Sashe 75
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sadiya ki yi haƙuri don Allah karki tanka mata, ki bari har Nasir ɗin ga dawo" ,Tana faɗar hakan ta ɗan dafa kafaɗar Sasiya sai kuma ta juya za ta tafj muryar Meenal ta katse ta da faɗin
"To almunafunfun, dama ku ne baƙaƙen munafukan unguwa masu haɗa kishiyoyi faɗa saboda gulma da tsugudidi"
,Kallo É—aya matar ta yi wa Meenal ta ce
"Ke idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri don wallahi ni jna danne banza in lakaɗa miki na jaki in yi gaba" Bata jira cewarta ba ta kaɗa kai ta tafi don ta san ta turawa Meenal ɗin haushi. Matar tana fita Sadiya ta shige ɗakin ba tare da ta kula maganganun da take ta yadawa a tsakar gidan ba, duk da abin ya mata ciwo a ce tana uwar gida amma amarya tana neman yin iko da ita, amma dai mai haƙuri yana dafa ditse watarana har ya sha romonsa.
Tun da ta shiga ɗaki take waya da chartong da samarinta har la,asar jefi ,-jefi tana yin baƙi su gaisa a tsaitsaye su tafi.
Yanzh ta fara tunanin yadda za ta fara fita ci gaba da barikinta tun da dai yanzu zaman ya fara kankama ita kuma ta saba da bin maza tana ganin Nasir shi kaɗai ba zai wadace ta ba.. Sai dai gida ne ba ita kaɗai ba bata san ya za ta yi da Sadiya ba duk da ta san ba lalai ta kai ƙaranta wajen miji ba sai daj ido mudu ne.
Lokacin da Meenal ta ji ƙaran motar Nasir da sauri ta ƙirƙiri kukan ƙarya har ya shiga ɗakinta ya ganta zaune a bakin gado ta takarkare tana ta sharɓar kuka hankalinsa ya tashi ya ma rasa ya zai yj sanann lallashin duniyar nan da kumambada baki ya yi amma ko gizau bata yi ba bare ya saka ran za ta amsa masa.
Sai da ya sha fama kafin ta ce
",Tun da ƴan nepa suka zo na basu kuɗin nan suka yanke ɓanbaren Sadiya shi ne fa matar nan ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, baƙaƙen maganganu sai da na yi da na sanin zuwana cikin gidan nan har da wata maya da ta zo siyayya wurinta suka haɗu sika ci mini mutunci, wai baƙincikin san,a nake mata saboda ni ba na siyar da caass bare asss" ,Cike da mamaki Nasir ya ce
"Ita Sadiyar ce da É—anyen aikin wannan ita bata san albarcinki take ci a gidan nan ba ba don ke ba da tuni ta cikawa rigarta iska fa," Wani daÉ—i ne ya cika zuciyarta tana rayawa a ranta indai tuggu ne da kutungwila ai sai ta gane shayi ruwa ne.
Meenal ta ce
"Ina fa ta sani wai har da ce mini zaune gari banza ce ni wai ina zaman kashe wando bana sana,ar komai, wai Nasir ɗin ma ba ya jin maganata wai ban isa in saka kaki mayar mata da nepa ba" ,Nasir jin tana magana cikin muryar kukan da ta yi wa muryarta ado da shi ya sa ya miƙe zumɓur yana faɗin
"Zo mu je ni ba na son munafurci" Tun daga ƙofar ɗakin Meenal yake kwaɗa mata wani mahaukacin kira, amma bata amsa ba tana jinsa dama riga take sakawa kasancewar jo ta yi rigar jikinta ta ɗame ta duk bata jin daɗin yadda ta kamata shi ya sa ta gwammace ta cire ta duka. Tana jin baloƙoƙon da yake amma bata tanka masa ba ko kiran bata amsa ba so take ya shigo ɓangarenta.
Sai da ya kira sau uku a na huÉ—u ta amsan tana fitowa daga É—aki ta samu kujera ta zauna a falon tana cewa
"Shigo mana Baban Kalifa" Ransa ne ya ɓaci jin wai shi take kira ma wato ita ba za ta je ta zama ɓarjajjiya da mai. Fuuuu ya taho Meenal ta take masa baya domin so takr ta ga ƙwaƙwaf sannan tana so ta nunawa Meenal ita ce da gida ba Nasir ba.
Yana shiga falon a faÉ—ace ya ce
,"Yanzu kenan sai na zo ke ba za ki iya zuwa ba" Sadiya ganin Meenal a bayansa ta shigo mata É—aki sa ta sauya akalar murya da ta fuskarta ta ce
"Ayya sorry Baban Kalifana na taho zan zo sai kawai ƙafata ta riƙe shi ya sa na dakata" Ta faɗa tana kallallame murya don ta luta in bata zama ƴar bariki ba kishiya za take kissar haɗa ta da miji wannan yana daidai da kashe mata aure yanayin yadda ta yi magana sai ya ji zuciyarsa ta ɗan sauka, ba kamar lokacin da ya taho a fusace ba. Meenal ganin bai yi magana ba sai abin ya bata mamaki Sadiya ta yi saurin faɗin
",Sannu da zuwa ya kasuwa"
Kawai sai Meenal ki ta yi ya ce.
