Sashe 41
Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryarsa ce ta katse mata tunani ya ce
"Aliya amaryata" Watanuwar harara ta galla masa kamar idanunta za su faÉ—o, falon ya fito ya É—auki lemon tana fakar hanyar É—akin ya buÉ—e five alive ya jefa maganin da Salis ya bashi a ciki ya mayar ya rufe.
Duka ya ɗauka ya shiga ɗakin ya ajiye a gaban gadon ya koma falon bayan ya ce mata shi zai kwanta a falon tun da bata buƙatar ya zo inda take banza ta masa son ko magana ya yi haushi yake bata. A doguwar kujera ya kwanta yana jin duniyar ta masa zafi. Aliya kusan awa biyu ta ɗauka a zaune, cikinta da yake mata ƙugi ta ɗauki lemon da aka saka magani ta buɗe ta kafa kai ta sha ta ajiye ko rufewa bata yi ba, jim kaɗan ta fara hamma bata san ta kwanta a gadon ba bacci ya yi awon gaba da ita da mafarkin gidan Jidda, tana ta gani a mafarki gata nan a gidan Jiddansuna rayuwa da Ibrahim matsayin mijinta.
Zuwa can Kasim da ya yi tsai yana jin babu motsin Aliya a ɗakin, lallaɓawa ya yi ai kuwa ya ga ta yi bacci, hakan ya sa ya ci karensa babu babbaka a nan ya ɓingire bacci da mafarkin Aliya da take kusa da shi yau dai burinsa ya cika.
Aliya wacce maganin baccin ya saki, ta riga shi tashi a bacci don lokacin har gari ya fara haske, tana tashi ta ga abin da ya faru wanda ya ɗaga mata hankali sai dai a ƙwaƙwalwarta tana iya tuno kamar a cikin baccin ta ga ta bashi haɗin kai, kamar kuma ba a bacci ba ne kamar dai a zahiri ne kallo ta shiga ƙarewa Kasim da yake shararar bacci ko kayan jikinsa bai mayar ba. Hannu ta kai ta rufe bakinta gudun kar ihun da take ƙoƙarin wwace mata ya fita, a kiɗime ta sauka daga kan gadon tsabar ruɗani bata san ma ina take jefa ƙafafunta ba, ko kaya babu a jikinta haka ta ɗakko wayarta da ta gani a kan madubi da hanzari ta fito daga falon tsakar gida ta nufo tana fitowa ta yi tozali da injin da bashi da maraba da tsoho wani haushi ya turnuƙe ta duk da halin da take ciki ya doke wannan.
Kicin ta nufa ta kamo sunan Umma, Umma da take kan sallaya Abba bai dawo daga masallaci ba, tun da ta idar da sallah take zaune a kan sallayar ta doka uban tagumi tana tunanin Aliya da gidan da ta tafi zaman aure babu abin da ya fi ƙona mata rai da akance gidan Jidda haske ral amma gidan Aliya ana shiga da amarya inji yana mutuwa dakyar aka samu ya tashi sai da masu gyara suka masa ribdugu. Tunani da damuwarta ɗaya Jidda tana can ta kwana a gida mai kyau Aliya kuma a gidan ya ku bayi.
Tana cikin wannan tunanin ta ji ƙaran wayarta gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta nufi wayar don tana tsoron ko sanarwae mutuwa za a faɗa mata, sai dai ganin sunan Aliya ya sa ta danna Ok da sauri tana karawa a kunn Aliya ta fashe da kuka ta ce
"Umma kin san wa na aura?"
Gaban Umma ya bada dididdimdimmm a tsorace ta ce
"Aliya ba Kasim kika aura ba"
Aliya ta ce
"Umma ki bar maganar wai Kasim na aura eh shi na aura amma Umma akwai ɓoyayyan al'amari wallahi mai firgitarwa Innalillahi wa inna ilaihi Umma ... Na aura!".
Umma da take tsaye sai gata gata ta yi zaman Æ´an bori idanunta tamkar za su faÉ—o numfashinta yana barazanar guduwa ya barta...
*KU JE KU DISKANTA SHIN WACE CE A CIKIN KU ZA TA BANI AMSAR WA ALIYA TA AURA? NA BAKU GARI😃* *AMMA* *KO NI NA TSORATA SA ABIN DA TA FAƊA LALLAI KASIM YA SHAMMACE MU, SAI DAI AMSAR TANA NEXT PAGE IN MUNA RAYE*
Shin wai bakwa neman maganin mata mai inganci don ku birge mazajenku? Ku kankarowa kanku mutunci da magungunan sa nake siyarwa akwai maganin sanyi akwai atamfofi lesuna zanin gado takalma kayan yara akwai plazzo set na yara da manya kai komai ma akwai mai so ya min magana don mallakar nasa har kayan kicin duk akwai a farashi me sauƙi
MAMAN AFRAH
09025576222
https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=ems_copy_t
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
*SADIYA*
Duk da kasancewar ta mai haƙuri da kawar da kai, komai ya farutana yin kamar bata gani ba idan kuma ta ji tana yin kamar bata ji ba, sai dai wannan furucin nasa ya taɓa mata zuciya. Ta yaya za a yi ya faɗa mata cewa saboda Meenal ya saya mota ita da bata zama matarsa ba duk da za ta zama, wato su iyalinsa basu kai matsayin da za a sayi mota saboda su ba, har ya duba ƙwayar idanunta yana faɗar saboda Meenal ya sayi mota don kar ƙawayenta su ce bashi da mota. Danne abin da ya ɗarsu a zuciyarta ta yi tare da ƙoƙarin ƙirƙirar wani murmushi don a a rayuwa ba komai ba ne sai mutum ya magantu a kansa, ba komai ne sai ka yi magana ba, ba a kowane abu ake ƙorafi ba!.
