← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 106

Sashe 67

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka rayuwar gidan Nasir ta ci gaba da kasancewa sai abin da Meenal ta ce ake zartarwa don sun gama barbaÉ—awa Nasir magani a abinci ya cinye yanzu sai abin da ta zartar ake yi. Sadiya bata ma su take ba ta saka sana,arta a gaba duk yadda Meenal ta so takalar ta da faÉ—a bata kula ta sai ta yi kamar bata ji ba gorin duniyar nan babu wanda bata mata ba na cewa ai babu abin da bata sani va game da halin gidansu kawai bata biya ta su yi faÉ—a nr don tana tsoron komawa gida mahaifinta ba zai bari ba.

Hatta abinci ita take aunaw Sadiya tamkat ba ita ce uwar gida ba, sannan a ba Meenal kulin cefane ita a hanata, duk wani abu na bambanci ko rashin adalci shi ake yi a gidan, ita ta yi girki da gawayi ita ta É—ora a gas sannan ita Meenal tana da mai wanke wanke almajiri ita kuma Sadiya da kanta take yi.

Hajiya sai da ta ga dankali da kayan shayi ya ƙare kaf sannan ta ce Nasir ya siyo wani buɗar bakinsa ya ce

"Hajiya yanzu idan akamce zannke siyan ƙwai doya dankali da kayan shayi ruɓi biyu gaskiya za a samu matsala ga mota ta yanzu tana yawan bani matsala sai kuɗin gyara take ci sannan yanzu Meenal bata taɓa yin girki babu nama"

Hajiya ta ce

"To mai kake nufi yanzu?"

Nasir ya ce

"Sai dai idan har kuna sona dankalin su Husna suke zuwa suna aikatawa sai Meenal take É—auka musu suna kawo muku kamar yadda Meenal ta tsara, amma na san ita Meenal ba za ta yarda ta girka muku ba" Da bala,i Hajiya ta ce

"Bata isa ba dole ta girka don na fahimce ka na rashin siya a can gidan da kuma nan ni ma bana so ka wahalta aljihunka saboda auren ƙanannka amma dai tun da ita uwar muyane ba za bari a dafa a nan a bata ba dole ta dafa" Nasir jikinsa ya yi sanyi hakan ya sa ya ce

",Ba komai kawai zan saya muku " Yana barin gidan ta kira Meenal tana É—agawa ta ce

",Hajiya ya ne? Ƙalau dai ake kirana" ,Ran Hajiya ya sosu da ta ji wannan batu amma sai ta ce

"Fitsararriya mai ido a tsakar ka, ina so in ƙara tabbatar miki da cewa ɗana ni na haife shi dole ya mini abin da nake so gashi can zai sayo mana kayan kari in kin isa mu zuba ni da ke!" Tana faɗar hakan ta kashe wayar ta bar Meenal da waya a kunne. A ƙufule Meenal ta kira Nasir ta ce

"Yanzu kai baka isa da ƙannenka ba saboda na ce suke zuwa suna mana girkin safen kawai shi ne za ka je ka siyo wasu kayan saboda ka nunawa ƙanennka ban isa da mijina ba su rainani na gode" Tana kai wa nan ta fashe da kukan kissa ta kashe.. Nasir ya kira ta yana ta aikin lallashi ya ce ya fasa siyowa zai tilasta su Husna zuwa.

Kawai Hajiya sai kiran Nasir ta gani tana É—agawa ta ce

"Yawwa ka kira a kan gaɓa dama yanzu nake son kiranka in ce mun fi son dankalin mai manya manya douar kuma sabuwa muke so ta fi daɗi" Nasir ya ce

"Hajiya ya za a yi a ce ni ban isa da su Husna ba bayan an ce babban wa uba, kawai suke zuwa gidana suna girkawa" Salati ta hau yi ta kashe suka hau jajantawa ita da su Husna Hibba sai É—urawa Meenal ashar take yi suna cewa ta mallake musu É—an uwa Hajiya kuwa har da kukan takaici wai an fi ta iko da É—a.

Washe gari suka ƙi zuwa sai Hajiya ta yi musu tuwon shinkafa suka ci kaɗan sun saba da kayan dankli da kwai da shayi mai kauri yau kuma sai bunu suka sha wato lipton.

Haka suka yi ta mita wata washe garin saj suka kwashi ƙafa suka tafi gidan sun daɗe zaune a ƙofar ɗakin Meenal suna jiranta kafin ta fito a shelaƙe ta basu kayan da za su yi aikin kuma din takaici ta ce kar su taɓa mata cooker gas ta ce su yi da gawayi haka suka yi wahala suka gama ta zo ta ɗauro musu kayan shayin kamar wani ƙullin roƙo kuma a waje ɗaya ta haɗa madara da milon. Basu gama sanin bata da mutunci ba sai da ta ce sai da su koma su kawo kwanon sa za a zuba ko ta zuba a leda haka suka tafi suna ta tsene mata har da uwar ta sai da suka tsinewa haka ma Hajiya ta ringa zaginta da ta ga kayan shayin ta ɗakko wani ramgameman fulas ta basu, suna kaiwa Meenal ta tsakura musu wani a ƙasan kwano ko Hajiyar ba zai isa ba bare su.

