← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 106

Sashe 52

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abba Kasim ɗin ba namiji ba ne sak!." Sai da ta yi furucin sannan ta ji wata kunya ta lulluɓe ta, maganar ta ɗaurewa Abba kai ya fara tunanin to ita Aliya a ina ta san namiji da har za ta ti ikirarin shi Kasim ba namiji ba ne, bayan jiyan ne ranar farko da ta kaɗaice da na miji ba ma wannan ne abin mamakin ba yadda har ta baro gidan miji a kan wannan ƙaramar matsalar don iya hasashen sa dai kamar tana nufin bashi da wani kataɓus a wajen aiwatar da sunna ma'ana yanayin jikinsa ba zai gamshe ta ba.

Ba kallon ita ba hatta Abba sai da ya ji kunya amma dai ɓacin ran da yake ciki ya danne kunyar Aliyar ya ƙara buɗe baki yana ƙwalawa Umma kira, sai ga Umma a sukwane zaninta riƙe a hannu don yau an damalmala mata lissafi damuwa da takaicinta in ta tuna mummuna Jidda tanaa can hankalinta kwance ita kuma da kyakkyawar ɗiyar ta suna nan hankali tashe, ƴar tata ta since musu zani a kasuwa. Umma tana fitowa ya hau ta da faɗa duk da haƙuri da kawar da kai na Abba amma yau kam ta gane shayi ruwa ne don a yanayin yadda yake faɗa tamkar babu abin da zai hana shi kai hannu ya ce

"Saboda ban isa ba yarinyar ta baro É—akinta a kasa samun wanda zai kira ni a waya ya faÉ—a mini, sai dai daga waje a sanar da ni, yanzu wannan abin kunyar ina za a kai shi a ce wai saboda wani dalili marar tushe saboda Aliya ta raina mutane ta kamo hanya ta dawo gid" Umma da sauri baki yana rawa ta ce

"Baka fuskanci abin da take hufi ba Kasim ɗin ne yake da halittar mata maza" Ɗan shiru Abban ya yi yana tunanjn ya aka yi daga ɓangaren Kasim ba a sanar da su da wannan babbar larurar ba, amma dai babu yadda za a yi a ce ta baro ɗakinta ba tare da ta sanar ba wannan shi ne abin da ya ƙona masa rai.

Abba ya ce

Mai ya sa baki yi waya kin faÉ—a ba za ki kamo hanya ki taho bakya bari a je can a sulhunta" Aliya ta ce

"Abba ni ba sai an sulhunta ba na haƙura da shi kawai" Abba hannu ya ɗaga ya wanke fuskar Aliya da mari ba tare da ya ce komai ba ya juya a ƙufule ya fita waje, Umma duk kunya da takaicin mutanen wajen ya kama ta amma dai gwara a warwate matsalar ita bata ma ƙaunar Aliya ta dawo gida da zama a nata ganin da Jidda ce za ta yi kwantan rashin miji sai gashi yanzu tata tilon ƙar tana neman yin kwantai don a ganinra kwana ɗaya a ɗakin miji ma ai zai karya lagon ƴanmatancin Aliyar don ta san ma ai tuni ta zama bazawara idan ya sake ta sannan bata da tabbacin ba a samu rabo jiyan ba tun da dai ta san tun da har Aliyar ta ga halittar da yake ɗauke da ita to tabbas an aiwatar da sanna.

Abba yana fita ya É—aga waya ya kira Baban Kasim yake labarta masa abin da yake faruwa, nan da nan ya sanar da Abban cewa gashi nan zuwa gidan Abban. Baban Kasim yana kashe waya sai ya shiga kiran Kasim don jin ba a sin yadda aka yi ya bar matarsa sabuwar amaryar kwana É—aya tak ta tafi gida, tun da wannan abu ko shi ne aka yi wa Æ´arsa hakan ba zai ji daÉ—i ba don wannan abin kunya ne abin takaici ka kai Æ´a É—akin miji ta dawo gida.

Kasim da yake shirin fitowa daga shagon nan kiran Babansa ya katse masa hanzari yana É—agawa Babansa ya ce

"Kasim mene ne dalilin da ya sa ka bar matarka ta taho gida? Kai baka mata bayanin cewa tun kana ƙarami aka maka tiyata cewa kai ba mata maza ba ne kuma mata maza suna iya rayuwa kamar kowa su haihu kamar kowa, sannan suna da dama kamar kowa ba?" Baban Kasim da ya katse gaisuwar da Kasim yake kawo masa ya faɗa cike fa hargagi har Babar Kasim da take kicin ta jiyo abin da yake faɗa, hakan ya sa gabanta yankewa fa faɗi a nata ganin ta aurar da ɗan nata amma kuma wata wutar tashin hankali yana tunkaro su. Kasim a take ya ji bakinsa ya bushe wani tashin hankali ya saukar masa maimakon ya ba Babansa amsar tambayar da ya masa sai ya ce

"Gani nan zuwa Baba" Baban nasa kuwa ya yanke kiran, shi kuma Kasim ya yi hakan ne son kawo ƙarshen maganar saboda yana mamaki da tantamar anya Aliya ta tafi gida kuwa? Tun da ya san a gidan ya barta.

A rikice ya yi cikin gidan yana ƙwala mata kira, amma shiru ko ƙutarta bai gani ba banɗaki ya nufa amma bai ganta ba, kicin ma haka duk da ba ya saka ran ganin ta a kicin ɗin saboda ya san babu abin da za ta je yi, yana komawa ɗaki da ya je bedroom a nan ya tabbatar da maganar Babansa don ya ga alamar hargitsa kaya da Aliya ta yi.

