Sashe 37
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Karka zauna a kusa da ni don ban gayyatoka ba" Fasa zaman ya yi ya shiga mata nuni da hannu yana mata alama cewa da mutane a falo a gefe ɗaya yana mata alama da cewa ta yi ƙasa da muryarta. Cikin hargagi ta ce
"Ina ruwana da mutane, ko akwai wanda na kaiwa katin gayyata, da suka kwaso koɗaɗɗun ƙafafu suka zo, to yadda suka zo haka za su ɗauki ƙafa su koma inda suka fito" Kalamanta sun kusa saka ya zauce saboda ɗimuwa, ya san dai duk abokansa sun ji abin da ta ce, bai taɓa zato ko tsammanin hakan ba, wannan ranar babbar rana ce a gare shi mai ɗimbin tarihi amma yanayin Aliya ya nuna so take ta rusa komai, so take ta tada fitina, so take ta shayar da shi ruwan guba mai ɗaci ba ruwan zuma ba, a ce a ranar farkonta a gidansa tana magana kamar za ta kai masa duka anya zaman zai iyu?.
Kafin ya gama shan ruwan mamakin da Aliya ta shayar da shi, ji yake kamar ya nutse don kunya shi bai ma san ta ina zai fita falo kuma da wane ido zai kalli abokan nasa ba don ya san sun ji komai, kawai sai ya ga ta miƙe tsaye ta shiga warware laffayar jikinta, ya zamana daga ita sai leshin jikinta, wanda ya matuƙar amsar kyakkyawar fatar jikinta baƙin lalle da ja da ya ƙara haska kyakkyawar fatarta, ji yake yana son kaɗaicewa da ita a wannan daren mai ɗimbin tarihi amma hakan zai iyu?.
Na ce muku hakan zai iyu😃😃😃 ku bani amsa wato cmmnt ma sai kun bushi iska kuke yi a toh nima ai kuna gani a ƙwaryar shanku sai na bushi iska nake typin😒😕 labarin nan yana da tsayi akwai darasi akwai cakwakiya, abubuwa masu kamar almara za ku ji yadda.... Ba zan dai faɗa ba kawai ku biyoni mu cigaba da tafiya ko ni ina jin labarin a cikin raina.
MAMAN AFRAH
09025576222
https://chat.whatsapp.com/I3Lo5jRFh1CDcU1leu8VXW
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
*SADIYA*
Maganar Hajiya ta saka Sadiyar shiga ruɗani sannan abu ne wanda bata taɓa zaton cewa ko a mafarki Hajiyar za ta ambata ba, domin cikin ai ba na shege ba ne da za a yi maganar zubar da shi. Maganar da Hajiya ta ƙara yi ne ya dawo da ita hayyacinta jin Hajiyar tana faɗin
"Don haka ki É—akko mayafi ki zo mu tafi a cire cikin, saboda gidan nan ba matattarar yara va ce ta yaya za a ce daga yin yaye har kin sake É—urar wani cikin " Cike da jin nauyi da kuma jin kunya Sadiya ta ce
"Hajiya ni ma Allah ne ya ƙaddara ya bani wallahi ba da sani na ba ne...
Hajiya tana ɗaga mata hannu a harzuƙe ta ce
"Sadiya an ce miki jahila ce ni ban san Allah yake bayarwa ba?" Kai Sadiya ta shiga girgizawa alamar a'a, Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora cike da ɓacin rai take faɗin
"Ke duk ƴan dabarun nan na mata bakya yi, shin mai ya sa vaki saka tsinke a hannu ba ko kuma kin je an saka miki na bakin mahaifa, ko ki sha magani abubuwan tsarin iyali gasu nan barkatai amma kika yi hirim da ke kika sake ɗaukar ciki, saboda baƙin hali da mugun kishi saboda za a yi amarya ku mata dama damuwarku gado shi ya sa baku da aiki sai gasa a haihuwa so kike kafin ta zo kin tara bataliyar ƴaƴa yadda ba za ta taddo ki ba, to albishirinki ba wani dogon lokaci za a ɗauka ba da har kike tunanin tara ƴaƴa a kwana kusa Nasir zai angwance" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalli Hajiya sai kuma ta sunkuyar da kai.
Hajiya ta ƙara kallon Sadiyar kallo irin na ƙasƙanci don ita duk ladabi da biyayyar Sadiya da kuma haƙuri ba wani birgeta yake yi ba ta ce
"Ina so ki sani ciki dole a zubar da shi idan kuma har ƙin ƙi to shawara ta ragewa mai shiga rijiya, ko ya faɗa ko kuma ya sauya shawara, zaɓi biyu ne ko dai ki yarda a zubar ko kuma ki zauna ki raini cikin amma ki sani ɗawainiya ce kika ƙarawa kanki, don Nasir bashi da ƙarfin riƙe mata biyu da yara biyu a yanzu ga kuma hada-hadar shirye-shiryen aurensa shin da wanne zai ji? Wallahi wasu matan baku da lissafi"
Sadiya a fili ta ce
"Ki yi haƙuri Hajiya amma ba zan iya kisan kai ba"
A zuciyarta kuma ta ce
'Duk irin rufin asirin da yake da shi ai a samun Nasir ko ƴaƴa goma ne ba zai gagara ya riƙe ba amma saboda son zuciya da sarewa sannan kuma bai yi dacen mahaifiya ba shi ne kuke raina ni'imar da Allah ya bashi'
Hajiya ta sake cewa
"Dama na zo in kai ki a zubar ne amma tun da kin ce kin ji kin gani to ga wajen nan"
Tana faɗar hakan ta juya ta fice, zuwa jimawa can sai ga Nasir kamar an jefo shi mamaki ma take dama bai tafi wajen kasuwancin ba, ko arziƙin sallama basu samu ba haka ya shigo kamar wanda ya zo filin yaƙi, yana shigowa ya ce
"Sadiya wato kin rainani kin raina mahaifiyata, Hajiya ta zo har gidan nan amma ki ambula mata ƙasa a ido ke ga ishashshiya da mai ko? To ki sani tun da kika ƙi zubar cikin nan ni ba zan dawwama da wahala ba kullum kuna jinya ke da yara ga shirin auren nan" Ya faɗa yana tada jijiyoyin wuya.