Haka suka tafi ransu duk a ɓace sai da suka je sai suka fara zancen da a ce Sadiya ce ta samu wannan damar da ba za ta musu haka ba.

Kullum haka suke zuwa su girka ta basu su tafi dama yanzu da kwano suke tafiya Sadiya kuwa babu ruwanta da sabgarsu ko Nasir rabon da ya taka ƙafarsa a tsakiyar falonta ma tun kafin Meenal ta tare bare a yi zancen biyan haƙƙi. Ga cikinta ya tsufa tana dab da haihuwa. Wata ranar laraba sai kawai Meenal ta ce Nasir ya sa maau aiki su buga kicin na langa langa Sadiya ta kwashe mata kaya daga kicin haka kuwa aka yi, Sadiya ta kwashe komai nata, don ita yanzu in banda gayan kayan abinci babu abin da ake bata a gidan shi ma ba ishashshe ba.

Yanzu da ta lura Kalifa yana ganin dankali da ƙwan da ake soyawa sai ta saya kokai ta ajiye su ma take soya musu tun da Allah ya rufa mata asirin da sana,ar da take yi wanda wannan abu shi ne ya tsayewa Meenal a rai don ko buga gidan aka yi za a saya abu ta ringa masifa tana cewa ana katse mata bacci.

Yau lemon mango tun safe ake saya haka ya sa gabaɗaya ma kayan sanyin suka ƙare da yake tana da ƙanƙara kuma akwai nepa sai ta zauna ta haɗa wani tana zubawa a robobi. Gidan da aka buga ya sa ta yi magana aka ce ƴan nepa ne bill ne muka kawo, ta je ta karɓo yana nannaga mata idan ba a biya yau ba gobe za su dawo su yanke.

Za ta zuna sai Meenal ta fito a gadarance sanye take da baƙin wando da ya kamata tree quarter da farar riga kai babu ɗan kwali sai wani kaɗa jiki take tana fitowa ta ce

"Kawo wannan bill ɗin tun da ba ɗakin ki zai shiga ba tun da ma ke ai baki da bakin kwana a gidan nan" Sadiya bata ce komai ba ta ba Kalifa ta ce ya kai mata, haka ta karɓa ta shige ɗaki.

Ko da ya dawo gidan suna zaune da daddare ta yi filo da cinyarsa sai ta ce

"Ga bill can Æ´an nepa sun kawo, sun ci gobe za su yanke in baka biya ba"

Ya yi shiru ya ce

"Ni yau kasuwar nan bata yi kyau ba" Wani daÉ—i ta ji don an zo wajen da take fatan a zo

Sassauta murya ta yi cike da kissa ta ce

"Honey ni kana bani mamaki ya za a yi a ce wai kullum kai kake biyan nepa" Da mamaki ya ce

"Wa zai biya min"

Ta ce

"Sai kuke raba daidai da Sadiya ai ta fi kowa morar nepa a gidan nan, amma yanzu idan ka tunkare ta da maganar ba lallai ta bada kuɗi ba kawai idan ƴan nepa sun zo sai su tanke mata ɓangarenta in ya zo nan gaba idan aka ce ta bayar ba za ta yi musu ba" Shiru ya yi sai kuma ya miƙa mata hannu suka tafa yana jin lallai shawarar ta yi daidai da ma,ana sai ya ce

"Wallahi ƙwaƙwalwarki tana aiki ban taɓa wannan tunanjn ba" Murmushin cin nasara ta yi.

Da safe kafin ya fita ya bata kuɗin nepa ya ce idan sun dawo ta basu, amma sai ya yanke wani kaso daga kuɗin ya ce ta ce su yanke ɓangaren Sadiya.

Sadiya yau tun da almajirinta ya ɗauki kayan yake dawowa yana ƙarawa gashi daga unguwa ma sai zuwa ake nan da nan ya ƙare tas. Ta zauna ta sake wani ta jera a frige. Ta gama zubawa kenan sai ta ji ana bugawa da aka yi magana aka ce ƴan nepa ne a kawo kuɗin wuta, Meenal ta ɗauki kuɗin ta je da takardar ta basu, ta musu bayani babu musu suka yanke ɓangaren Sadiya, Sadiya tana tsakar gidan tana jin ƙaran tvn Meenal kasancewar ta ƙure ƙara, amma tana shiga falonta sai ta ga ƙwayayen basu kawo ba ta duba ko ina ta ga babu nepa ta ƙara fitoea ta ci gaba da jin ƙaran tv a ɗakin Meenal a nan take ta fara tambayar kanta

"Ya haka?"

ALIYA

Amatullahi ce take mata alama da ido alamar ta amince a take ta shiga kaɗawa bakanya kai, sai kuma suka tambaye ta kuɗin aikin ta ce sai sun kawo cokalin an yi aikin tukunna. A tsorace suka baro wajen suna tafiya har suka fito daga surƙuƙin dajin suka zo bakin titi sun daɗe suna tsaye suna tattaunawa Amatullahi tana faɗawa Aliyar kawai daga nan ta wuce gidan Jidda ta san duk yadda za ta yi ta ɗakko cokalin tun da gobe dole su dawo su kawowa bokanyar cokalin.
Chapter 67 · 0% Book details