"Kasuwa sai godiyar Allah" ,Ya faÉ—a yana É—an sassauta muryarsa Meenal jin zuciyarsa ta sauka ba kamar da ba sai ta karkata murya cikin É—an jan hanci ta ce
"Ni ma Allah zai bani abin yi Sadiya, kowa rabonsa yake samu kuma sana,a ma lokaci ne yadda Allah ya baki jari nima zai bani watarana!". Tana faɗar haka ta juya za ta tafi Nasir ya riƙo rigarta ya ce
"Haba Mrenal ai zan yi mata magana" Sadiya kuwa tana tunanin maganar mai sai kuwa ya tsuke fuska ko kula Kalifa da yake faman kiransa bai yi ba ya ce
"Sadiya a kan mai za kike mata gorin sana,a har kike cewa wai ita ce mai zaman banza" Kallon ni kika yi wa haka Sadiya ta yi wa Meenal sai dai kuma sanin tuggun mace ya sa ta ce
"Ka yi haƙuri ni ban yi da wata manufa ba"
Nasir ya haɗe girar sama da ƙasa ya ce
"Ai in har dai nepa ce to ba za a mayar yanzu ba sai na nuna miki Meenal ma ta isa a gidan na kamar yadda kike matata haka take ita ma don haka ki kiyaye a kan Meenal komai yana iya faruwa" Ganin ya juya zai tafi Sadiya ta ce
"Ina son magana da kai " Ya juya ya kalli Meenal da ta kashe masa ido É—aya ya ce
",Ki faÉ—a a nan kawai don ko a bayan idanunta kuka faÉ—a tamkar a kan idonta ne don da ni da ota mun zama tif da taya" Meenal fakar idon Nasir ta yi ta aikawa Sadiya gwalo Sadiya kuma sai ta yi kamar bata gani ba don bata yarda ta nunawa Meenal cewa hakan ya mata ciwo ba.
Danna É—acin da ya ziyarce ta ta yi ta ce
"Dama ina son zuwa gidan Noor ne gobe" Cike da mamaki ya ce
"Kuma shi ne za ki faÉ—a min tun yanzu tun da dai ai na san ba yau za ki je ba...
Meenal ta yi karaf ta ce
"Ka san da yake yanzu bata da ranar girki shi ya sa da ta ganka yanzu ta faɗa maka don karka suɓuce mata ka san fa ko wayarta in kana ɗakina ba ɗagawa kake yj ba" ,Abin ya yi wa Sadiya ciwo duk da ta san ko ma mene ne ba laifin kowa ba ne illa na Nasir shi ya sa Meenal take ɗaukanta ba a bakin komai ba duk da ta san shi ɗin ma ba komai ba ce a wajensa.
ÆŠan murmushi ya yi ya ce
"Kuma haka ne fa, gaskiya amarya da zafinki kika shigo fa"
Meenal ta ce
"Ai ƴan magana sun ce da zafi-zafi ake dukan ƙarfe ko ka ga laifina" Ya amsa mata da a,a suka ƙyalƙyale da dariya, wato sun mayr da Sadiya kamar wata mahaukaciya, hakan ya sa ta miƙe tsaye ta kalli Meenal tana nuna ta da yatsa cikin ɗaure fuska ta ce
"Ki fitar min a ɗaki!" Meenal da mamaki take kallon yadda Sadiya ta haɗe rai hakan ya sa ta taɓe baki ta juya ta fita, tana fita Nasir ya juya zai bi bayanta Sadiya taku ɗaya biyu ta yi ta sha gabansa ya tsaya da mamaki yana kallonta tana hucin ɓacin raj ta ce
"Duk abin da kuke mini a gidan bai isheku ba har sai kun biyoni har É—akina khna ci mini fuska?" Ta faÉ—a tana kafe shi da idanunta. Ganinnya sha jinin jikinsa ya kasa furta komai ta ci gaba da faÉ—in
"Yaushe rabonka da ka shigo ɗakin nan matsayina na matarka? Ni da ɗanka mun zama saniyar ware? Ka na ba amaryarka cimar da take son ci mu kuwa ko oho, hatta abincin da za a tsakura mana wanda va zai isa ba ake bamu babu mahaɗi sai dai no in nema, shin wnanan shi ne adalci? Allah cewa ya yi ku aura mata biyu biyu, uku uku ko huɗu huɗu in ba za ku yi adalci ba ku aura ɗaya, amma ka san ba za ka kwatanta adalci ba ka aura biyu ka zo kana tauye haƙƙin ɗaya?
A zafafe ya ce
"Ya isheki Sadiya wai yaushe har kika ga makwancina da kike daɗa mimi maganar da ta zo bakinki? Haƙƙin me na tauye miki? Idan har haƙƙin kwanciyar aure kike magana ke ba taimakonki na yi ba a wannan jikin naki kina fama da tsohon ciki za ki iya ɗaukan ɗawainiyar miji? Mai za ki iya taɓukawa daga wannan haƙƙin sai wanne aka tauye? Ita baka ganin sabuwar amarya ce komai za ta ɗauke ke kuwa ki ji da fama da kanki mana" Tsabar mamaki ma ta rasa mai za ta ce sai binsa da ido take ganin haka ya ce
"Idan baki da abin faÉ—i zan tafi" Ganin ya juya tana shirin tafiya ta ce
"Ita kuma nepar da aka ware ɓangarena aka yanke fa ko ita ma duk tana cikin tsohon cikin da nake ɗauke da shi?"Ta faɗa tana kafe shi da ido. Rasa mai zaj ce ya ce
"KuÉ—in wuta ne bakya biya ya kamata tun da kina samun kuÉ—i kike biyan wani kaso daga kuÉ—in nepa" Kallonsa take rana son tantance abin da yake faÉ—a cike da mamaki ta ce..