Bai yi wata-wata ba ya fito daga gidan sai da ya zo ƙofar gida ya tuna bai ɗakko mukulli ba ya koma ya ɗakko ya fito yana cikin datsewa ya ji wani yana cewa
"Ango ka sha ƙamshi" Yana juyawa ya ga wani abokinsa ne, hannu kawai ya iya ɗaga masa ya tsare mashin ya hau don ya lura idan ya tsaya zai iya gane ba ya cikin hayyacinsa. Suna cikin tafiya kiran Babansa ya shigo yana ɗagawa Baban nasa ya ce

"Kasim ka zo gidan Abba muna can" Gabansa ne ya hau dakan lugude yana fatan kar wannan zaman da za a yi a saka ya warware igiyar aurensa da Aliya.

SADIYA
Da kamar ta nufi gidan Kaka amma sai ta daure ta ƙarasa gidan, tana zuwa sai ta ga babu mukulli a ƙofar gidan mamaki ya kama ta kenan mai yake a gidan bai fita ba ko dai ya dawo daga kasuwar ne ko kuma mene ne dalili da wannan saƙe-saƙe ta shiga gidan tana jin babu daɗi a ranta na wunin ranar yau bata sayar da kayan sana'ar ta ba bayan ta saba kama kuɗaɗenta. Tana shigowa ta fara sallama amma shiru ba a amsa ba sai dai ta ga takalminsa a ƙofar ɗakin sai da ta yi sau uku amma babu alamar zai amsa haka ta shigo ta ɗaga labaulen falon ta shigo dama Kalifa bacci yake a bayanta a ranta tana raya ko ina motar tasa kuma tub da baya ganta a ƙofar gida ba.

Ko da ta shiga ɗakin yana gaban madubi yana idaidaita hula a kansa amma ko kallo bata isheksa ba, kamar dai ba a yi ruwanta a wajen ba. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi wanda take fatan hakan ya narkar da takaicin da yake danƙare a ƙirjinta. Ta ɗan daure ta ce

"Barka da yamma" Bai amsa ba illa ya saki hular tasa ya riƙe ta da hannu ɗaya saɓanin lokacin da ta shigo hannuwansa biyu suka riƙe suke da hular, ɗaya hannun marar hular ya yi amfani da shi wajen ɗaga mata hannu alamar ta dakata hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru tana kallon ikon Allah duk da bata san dalilin dakatar da ita ɗin ba. Ya kusa minti huɗu yana daidaita hular har sai da ya ga ta masa yadda yake so ita kuma tana jira ta ji abin da zai ce. Da ya gama gyara hulae bai juyo ba yana kallon madubi sai da suka hala ido ta cikin madubin ta ji ya ce

"Ki daina kalle mata kwalliyar" Cike da mamakin furucinta da kuma rashin sanin inda maganar ta dosa sai kuma ya ce

"Na ji kina mini barka da yamma ke ai ya kamata a yi wa barka ko?" Da nuna alamar tambaya a fuskaryta ta ce

"Ban gane ba barkar mai?" Ya ce

"Barkar dawowa ɗakin ki mana, ai nan Baba ya kirani a waya yana ta bani haƙuri, na ce bari na tambayi Meenal ɗin in ta haƙura sai ki dawo" Har sai da idanunta suka ciko da ƙwallah tsabar ɗacin da maganar ta mata wato dai Baba ya zubar mata da mutunci da kima a ce ya kaita gida amma saboda ta zauna a gidan aure yake bada haƙuri gashi yanzu ya ja mata raini har ana mata barka da dawowa ɗakinta, wato ta ga samu da ta rashi ɗan kawar da kai gefe ta yi tana danne abin da ta ji ta ce

"Allah sarki Baba yana son ƴaƴansa su yi zaman aure ne ai sannan mutum ne mai son zaman lafiya ba ya son tashin hankali shi ya sa ya zaɓi ya bada haƙuri a kan ciccira magana" Ta ce tana jin kamar mai.

Wata Æ´ar dariya ya yi wacce ta yi kama sa ta yi kama da ta raninin hankali ya ce

"Allah ko?" Bata tanka masa ba ta zaɓi ta bar ɗakin don ta ga abin cin fuska ne. Tana dab da fita daga ɗakin ya ce

"Da farko na dakatar da ke ne da kika min mafana saboda ina saka hula bana so ta karkarce kin san idan za a yi wa amarya kwalliya abin a tsara ne don a birge ta" Murmushi ta yi ta ce

"Wannan gaskiya ne" Bai jira ta ce wani abu ba ya ce

"Na ce kina kalle mata kwalliyae ne saboda ta ce mini kar in bar ƴan mata su kalle mata ni" Maganar ta ɓata mata rai amma sai ta zaɓi mayar da martani cikin ruwan sanyi ta ce

"To ai ƴanmata ta ce ka ga bata ce har matarka ba kenan matarka ta fi damar ta kalle ka don halaliyarka ce" Tana faɗa ta juya ta fita. Shi kuma ya murmusa don yana ganin Baba ya ƙara bashi damar wulaƙanta ta tun da yana nuna dole sai ta zauna a gidan, tun da yana faɗa masa sauran ƙannenanta suna nan babu mashinshi ni.
Chapter 52 · 0% Book details