← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 106

Sashe 39

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya fita wajen Hajiya ya je bayan ya karya da break fast mai rai da lafiya, su Sadiya kuwa waina ce ya siya musu ta ɗari uku ba don ta ishe su ba kasancewar gidan kakar da ta je bata yi tuwo ba shi ma sai da ya gama mita sannan ya sayi wainar. Hajiya ya korawa bayani jin haka kuwa ta yi uwa da makarɓiya cewa ai dole ma ya bar Sadiya ta yi sana'ar ba don wai tana son ƙwatawa Sadiya ƴanci ko haƙƙi ba sai don ta nuna masa alfanun hakan zai ke ƙaruwa ne tana bauta masa a gidan, sai lokacin ya ji sanyi a ransa da ya ji shi ma zai ƙaru da sana'ar don shi ya sha'afa da cewa ya ce mata ma ta kama sana,a kawai dai da ya ji cewa har frige xa a saya mata bayan ya ɗauka sana,ar ƙarama za ta yi yadda daga ya sakar mata da abubuwan gidan jarin zai karye katsak saboda mugunta.

Ta ji daɗi da ya amince ta yi ta masa godiya kamar ta ari baki, shi kuma a ransa yana gani kansa ya yi wa gata. Bayan kwana uku da yamma sai ga mai baro da Kaka, mai baron ne ya fara kawo frige ɗin da ledar pure water goma sai kuma Kaka ta zo a napep frige ɗin yana da tsayi amma ba sosai ba yana da murfi biyi sama da kuma ƙasa sannan dama da yake na amarya ne bai ji jiki ba zoɓo kwano uku da su kayan haɗa zoɓo har da kayan ƙamshi, sai kayan haɗin mangon da leda da kuma jarkokin lemo wanda za take zubawa a ciki su ma cikin buhu. Har da kukanta tana ta yi wa Kaka godiya, haka Kakar ta musu sallama ta tafi. Sadiya ta wanke frige ɗin tas ta goge ta ta jona dama akwai nepa ta jera pure watern a ciki, ta rasa inda za ta saka ranta don daɗi.

Wani almajiri da ya yi bara ya faɗa mata makarantarsu bata da nisa da gidanta, shi ta aika maƙota ta ce ya faɗa musu abubuwan da za take siyarwa, sannan ta ce masa zai ke zuwa yana mata talla ya amince cike da murna, don dama idan suka yi karatun safe sai a tashe su ƙarfe tara, kowa sai ya tafi bara sai kuma karatun yamma da na dare, sai yance zai ke mata tallar daga ƙarfe tara zuwa ko ƙarfe uku ne, ta ji daɗi haƙiƙa Allah ya karɓi addu'arta don yaron yana da hankali. Ko da ta faɗawa Mama da Baba a waya fatan alkairi suka yi Baba har da cewa

"Sadiya to ita amfanin sana'a dama don kake yin alkairi a ciki, don haka idan ana samun kar ake mantawa da iyeye don su saka albarka" Jin haka ta gane mai yake nufi sai ta ce masa

"In sha Allahu Baba"

Nasir ko da ya dawo ya ga sha tara ta arziƙin da Kaka ta kawo a ji daɗi, don haka jarkokin da ta wanke da soso da klin ta zuba zoɓonta mai daɗi ya ji kayan haɗi, sannan ta haɗa mango ɗin ma da kayan haɗin mango ta saka kala, sosai ya yi tamkar kana sha lemon mango ta kamfani har ya fi na wani kamfanin ma daɗi!.

Bayan kwana biyu sana'a ta kankama, ƙanƙarar yara haka yara suke zirya daga unguwa da kuma islamiya idan an fito musu tara, ga almajirin bashi da wasa daga ya fita da kayan kamar wanda yake rabawa kyauta, don duk wanda ya sha sai ya yaba da daɗinsa. Kafin meye wannan sana'a ta fara ƙarfi mazan unguwa sai su ba yara su siyo musu babu mai zuwar masa gida, sai ya zamana yanzu Sadiya kawai ta mayar da hankalinta kan sana'ar ta kuma duk abin da take so haka take fitarwa ta yi abinta sana'a mai daɗi ko wulaƙancin da Nasir yake mata yanzu ya ɗan rage saboda dama wani don za ta ce masa ya mata wani abin ne.

Sai dai wuyarta ya shigo kawai frige yake buɗewa ya ɗauka ya sha, daga an jima ya ƙara ita kuwa ko a ka bata kawo shi, tun da ta san duk abin da zai yi sai ta fita, don kayan sana'ar ruwa suna da riba sosai.

Bayan sati guda tana zaune bayan ta gama ɗura zoɓo da yamma, da yake yau ya ƙare tas har ana nema, yanzu pure water ne a ciki da zoɓon da ta saka yanzu, da sallama Nasir ya shigo bakinsa yana washewa, abin da ya bata mamaki har da ɗauka Kalifa shi kuma yaron ya ƙi sakewa da shi kasancewar ba sabawa ya yi da hakan ba. Mukulli ya ɗaga a hannunsa yana karkaɗa mata bayan ta masa sannu da zuwa duk da ta ga yau ya dawo da wuri sai dai tana mamakin fara,arsa. Cike da alamun tambaya a fuskarta ta ce

"Mukullin mene ne?"

Ya ce

"Sabuwar amarya na yi wato mota" Ya faɗa yana washe baki, sosai ta ji daɗin maganarsa, ba wai don ya ce ya yi mota ba, a,a sai don fara,ar da yake ko yaya ɓacin rai ko nuna isa da gadara basu da wani alfanu ga namiji yake yi wa iyalinsa.

