← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 106

Sashe 95

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣9️⃣

UMMA

Addu,a take amma kukan da take na hawaye, kuka ne marar sauti wanda ambaliyar ruwan hawayenta ne kaɗai suke nuni da cewar kuka take sai bakin ne kaɗai yake kai komo, kai komo na addu,a da kuma kai komo na kukan da na sanin abin da ta aikata tun da dai ga shi ba a kai ga samun biyan buƙata ba matsaloli maau tarin yawa sun baibaye ta matsala ta farko riƙe ta da gawar ta yi matsala ta biyu gabaɗaya maganin ma ya zuba kuma ba a yi aikin da ya dace a yi da shi ba, wato aiki dai bai kammalu ba.

Jin ta kakare a wajen karatun da take sai ra ji ta ƙi gana ta ƙi ba ya sai wani abu da take ambato wanda ita kanta ta kasa bambance cewa karatu ne ko kuwa waƙa.

Jin ta take kamar ba a duniya ba idanu ta rufe gam tana tunanin mafita, ji ta yi an ƙarawa hannu da ƙafarta kaimi wajen riƙo, hakan ya sa ji duniyar ta mata zafi tana jin ina ma tana da damar da za ta tashi jama,ar gidan wataƙila su su kawo mata ɗauki amma yanzu lamarin sai saɓ barka. Kafin ƙiftawar ido sai ganin Malam Kalla ta yi a hankali yana tashi zaune har ya kai ya zauna dangargar.

Salatin da ta warto a bakinta wanda ba ta sanya da aka yi ba har ya fito fili ya karaɗe ɗakin tamkar landan ya taƙarƙare yana kiran sallah. tun daga salatin nan bakin Umma bai samu damar warto wani furuci ba ko da kuwa waƙa ce ba karatu ko addu,a ba. Sai kuka da take yi kamar an buɗe famfo zuwa yanzu taimako take nema ba ta ankara ba sai kawai ta ga Malam Kalla ya ɗauke hannun sa daga riƙon da ya mata na ƙafa da hannu ya ya ɗauke ta ya ɗora a cinyarsa duk da ƙoƙatin fisge kanta da take yi daga gare shi, tashin hankali wanda ba a saka masa rana jinta zaune a cinyar gawa har gawa tana miƙa baki saitin kunnenta tana mata raɗa da ƙarfi ƙirjinta ya buga wata irin karkarwa da jikinta ya ɗauka ita ta saka ta buɗe idanunta sai lokacin ta gane ba gaske ba ne a idanun zuciyarta ne da sauri ta mayar da kallonta kan gawar ta ganta tana a yadda take hannun gawa riƙe a ƙafa da hannunta wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a fili.

Sai lokacin ta fahimci cewa tsabar halin firgici da ruɗanin da take ciki ne ya sa ta kissima wannn abun na ganin gawar ta ɗora ta a cinya, wannan ya ƙara ruɓanya halin tsoron da take ciki hakan ya sa ta saka a ranta duk runtsi sai ta kuɓuta, jan ƙafarta ta fara tana daga tsugunnen amma sai ta ji gawar kamar ta fisge ta, hakan ya sa ta yi zaman ƴan bori a cikin ruwan fitsarin da ta yi ɗazu. bata damu da hakan ba ta shiga jan jikinta don ta gwammace ko da rarrafe ne ta bar gidan.

Gani ta yi yadda take jan jiki za ta gudu tare suke da gawar domin motsi kaɗan sai ta ga gawar ta biyo ta ma,ana daga Umma ta ja sai ta ga haɗe take ja da gawa, amma bata damu da hakan ba ta bari idan suka je bakin ƙofar gida ta san yadda za ta yi ta tsere in ya so ko da a ce a wajen ne ta bar gawar a ɗauke gawar daga baya a kan ta zauna cikin wannan balai,. In ban da ma son zuciya irin nata kuma saboda neman biyan buƙata a yadda take da masifar tsoron gawa ba ta taɓa.zaton har za ta zo wajen gawa ba.

Dakyar take jan jikinta saboda nauyin gawar Malam Kalla da take ja, a haka ta daure har ta fito tsakar gida inda su Abba duk suke yashe kamar matattu. Har lokacin gawar a ƙame take, sai dai kash! Umma tana shirin kama hanyar ƙofar gida sai ta ji gawar ta fara rimjayarta Umma a zuciyarta ta ce ko ana ha maza ha mata sai ta ƙwaci kanta. A haka tana ja har wajen ƙofar fita sai dai tana shirin yadda za ta yi ta ɓanɓare gawar sai kawai ta ji kamar wanda aka ɗaga su sama daga ida har gawar ta gansu suna tafiya luuuu ba au yi masauki ba sai a tsakiyar ɗakin inda suke a ɗazu wato gawa ta koma gurbinta inda aka ajiye ta gaka ma Umma ta koma mazauninta inda take a gaba gawa. Umma ganin hakan ya sa ta rushe da kuka mai sauti a fili tana faɗin