Tana murmusawa ta ce
"Amma fa ka yi namijin ƙoƙari!.Gaskiya gwara da ka siya ko don ka fitar da ita kunyar ƙawaye"Ji ya yi kansa ya masa wani girma yana riƙe da Kalifan ya washe baki ya ce
"Ai kam kin san an ce amarya sai da lallashi" Tana dariya ta ce
"Gaskiya kam amarya ai hukuma ce sai da lallashi" Yana kallonta don ya ji daÉ—in furucin ta ya ce
"Uwar gida fa?" Wani murmushin ta sake yi ta ce
"Uwar gida sai haƙuri" Ya ɗan yi jim sai ya ce "Kenan ita uwar gida sai haƙuri mai ya sa kika ce haka?" Ta ce
"Kawai dai na ga dacewar hakan" Iska ya É—an hurar ya ce
"Kuma maganarki haka take"
Sadiya ta ce
"Dama mana" Kalifa ya miƙa mata ya juya ya ce mata yana zuwa ya rufo ƙofar, cikin gidan ta dawo tana jin lokacin da ya tada motar ya yi gaba, don dama ya iya mota, Kalifa ta ajiye ta ɗauki abin wasa ta bashi, ta cigaba da uzurinta don ita yanzu sana'ar nan ta fiye mata komai don ta lura ita ce gatan ta kuma rufin asirinta.
Kwanci tashi asarar mai rai yanzu cikin jikinta yana da wata bakwai, ya fito sosai, sana'a kuwa yanzu ta kafu, duk unguwa an san ta wasu ma daga wani wurin suna zuwa siya, don yanzu har da nono take ɗaurawa mai kyau sannan ribar da take ɓoyewa ta haɗa ta siyar da frige ɗin ta cika ta saya freezer amma ba sabuwa ba sai dai babu abin da ya same ta. Da yake Allah ya saka mata albarka sosai ta bunƙasa, yanzu duk ƴan ƙananun kayan jarirai tana saya wanda za a iya sakawa maza da mata, duk da tana zuwa awo amma ita take yi wa kanta komai kama daga kuɗin napep zuwa asibiti da kuma abubuwan da za ta buƙata har magunguna, tun da idan ma ta faɗa masa cewa za ta je asibiti iyakarta ya ce
"Sai ta dawo" Har ta saba da wannan furucin ita yanzu tun da dai tana sana,ar nan kuma tana rufa mata asiri bata damuwa ma da watsi da kuma wofantar da haƙƙoƙinta da yake yi. Yanzu ta fara siyar da farin man Ok da kuma manja, curry da sauran kayan miya na amfanin gida, yanzu gidan koyaushe baka rasa wanda zai zo siyan abu. Hatta kayan gwanjo siya take nata da na Kalifa sai ta saya kamar sabbi ta wanke ta goge suke saka abin su don haka dogayen riguna da wando da riga da kuma riga da skirt duk ta saya tana kwalliyarta a cikin gidan ta fito abinta tsaf idan ma tana marmarin abu sai ta siya ta dafa kayanta shi ma Nasir ɗin ya ci, hakan ya sa yake ba su Hajiya labarin ai kuwa Hajiyar take ce masa dama ai ta faɗa masa idan ma tana sana'ar duk a hidimar gida kuɗin zai ke ƙarewa, basu san sana'a sirri ba ce, tana yin alherinta a ciki.
Yau ta kama juma'a bayan ta gama ayyukanta, lokacin Kalifa ya yi bacci, tana so ma ta tashe shi saboda yamma ta yi amma kuma gudun rigima sai ta ce idan ta yu wanka ta shirya sai ta tashe shi. Bayan ta yi wanka ta shafa fowder ta lips stick, riga da wando na plazzo ta saka da hularsu kalar dark blue kayan sun karɓe ta ta shafa turare sai ƙamshi take buɗaɗawa. Cikn ta da ya fito ya yi ɗas a cikin rigar, ta je kusa da Kalifa za ta tashe shi don lokacin miyar dare ce kawai take dahuwa a kan gawayin ta gama tuwo. Sallamar wata yarinya ce ta dakatar da ita, inda ta ce ta bata farin mai kwalba guda da kuma curry ɗaurin ɗari biyu guda biyar sai zoɓo na ɗari uku, kasancewar dama man ɗaurawa take ta ajiye kowane awo ta bata duka ta bata canjin, ta karɓa ta juya ta fita ita kuma ta je za ta ajiye kuɗih kawai sai ta ji ƙaran tsayuwar mota a ƙofar gidan, ƙaran rufe ƙofofin motar ta ji sai kuma ta ji an turo ƙofar gidan, muryar Nasir ta fara jiyowa yana ɓaɓɓaka dariya, sai ta ji yana shigowa sai kuma take jiyo takun takalmi ƙwas-ƙwas wanda hakan yake nuni da ƙaran takalman mace ne, sai kuma zuciyarta ta bata tare da su Husna yake ƙannensa, har ta fara fargabar zuwansu saboda rashin arziƙinsu kar su mata halin nasu na rashin mutunci tun da su ba sa tunanin makomar nasu auren idan sun yi tun da su ma mata ne watarana gidan miji za su je!.