Sosai ta nuna farincikin ta, dama ta san yadda kasuwa take gara masa ai yana samu sosai kawai dai don abin a zuciya yake wato mammaƙon nasa a zuciyarsa yake. Hijabi ta saka suka fito ƙofar gidan motar tana sheƙin sabunta dark blue ya juyo ya ga yadda take ta fara'ar sai maganarsa ta katse mata hanzarin fara,arta ya ce

"Na sayi motar nan ne saboda Meenal, Meenal ta faɗa min tana son duk inda za ta je in kaita a mota, sannan bata son ƙawayenta su rainata su ce mijinta bashi da mota!"

*BABA*

Gabaɗaya ya mayar da hankalinsa ga son banza, don yanzu kowa ya gane yana jin daɗin a masa abinci mai daɗi, don haka yanzu da daddare idan yana bacci cikin dare za a lallaɓa wata daga cikin ƴaƴan ko matan za ta sace mukullinsa, a je a auni shinkafa a store a mayar a rufe, don da abin nasu ma ya yi tsamari sai a auni kwano uku biyu a dafa a gidan kwano ɗaya sai a siyar a yi cefane da nama ko kifi a yi girki lafiyayye kowa ta ci Baba a yi masa zubi ya ci yana santi da saka albarka, har yau bai san cewa tanadin da ya yi domin ya siyar ba ne ake kwasa ana ci tare da shi.

Yanzu ma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen bin malamai da masu siyar da maganin gargajiya yana siyan maganin farin jini domin ya samu ya aurar da ƴaƴan nasa, malamai kuma yana sakawa su yi roƙon Allah, amma shiru kake ji malam ya ci shirwa da alama dai addu'ar ta samu jinkiri ne, babban abin da ya ƙara tada masa hankali ma yanzu Sumy da Aisha da suka kammala karatun su na secondry yanzu kam waɗanda yake son ya aurar sun yi yawa. Shi ya sa ba ya ma son Sadiya ta kawo ƙorafi a ganinsa tun da dai ita Allah ya sa ta samu miji to duk wani ƙalubale ta haƙura ta rungumi ƙaddara!.

*MUBIN*

Da sanɗa ya shigo babban falon yana waige-waige sai dai ganin dalon wayam kamar yadda ya yi tsammani hakan ne ya sa ya ji ɗan daɗi a ransa, domin a ganinsa lokaci ne da kowa ya yi bacci idan ya shige ɗakinsa to zai zamana ko ma mene ne zuwa safiya Mamy ta huce daga fushin don ya san sai dai Mamy don Baffa ko a kwalar rigarsa. Takalmansa a hannu ya yi saɗaf-saɗaf kamar daga sama ya ga hasken fitila ya manaye falon, abin ya masa bazata hakan ya sa ya ji gabansa ya buga da ƙarfi, sai jin muryar Mamy ya yi kamar yadda ya tsammata ta ce

"Mubin daga ina kake?" Shiru bai bata amsa ba ta sake cewa

"Mubin irin tarbiyar da na baka kenan? Wannan ne sakayyar da za ka mini, maimakon ka zama ɗa nagari mai biyayya da bin umarnin iyaye, yi na yi bari na bari amma shi ne duk fadutukar da nake yi kake son watsa min ƙasa a ido" Ta faɗa lokacin zuciyarta ta fara karaya saboda tausayin kanta a nata ganin ba uwa ce kaɗai za ta kula da tarbiyae ƴaƴa ba haɗaka ya kamata iyaye mata da mazan su yi tarbiyar ƴaƴan amma shi ya bar mata komai ta yaya hakan zai yiwu gashi yaran suna neman kangare mata. Mubin cikin inda-inda ya fara maganar da rashin gaskiya ya hana shi furta abin da yake gaskiya ne dama hausawa sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake.

*JIDDA*

GabaÉ—aya Ibrahim ya rikita mata lissafi ya sa duk tana jin wata muguwar kunyarsa, ya sa tana jin ashe ita ma tana da wani matsayi don yadda yake yi mata jin ta take tamkar wata sarauniya.

Ta tafi gajeran zancen zucin nan na wucin gadi kawai sai ta ji yatsansa a saman leɓɓanta, abin da ya dawo da ita hayyacinta kenan, tana dubawa sai ta ga tsokace ya gutsuro yake ƙoƙarin bata a baki. Cikin wata murya mai kwantar da zuciya ya ce

"Idan baka ci naman nan ba kuka zan miki Jiddanah" Yanayin yadda ya fara bata ga alamar wasa a tattare da shi ba hakan ya sa ta danne guntun kunyar ta buÉ—e masa bakin ya saka, yana sakawa ta saka hannunta na dama ta rufe bakin da tafin hannunta saboda duk kunyarsa take ji kasancewar rashin sabo. Idanunsa ta ji yana yawo a jikinta alama ce ta ya tsare ta da kyawawan idanunsa hakan ya sa ta kasa É—agowa ta kalle shi shi kuma ji yake tamkar ya mayar da fuskarta cikin idanunsa ya zamana ita zai ke kallo a koyaushe.

Muryarsa tana sarƙewa saboda yanayin da ya tsinci kansa na kasancewa da ita a waje guda kuma matsayin mamallakiyarsa hakan ya sa ya ce
Chapter 39 · 0% Book details