Sashe 55
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sadiya ba sai kin mana banza a gidan ɗan uwanmu ba, mu ai mun isa mu saka ƙafarmu a ko ina a gidan nan ba tare da shamaki ma ko kin manta shi ne ya sha nono ya bar mana?" Hibba ta karɓi maganar ta ce
"Ke kika kula ta ma, bata san zamanta a gidan nan É—orin É—osano ba ne" Husna ta ce
"Wallahi kuwa ai kawai saboda Kalifan nan ne amma ai da wannan cikin ma saj dai a haife a gidan tsohon...
Kafin ta ƙarasa faɗa Sadiya ta miƙe tsaye a zuciye ta saka hannu ta finciko mayafin Husna rai a ɓace ta ce
"Husna duk abin da za ki yi ya tsaya iya kaina amma karki kuskura rawar kanki ya kai ga mahaifina wallahi za ki yi nadamar hakan" Husna duk da ta tsorata da yanayin da ta ga Sadiyar amma sai ta yi ƙarfin halin cewa
"Dalla malama saka min mayafina" Gamgam Sadiya ta riƙe bata saki ba sai da Husnar ta fisge sannan Sadiyar ta sakar mata Hibba kuwa bata furta koɓai ba ta yi ɗiff sai da suka yi hanyar ɓangaren Meenal Hibba ta ce
"Kyaji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, wato wutar kishi tana nuƙurƙusar zuciyarki shi ne za ki sauke a kanmu" Ko kallonsu bata yi ba suka nufi ƙofar ɗakin Meenal dama ɗauke suke da kwando mai food flask masu kyau da alama abinci suka kawo. Ƙwanƙwasawa suka yi amma shiru waya Husna ta duba lokacin goma har da rabi hakan ya sa suka kalli juna suna danne dariyarsu.
A can cikin ɗaki Meenal da ta narke tana zuba shagwaɓa ce jin ana bugawa sai Naair ya ce zai je ya buɗe buɗar bakinta sai ta ce
"Ka rabu da ita Sadiya cw kishi yake cinta take son rabamu fa" Murmushin yaƙe ya yi shi dai ya san yau ranar farin ciki ce amma kuma ya kasa gane ta ina walwalarsa ta samu naƙasu, kawai dai ya rasa ma mene ne yake damunsa. Kamar raƙumi da akala haka ya tsinci kansa da bin umarninta, ya koma ya hau gadon tare da kwantawa ita kuma ta mayar da kanta ta ɗora a cinyarsa yake shafa gashin kanta. Sun jima suna bugawa amma babu alamar za a buɗe Hibba ta buɗe baki ta ce
"Yaya!" Jin muryar Hibba sai ya yi karaf ya ce
"Kin ji ashe ma Hibba ce ba Sadiya ba" Ya faÉ—a yana washe baki, tamkar ya sanar da ita mutuwa haka ya haÉ—e rai ta ce
"To mene ne idan su ne, shin basu san yau ranar mu ba ce ba ma buƙatar hayaniya?" Wani abu mai kama da mamaki ya ɗarsu a zuciyarsa duk yadda ya ga tana haba-haba da su amma kuma yau sai ta canja fuska sai dai ya yi tunanin ko dai don tana cikin raɗaɗin amarcin ne bata ware ba.
Idan Hibba ta ƙwala masa kira sai Husna ma ta kira shi amma Meenal ko amsawa ta hana shi ya yi. Sadiya tana jin su tana danne dariyarta, har suka gaji da tsayuwa suka zauna a ƙofar ɗakin suna zaman jiran tsammani saboda zuciyarsu ta faɗa musu cewa ko suna cikin halin da ba za a iya ganinsu ba.
Tana ganin yanayinsa ya canja ta san kuwa saboda ta hana shi zuwa wajen ƙannensa ne saboda ta san son su yake kamar mai amma dai ta yi alƙawarin takawa wannan alaƙar tasu birki. Wayarsa ce ta shiga ruri bata masa magana ba ya ɗ kko a kan bedside drower yana ganin sunan Hibba da sauri ya ɗauka cike da shagwaɓa ta ce
"Yaya mun jima a ƙofar ɗakin amarya muna jiranka, Hajiya ce da kanta ta tashi tun asuba ta muku girki, abin da ya sa ma bamu ƙaraso da wuri ba saboda cewa ta yi mu bari rana ta ɗan yi kar mu yi sakko baku tashi ba" Ba tare da ya kashe yana cewa Meenal
"Bari na karɓo abinci ne suka kawo in ji Hajiya" Baki ta taɓe ta juya ta kwanta tana rayawa a ranta cewa kwa ji da shi ciwon ajali a yatsa. Yana fita ya karɓo, su kuma sai suka yi ƙoƙarin bin bayansa wai za su gaisa da Meenal tun da a tunaninsu babu wani abu domin ya fito sannan tun da gidan ba su kaɗai ba ne a ganinsu ai ba sa zauna suna ta yin abu ɗaya ba. Samun kansa ya yi da kasa dakatar da su, suka shigo falon suka zauna suna ganin falon sai wani daɗi suke ji Meenal matar yayansu.. A falo ya ajiye kwandon suna ta hayaniya ya shiga ɗakin gar lokacin tana kwance ta juya baya yana ɗan washe baki ya ce
"Abinci ya hallara ranjki ya daɗe sannan kin yi baƙi" Juyowa ta yi ta ɗan yatsiina fuska ta ce
"Baƙi kuma? Daga ina aka samu baƙi da sassafe" Ya ji abin da ya ɗaure masa kai ɗan ƙara washe bakin ya ya yi ya ce
"Ƙannenki ne fa, kuma yanzu maganar ƙarfe sha ɗaya ake kin ga kuwa ai ya fi sassafe" Bata bashi amsa ba yake tsaye kamar wani itace duk abin da ake a kan kunnen su Husna sai dai basa gane mai ake cewa amma tabbas suna jin alamun magana. Sai da ya sake maimaita mata ta ɗan yatsina fuska haɗe da karyar da kai yadda ba zai fahimci da gangan za ta yi abin da take shirin faɗa ba ta ce
"Ka ce musu su dawo an jima" Sheƙeƙe yake kallonta saj ta yi abin tausayi na kissa ta ce
"Ƙafafuna ne suke cewa kuma fa ka san duk kaine ka yi wannn aika-aikar ina fita za su fahimci wani abu" Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauke don furucin nan nata na ƙarshe ya kauda duk wani zargi da ya ɗarsu a zuciyarsa da farko ya ɗauka dai zaɓen tumun dare ya yi ma,ana bata ƙaunar ma ƴan uwansa tun da abu ne sabo da bai saba da shi ba daga wajen Sadiya wato wofintar masa d ƴan uwa ya san Sadiya ba kallon ƴan uwansa ba duk wanda zai sako ƙafarsa gidan ba zai yi kuka da ita ba. Yana nuna tausayawa don shi ma ya san tana tafiya kamar ta sabbin ƴan shayi sai ya karɓi uzurinta.