"Wayyo na ga ta kaina, Aliya kin haɗani da jaraba ke kina can ɗakin mijinki, ni yau bami da tabbas ma zan kwana a ɗakina, sannan igiyar aurena ma tana wala,ali" Ta faɗa jikinta duk yana karkarwa Allah ne kaɗai ya san halin tsoron da take. Kuka take wiwi tana rayawa a ranta shiknn asirinta ya gama tonuwa tun da gawa ba za ta ɓanɓaru daga jikimta ba, sannan wani babban tashin hankalin ma da ta tuna cewa matsawar gawar nan ba ta sake ta ba idan gari ya waye za a iya samun wasu jama,ar su zo sannan ya zama wajibi kowa ya ganta kenan asirinta ya tonu. Kamar ƙiftawar idanu sai ta ji an saki hannunta an kamo wuyan hijabinra da farko ma ta tsorata fiye da kima domin a tunaninta maƙogwaro za a shaƙe mata a kashe ta ita kuma ganin gawa muraran tana rike da ita ya ƙara saka mata tsoron mutuwa, nan suka shiga kiciniya iya da gawa har hijabin ya yage!.

Kamar daga sama ta ji wata murya ta ce
"Lubabatu!" Gaban Umma ya buga da ƙarfi har ba ta san lokacin da wata tusa mai balain ƙara ta kuɓuce mata ba sai ƙara ta ji bobott tana fitar da iskar. Jikinta kamar mazati haka yake rawa bata taɓa jin tsoro irin na yau ba gabaɗaya wani gumi ya wanke ta kamar an sheƙa mata ruwa, faɗuwar gabanta ta tsananta yanzu kam ta tabbatar sai yadda hali ya yi shiga motar mai taɓi, don ta ga gawa ba ta da niyyar sakinta wato babu niyya ango ya kwana da wando!.

Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, jin sunanta da aka kira kuma ba ta ga kowa ba sannan gawar dai ba ita ce take magana ba hakan ya sa Umma ta fara tunanin ko dai taɓin hankali ne ya samu ƙwaƙwalwar ta da za ta ji an kira sunanta.

Sunanta da aka kira a karo na biyu ta shiga amsawa a tsorace sai ta ji an ce

"A gobe da safe za a rufe ku a kabari tare da Malam Kalla, don haka kina da damar ƙarasa aikinki na zuba maganin, don wannan hannun ba zai taɓa.sakin jikinki ba sai dai a binne ku a tare"

Idanu Umma ta hau wurwurgawa jin wannan batun sai da hakan uanyi sanadiyyat ƙwacewar wata ƙaramar gudawa, ta sassauura murya a ranta tana faɗin to ko dai mala,ikan mutuwa ne ya zo mata a ɗakin Malam Kalla.

"Cikin faÉ—uwar gaba ta hau faÉ—in

"Yanzu zan tafi gida, dama don bai saka min ƙafa ba ne, wallahi tallahi ina da rai ban mutu ba shi ne ya mutu!" Wata irin dariya aka sheƙe da ita Umma sai kallon kowa na ɗakin take amma ta ga ba su ba ne.

Ta ji ana magana da murya kamar gargaÉ—i aka ce

"Ɗayan biyu ko dai a binneku tare ko dai a datse mki ƙafa da wuya sannan ne za ki kuɓuta" Umma tana hawaye ta kalli ƙafarta da take manne da gawa ta fara kwatanto yadda ba za ta yi kyan gani ba idan babu hannu da ƙafa, wato babu hannu ɗaya babu ƙafa ɗaya.

Kamar al,mara sai ta ga idon Malam Kalla guda ɗaya ya buɗe da sauri ra rufe nata idon tana son tuno wata addu,a da ta iya domin komai ya kwance mata, cikin ikon Allaj ta samu ta kamo sunan Allah Al,maliku ta shiga maimaitawa sai hawaye da suke zuba kamar an buɗe famfo. Tana cikin hakan kamar a mafarki sai kawai ta ji hannun gawa ya fara sakin wuyan hijabin da aka shake da alamar an fara sassauta riƙon, kaimi ta ƙara wajen ambaton sunan Allahn amma ko idanun ba ta buɗe ba, a haka sai da ta ji ƙafa da wuyan sun saki, sannan cikin faɗuwar gaba ta yi saurin jan mayafin ta rufe gawar, ba ta jira komai ba ta fara rarrafe saboda ta san a halin da take ciki yanzu ba za ta iya tashi tsaye ba haka ta rarrafo ta fito cike da tsoro da fargaba, tana fatan Allah sa haka ne bakin wahalarta, wato kar sai ta zo fita daga gidan a ƙara mayar da ita ɗakin.

Tana haki ta warci takalmanta a hannu ba don ma kar a ga baƙon takalmi ba, da babu abin da zai saka ta ɗaukan wani takalmi tashin hankalin da take ciki ma ya ishe ta. Haka ta taho gwiwarta tana zafi saboda yadda take cin karo da dutsi da kuma ƙananan itace suna cake mata gwiwoyin.

Sai da ta fita daga gidan ta sako bakinta a zauren gidan ta dage ƙarfinta ta ce
Chapter 95 · 0% Book details