← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 106

Sashe 15

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi dai bai ƙara bi takansa ba ya fara tafiya yana ta addu'ar dacewa, dacewar kuma ba ta komai ba sai ta sa'ar ganin Jidda tare da fallasa mata asirin zuciyarsa da fatan ta amince da shi....

*Akwai abaya gwanjo masu kyau da imganci akwai dila, akwai rabin dila, akwai kwatar dila akwai sayen É—aya*

*Sannan akwai zannuwan gado, labulaye, abaya mayafai* *kayan yara takalma lesuna atamfofi shaddodi hijabai amma su sabbi ne da sauransu*

*Sannan akwai magungunan mata, kama daga daka mai kyau da matsi ba wanda ake sanyawa ba wanda ake tafasawa a shiga, akwai maganin gyaran breast ga matan da nononsu ya zube ko ya yaƙune da wanda suke yi yaye da masu shirin yaye, akwai tsumi domin dawo da darajar ki wajen miji, akwai kuma sanyi wanda shi maganinsa dole ne don idan kina da sanyi ko kinnsha magani ba za ki ga kyansa ba.*

*Akwai mayuka na gyaran fata, kama daga wanda zai saka fari da wanda baya saka fari wanda shi iya fata zai gyara ya saki yi glowing, akwai shower gel, da sabulai da dai sauransu*

*Mai buƙata ta min magana ga no ta nan a ƙasa*

MAMAN AFRAH
09025576222
[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/C12RFYqXnWf36AhjVZWDw4?mode=ems_copy_t

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 7️⃣

*MAMY*

Da kallo ta bi bayan Mubin har ya ɓacewa ganinta tana jin babu daɗi a ranta, Zalika ce ta dawo da ita daga ƙaramin tunanin da ta tafi ta hanyar faɗin

"Mamy ki yi haƙuri kawai amma dai Baffa ba ya kyauta mana, tun muna yara bamu san daɗin hira ko zama inuwa ɗaya da mahaifinmu ba, gashi har mun girma abin yana mana ciwo amma hakan bata sauya zani ba"
Mamy ta É—an nisa ta ce

"Zalika kin san na yi iya ƙoƙarina wajen ganar da mahaifinku kuskurensa amma ya ƙi fahimta ko ya gane bare har na saka ran cewa zai yi aiki da shawarata, kin san da yawa wasu mazan suna ganin mata basu da tunanin sannan kasancewar an ce mace tana ƙasan namiji haka ya sa wasu mazan suke ganin mace ba za ta basu shawara ba su ɗauka, bare shi da yake ganin kawai duk abin da zan faɗa ma labarin ƙanzon kurege ne don shi a tashi fatawar idan ya ba ƴaƴa abinci da biya musu dukkan buƙatunsu shikenan ya sauke haƙƙi!"

Suna cikin tattaunawa suka ji mai gadi ya buɗe ƙofa, jim kaɗan sula ji shigowar mota wacce sun tabbata Baffa ne ya dawo domin lokacin dawowarsa ya yi.

Zalika ce ta miƙe tsaye da sauri, Mamy ta riƙo hannunta ta ce

"Ina za ki je?"

Zalika ta ce

"ÆŠaki zan je"

Mamy ta ce

"Mai ya sa?"

Zalika ta ce

"Kin san yanzu Baffa zai shigo ni kuma ba na son yake wannan É—aure fuskar" Jin furucin ta sai Mamy ta sakar mata hannu abin da ya ba Mamy mamaki da sassarfa Zalika ta bar falon tamkar wanda take gudun kar wani abun tsoro ya afka mata.

Karaf ƙaran buɗe ƙofar falon ya ziyarci kunnuwa Mamy wacce ta yi tsuru kamar mai jiran tsammani. Kamar yadda ta tsammata ɗin hakan ce ta kasance domin yadda ya turo ƙofar kamar wani kumurcin zaki haka ya shigo ran nan nasa a ɓace kamar an faɗa masa mutuwa, ko arziƙin sallama ba a samu ya yi ba, ƙofar ya mayar ya rufe sai da ya zo tsakiyar falon ya ja ya tsaya yana ƙarewa ko ina kallo. Har lokacin Mamy bata ɗago ta kalle shi ba.

Takowa ya fara yi sai dai ya zo falon sannan ya nemi waje ya zauna bayan ya ajiye ledar da ya shigo da ita, kallonta ya yi ya ce

"Baki ganin mutum ya shigo kika watsa yina?" Sai da ta yi yaƙi fa zuciyarta ganin bata faɗa masa wata magana da za ta ƙona masa rai ba, a hankali ta buɗe dashashshiyar muryarta ta ce

"Sannu da zuwa"

Kallo ɗaya ya juya ya mata ya ga ɓacin rai kwance a saman fuskarta sannan daga hakan ma ya fahimci tana cikin damuwa don yanayinta ya sauya kuma yana iya hango sawun hawayen da ya zuba a idanunta.

Sai dai kasancewarsa ba ya cikin mutanen da suka damu da damuwar iyalansu ba sai ya juya ya nufi hanyar da za ta sada shi da part É—insa, Mamy É—ago kai ta yj tana bin bayansa da kallo ji take kamar ta janyo shi ta buÉ—e kunnuwansa ta faÉ—a masa cewa ya gyara halayyarsa sai dai ta san wannan ba mai iyuwa ba ne.

Bayan tafiyarsa da mintina kaɗan ta tashi ta goge fuskarta ta bi bayansa duk da ta san bin bayan nasa ba ƙaramin matsala ba ne amma dai tana ƙoƙarin sauke nauyin haƙƙinsa da ya rataya a wuyanta matsayinsa na miji a gare ta.