Fitowa ya yi ya same suka zuba masa na mujiya don tunaninsu a yadda suka saba da ita za ta fito daga ta ji shigowarsu amma sain gashi da har da aike ta gagata fitowa kamar wata sarauniya. Shi sai da ya zo falon ma ya tuna bai tanadi abin faɗa musu ba sosa ƙeya ya yi ya ce
"Bacci take" Junansu suka kalla da mamaki din sun san sun ji muryarta sai kumamsuka kalle shi, sai lokacin ma ya gane ɓaran ɓaramar da ya yi don ga san za su iya jin dirin muryoyinsu Hibba ce ta ce
"Baccj kuma yaya? Ko dai ba za ta samu ganinmu ba?" Saurin É—aure fuska ya yi ya ce
"Ƙarya zan muku kenan?"Kai suka shiga kaɗawa kamar ƙadangaru sai ya ce
"Ku tashi ku wuce gida an jima kwa dawo" Sum-sum suka tashi kowacce tana gungune sula fita, bayansu ya bi ya rufe ƙofar, lokacin Sadiya tana tsaye jikin windon falonta daga wajen tana gogewa, kallo ɗaya ta musu ta gane a jone suke wato ransu a ɓace ko kallo bata ishe su ba, suka fita fuuuu.
Tun da suka fita a hanya suke ta mita suna mamakin faruwar hakan, ko da suka je gida suka faɗawa Hajiya sai ta musa tana faɗin ai ƴarta Meenal ba za ta yi haka ba wataƙila ma tana cikin yanayin farkon amarci abinka da sabuwar rayuwar da ba a saba ba. Haka dai suka haƙura amma ba don sun yarda ba suna da mamaki kawai!.
Sai sha biyu ta sako ƙafafunta daga kan gadon lokacin har an maimaita abin da aka gabayar jiya na amarci, abin da ya ɗaurewa Nasir kashi ne kamar wanda ya kai zicyara ƙofar gari haka ya ji hanyar zurum babu wani birki, don lamarin ya fi ƙarfin na darw har gwara da dare da sauƙi. Sai dai abin mamakin daga ya gama aikata sunnar sai dai abin ya tsaye masa a rai ga abu na damuwa amma ya kasa tuna mene ne. Sannan yadda take raki bashi da banbanci da farin shiga bai sai duk ana yin hakan don a kawar masa da zargi duk da ta san maganin da ta yi amfani da shi jiya da dare sai ya fi aikinngusar masa da mummunan zato fiye da kissa da kisisinar da take yi . Shi ya jona tuwan kamar dai wanda ya jona musu na farko ya kai ya haɗa ta shiga tana mita irin ta sabbin amare abun da bai sani ba har wankin ciki an taɓa yi mata wanda suka santa ba mutum ɗaya ba ba biyu ba ta daɗe tana gararamba da mutanen banza kuma har yanzu suna da contact na juna ba wai an rabu ba ne ana tare!.
Sai da suka fito falon ya buɗe kwanukan tana zaune tana wani yaɓe baki, plate ya fito ya ɗakko da kofuna, lokacin Sadiya tana ɗaki kallon ɗakinnta ya yi yana tuna irin romon amarcin da ya sha kwasa tana farkon zuwa sannan da ya kasance mace ce mai kula da kanta har yau ba za ka ji wani sauyi mai yawa daga gare ta ba duk da ta haihu, shiru ya yi yana son ya tuna mene ne bambanci tsakanin Meenal da Sadiyar mene ne aibun da ya bambanta su sai ya ji kansa ya sara, haka ya wuce da plate da kofunan ya koma part ɗin amarya.
Ko da ya zuba musu komai ya haɗa shayi kofi biyu da madarar da Hajiya ta ƙullo da milo a leda bata ce masa komai ba sai da ya gama ya ce
"Sakko mu karya" Da yake a kan kujera yake a zaune kallon sheƙeƙe ta masa don dama babu labarin da bata sani a kan lamarin gidansa da uwaraa take tafiyarwa ba ita kuma ko a mafarki ba za ta ɗauki wani renin wayo ba dole akwai sake!.
ÆŠan haÉ—e fuska ta yi ta ce