ta kira Umma tana zayyana mata ƙusurinsu na fitar da Jidda daga gidan da kuma samawa Aliya gurbin zama Ibrahim ya auri ta. Buɗar bakin Umma ta ce
"Kun yi min daidai ƴan albarka ubangiji ya muku albarka ke da Amatullahi ƙawar arziƙi, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha dole a fitar da Jidda daga gidan wannan idan ma har hakan ba zai iyu ba sai dai ke ki shiga a rufewa kowa baki hatta uban naku sai an rufe masa baki ruff in ya so sai ta rayu cikin uƙuba a gidan ta zama da ita da babu duk ɗaya da samuwarta da rashinta duk ɗaya!" Umma ta faɗa tana tunano irin yadda za ta baza capacity idan ta zama sirikar Ibrahim babu abin da take so irin ta ga Aliya a gidan nan da ake ta bada labari.
Bata ƙara bi ta kan Ibrahim ba sai ta tattara shi ta ajiye bata sake kiransa a waya ko masa saƙon whatsapp ba, tun da dai tana ganin aski ya zo gaban goshi, saura ƙiris ta koma gidansa sannan a matsayin matarsa.
Washe gari bata tambayi Kasim fita ba sai kawai ta bari da ya fita Amatullahi ta kira a waya ta faɗa mata su haɗu a marabar bamin titin suna haɗuwa suka tafi, ko da suka kai wa bokanya cokalin ta shafa wani magani ta ringa wani siddabaro tana ambaton sunan Ibrahim. Da ta gama ta ɗakko wani jan ƙyalle da baƙi ta ajiye a gefe ta shafa wani magani da mai sai kuma ta saka baƙin ƙyallan ta goge cokalin sannan ta saka jan ta ƙara gogewa sai da ya dawo tass sannan ta miƙawa Aliya ta ce
"Karɓi da ƙafarki ta hagu" Haka Aliya gabanta yana faɗuwa ta miƙa ƙafar hagu bokanya ta saƙala mata cokali ta ce
"Sai kuma ki ɗauke shi daga ƙafar taki da hannun dama" Haka Aliya ta aikata sai bokanya ta ce
"Kamar yadda ƙafar hagu take a gefe hannun dama a gefe basu haɗa hanya ba to idan Ibrahim ya ci abinci da cokalin nan haka zai yi gabas Jidda ta yi yamma, ba zai sake kallonta da idon soyayya ko idon rahma ba babu wacce zai so sai ke kaɗai!". Bakin Aliya kamar ƙofar gari wani daɗi da sanyi ya ziyarce ta har ta fara hango yadda za ta yi idan ta shiga gidan naira saboda da butulci ma ko da ta sauke idanunta a kan Amatullahi a zuciyarta ta ce
'Sai dai ki yi haƙuri Amatullahi idan na shiga daula zan sallame ki da kuɗi masu kauri sai dai dole na sauyaki a matsayin ƙawa don babu ni babu ƙawa da talaka ko hanya ba za mu haɗa ba, sai dai na samu matan masu kuɗi kuma mata masu aji, sannan ma ke barazana ce ga shiga ta gidan Ibrahim kar watarana faɗa ya haɗomu ki tona mini asiri!'
Aliya ta ce
"Bokanya kuma batun toshiyar baki fa mahaifina ba zai taɓa bari na auri mijin Jidda ba, sannan mutanen gari za su zargi wani abu uwa uba mijin Kasim ban san ya zai sake ni ba!" Da wata dariya bokanya ta bushe mai ban haushi ta jima tana dariyar kafin daga bisani ta haɗe rai tamkar bata taɓa yin dariya ba ta ce
"Wannan aikin da aka miki na cokali ya haɗa komai da kowa, babu wanda zai buɗi baki ya ce din me, babu wanda zai yi musu kuma Kasim a take kina ambata takardar saki zai baki shi ma mahaifinki ba zai tambayi dalilin wani auren ba ko dalilin mutuwar auren naki, sannan ruwanki ne ki bari ki yi idda kuma ruwanki ne ki yarda a ɗaura auren a ranar da aikin ya afku, sannan Jidda in kin ce ya sake ta ba zai yi musu ba kuma in kin ga dama zaki iya barinta a gidan kike gana mata uƙuba!" Sosai ta ji daɗi sai murmushi suke dokawa ita da Amatullahi don sun dara jin ƙamshian nasara.
Sun sanar da ita saboda taka tsantsan za su bari sai bayan kwana biyu Aliyar ta je gidan Jidda saboda kar su zargi wani abu, bokanya ta ce ko shekara ɗari za su yi babu matsala kawai dai a tabbatar Ibrahim ya yi amfani da cokalin. Dubu sha biyar ta karɓa kuɗin aiki Aliya tana jaddada mata sai sun dawo kawo mata gagarumar kyauta idan aiki ya ci!. Daga nan basu zame ko ina ba sai ƙyamis ta saya ƙwayar hana haihuwa pills don ta ce kar tsautsayi ya sa cikin Kasim ya shiga gwara ta fara planning don haihuwa sai a gidan Ibrahim.
Ko da ta dawo gida Kasim bai dawo ba don haka ta samu waje ta ɓoye cokalin da take jin tamkar da bugun numfashinta yake rayuwa!.
Bayan kwana biyu ta kira Jidda ta ce gata nan za ta kawo mata ziyara wai Kasim ne ya yi tafiya zai raka abokinsa wani gari É—aurin auren yayan abokin kuma yance kwana zai yi don garin da nisa hakan ya sa ta ji kaÉ—aici ya ishe ta za ta je ta wuni, Jidda ta ji daÉ—i kuma bata kawo komai a ranta ba.
Bayan ta je gidan Jidda wajen sha biyu na rana, suna ta hidimar girki tare Aliya tana maƙale da jakarta mai ɗauki da cokalin siddabaru. Har aka gama abinci bata ga Jidda ta zuba na Kasim ba kawai su Saude ta kwasawa a ƙaton fulas, ta ɗauka musu ita da Aliya. Suna cin abinci ta ce
"Ni ina mai gidan kuwa" Ta tambaya gudun kar ta ce ina abincin sa din marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, nan Jidda ta sanar da ita yana office yance yana da aiki da yawa ba zai dawo ba sai ƙarfe biyar.
Bayan sun yi sallar la,asar Jidda ta zauna ta yi azkar É—in maraice kamar yadda take yj kullum safe da yamma domin kariya daga dukkan sharri. Bayan ta idar ta shiga kicin ta fara É—ora tukunyar tuwon shinkafa da mai gidan ya ce ta masa da miyar agushi Aliya tana falo a kwance tana ta charting ita kuma Jidda suna kicin ita da Saude sai Baba Kulu da ta zo ta yi goge -goge ta fita.