Sadiya a zuciyarta ta ce
'Wai namiji da Allah ya É—ora masa gabaÉ—aya É—awainiyanda kulawa da iyalansa amma shi ne yake gajiyawa, bayan babu wani abu da Allah ya É—orawa mace ta sayawa kanta ko ta sayawa Æ´aÆ´a sai dai don kyauatatawa gabaÉ—aya É—awainiya kan namiji take kama daga ciyarwa shayarwa tufatarwa lafiya da sauran abubuwan da baki ba zai iya furtawa ba' Ganin ban ce komai ba ya ce
"Aure dai babu fashi idan ma kin yi haka ne don in ji tsoron É—aukar É—awainiya in janye batun aurena, ko kina so ko bakya so sai wata ta shigo gidan nan, don mi ban gina gidana don mace É—aya ta zauna ba, ni mijin mace huÉ—u ne!".
Cikin halin nuna tashin damuwa da kalamansa ta ce
"Allah nuna mana, ya sanya alkairi!." Wannan maganr da ta yi ta ƙara fusata shi, ya so a ce ta ji haushi ya ƙuntata mata amma sai ya ga bata damu ba, a zuciyarta ta ce
'Mace tana kishi ne a inda aka san darajarta, zuciya tana damuwa da wanda ya damu da ita ne wannan shi ne cancanta mafi daraja amma mijin da bai ɗaukeka a bakin komai ba mijin da yake wulaƙanta ka kishin mai za ka yi a kansa?'
Kamar zai kai mata duka ya ce
"Idan ma ba har zuciyarki kika faɗa ba can ta matse miki" Yana faɗar hakan fuuuu ya fice daga gidan, Sadiya tana mamakin mahaifiyar Nasir da bata kawo zaman lafiya a cikin gidansa ita da ƴaƴanta kullum ƙoƙarinsu su famfa shi, su rura wutar gutsiri tsoma a gidan bata tunanin su Husna ma mata ne kuma dole watarana gidan miji za a kai su, basa ma tsoron a musu abin da suke yi wa wani tun da duk abin da mutum ya yi shi ake yi masa.
Tun daga wannan rana sai al'amura suka ƙara taɓarɓarewa a cikin gidan, idan Nasir ya bada ɗanyen abincin da ba zai isa su ci ba sannan sai ya hana kuɗin cefane, gashi babu abin da take siyarwa bare ta samu abin da za ta yi amfani da shi, ta yi masa magiya har ta gaji amma ko a kwalar rigarsa, sannan wani abin ɓacin ran ta fahimci yanzu abincin gidan ma sai ya ga dama yake ci, sai dai ita da Kalifa su ci wataran ma sai dai ta saka musu ɗan gishiri su ci ko babu mai don yanzu abin na Nasir ya ta,azzara ko maggi ya daina siya bare mai komai yanzu ya janye jikinsa daga siya, ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta.
Duk da kasancewarta mace mai sirri da ƙin bankaɗa damuwarta amma haka take faɗawa ƙawarta Noor wasu abubuwan tun da ita Mama ko ta kira ta a waya za ta zayyana mata damuwarta sai ta dakatar da ita idan ma ta fara faɗa sai ta ƙaryata tun da har yau Nasir yana hidima da su in aka shafi kwanaki yana basu kuɗi wannan dalilin ya sa suke ganin ma kawai shaci faɗi ne don dai ta ɓata masa suna. Tun da a ganinsu idan har gida bai ƙoshi ba ai ba a ba wa na waje ba da a ce a gidansa bai wadata su ba ai ba zai ke ba sirikansa ba, basu san duk wannan yana cikin shika-shikan rashin mutuncin Nasir ɗin ba.
Noor ita take kwantar mata da hankali sannan ita take bata ɗan wani kuɗin ta saya wani abu da bta da shi, duk da bata fitowa ta faɗi komai da komai sai dai bahaushe ma yana cewa labarin zuciya a tambayi fuska. Akwai lokuta da dama da wani yake cikin damuwa ko cikin halin son a taimaka masa saboda wata matsala amma kuma bakinsa yana da nauyi wajen sanarwa da wasu damuwar tasa, sai dai ba kowane lokaci ne sai mutum ya faɗi ainihin a taimaka masa ba, ko kuma sai ya bayyana buƙatarsa, wani a ɗan fashi baƙin da zia faɗa ko bai warware komai ba hakan ya isa a gane a taimaka masa inda hali ba sai ya yi roƙo ba wani yana jin nauyin ya roƙa, wannan halayyar ce take faruwa tsakanin Noor da Sadiya.