Tana zuwa ta ɗan yi kamar minti uku a bakin ƙofar kafin ta tura ƙofar, taa shiga ta mayar ta rufe, Baffa da yake ɗaure da towel a ƙugunsa ya juyo ya ce

"Lafiya dai?" ,Duk da ba wannan ne karo na farko ba da ya jefa mata tambayar ba amma dai ta sosa ranta. Cikin sanyin murya ta ce

"Lafiya ƙalau, dama ruwan wanka zan haɗa maka"

Baki sake yake kallonta kafin ya ce

"Ikon Allah na zaune ya faÉ—i, yanzu akwai ruwa a famfo a banÉ—aki da komai sai an biyoni" Jin furucinsa sai ta juya cike da takaici ta fita, ledar da ya ajiye ta É—auka ta adana kayan bata san wane irin miji ne shi ba ko ta ce bata san wace irin zuciya gare shi ba da babu ruwansa da iyalansa.

Bayan an yi sallar magriba ya shigo gidan dawowarsa daga masallacin magriba kenan, sai da ya yi kamar minti uku da shigowa sai ga Mubin ma ya shigo don dama ta san ba zai bari ya bishi ba irin na ɗa da uba sai dai kowa ya yi tafiyarsa da ban. A kujera ya yada zango ya ɗauki remote ya sauya channel ya ɗan ƙara volume.

Ko da Mubin ya shigo bai tsaya a falon ba, tun da ya yi wa Baffa sannu da zuwa ya amsa dakyar a ciki-ciki sai ya wuce ya tafi É—akinsa ya kwanta yana danna waya. Zalika ma da ta idar da sallah ta zo ta ce

"Baffa barka da dawowa, an dawo lafiya"

Baffa ya amsa a taƙaice da

"Yawwa" Sum-sum ta koma ɗakinta a kan sawunta. Mai aiki ta shigo ta jera kayan abinci a dining kamar ba gobe, Mamy ta ɗaga waya ta kira Zalika da Mubin a kan su zo a ci abincin dare duk da cewa ana cin abincin ne kamar a gidan makoki amma babu wani raha ko nuna kulawa a tsakanin iyalan, don shi wanda shi ne ginshiƙin gidan bai bada damar hakan ba.

Kusan a tare suka shigo falon, lokacin Baffa yana waya da wani abokinsa duk ya cika falon da karaɗin wayar da yake bakinsa a washe kamar an biya masa kujerar makka, yana magana yana dariya har da ƙyaƙyatawa. Daga Mamy har yaran sai suka mayar da shi TV domin su sai su manta ma da ganin fuskarsa a sake sai dai idan ya bar gida ko yana waya ko a kasuwa wajen shagunansa ki ga yana ta raha da jama'a, haka ake yabonsa cewa mutum ne mai fara'a da sanin darajar mutane amma su dai iyalansa basu san wannan ba.

Yana gama wayar ya haɗe rai kamar bai taɓa wani abu dariya ba, lokacin da Mubin da Zalika sun koma kan dining sun zauna.

Cike da izza ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya mayar da hankalinsa kan TV ransa a haɗe kamar ba shi ne yake dariya da ƙyaƙyatawa a waya ba.

Sun jima zaune kan dining É—in amma Baffa babu alamar zai taso, Mamy ma ta je ta ja kujera ta zauna, sai kallon kallo suke a tsakaninsu. Cike da takaicinsa ta ce

"Baffan yara kai muke jira fa" Ta faɗa tana kallonsa, kamar ba zai furta komai ba sai dai ya ƙara tamke fuska ya ce

"Zan zo ai" Ganin haka sai Mamy ta shiga zuba musu abincin, farfesun kifi ne, wani fulas ɗin soyayyan naman kaza, ɗayan farfesun kayan ciki, abinci ma kala biyar dambun kuskus, soyayyar taliya, sinasir, funkaso, ɓarjen alkama, drinks ma iya ganinka sai wanda kake so, kallon kwanukan da Mamy ta bubbuɗe tana zuba musu abincin Mubin ya yi ya ga, ga komai amma kuma babu farinciki!.

An zubawa kowa har Baffa amma har lokacin babu alamun zai taso shi ko kaɗan bai san cewa iyalinsa suna buƙatar kulawarsa fiye da kayan more rayuwa da zai wadata su da su ba.

Kowa sai juya cokali yake a ciki, tausayin yaran ya sa Mamy ta ce

"Baffan yara abincinka fa zai huce na zuba"

BuÉ—ar bakinsa sai ya ce

"Ki ɗakko nawa abincin ki kawo min nan ba na sha'awar cin abinci a kan dining yau" Kamar wanda ya zuba mata ruwan dalma a kunne haka ta ji yayin shigar maganarsa, idanu ta runtse don bata son ganin fuskokin yaran. Mubin da Zalika kamar wanda suka haɗa baki sai kowanne ya tashi riƙe da plate ɗin abincin sa a hannu, ƙaran buɗe ƙofa shi ne ya ankarar da Mamy ta buɗe idanunsa sai kuwa ta ga wayam gabanta babu yaran sun bar wajen, mayar da idanu ta yi kan dining ɗin sai kuwa ta ga duka babu plate ɗin kowanne a cikin su.

Juyowa ta yi ta mayar da kallonta kan Baffa tana so ta ga ya zai yi tun da dai ta san ya san cewa yaran sun tashi daga wajen ne saboda ba zai ci abinci da su ba.

*SADIYA*

Sai da ta kama Kalifa ta ɗago shi sai ta shiga duba jikinsa a matuƙar kiɗime tana son ganin inda ya ji ciwo, kamar daga sama ta ji muryar mai mashin ɗin yana faɗin
Chapter 15 · 0% Book details