← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 106

Sashe 2

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aisha kukan me kike mai aka miki?" Aisha wacce ta ja ƙasan hijabin ta ta rufe fuskarta hannun ta riƙe da jakar buhu irin wacce ake ɗinkawa da buhu, sanye take da farar riga da wandon uniform sai farin hijbi wanda aka masa tattara da koren yadi a ƙasan ƙafar wandon ma akwai koren, bata ba Mama Talatu amsa ba, cike da tsawa Baba ya ce

"Kee! Kukan uban me kike?" Da sauri ta cire hijabin fuskarta saboda ta cikin yadin hijabin nata wanda bashi da kauri kasancewar yadin ba mai tsada ba ne, ta haka ta shigo gidan sai dai bata kalli saitin inda su Baban suke ba shi ya sa bata san yana nan ba, ita kuma Mama Talatu da yake daga nan gefen da take tsaye kusa da hanyar zauren ne shi ya sa Aishar ta ganta.

Mama Bilki wacce take ɗaki tana jin kaf abin da yake wakana a gidan, tun da in da sabo sun saba da wannn halayyar ta gidan duk da kasancewar kowa a gidan shi yake nemawa kansa abincin rana damkarin kumallon safe idan tuwo bai kwana ba, domin iya tuwon dare ne kawai Malam ɗin yake bayarwa a gidan shi ma wataran idan ya hana kuɗin kayan miya sai dai wacce girkin ta ne ta siya ta yi haka za a yi miyar babu maggi sai dai kowa in an zuba masa ya nemi maggi dunƙule ya barbaɗa, abincin rana kuma sai ranar da ya ga dama jifa-jifa yake bayarwa.

Ba wai don bashi da halin wadata su ba, sai don sarewa irin tasa shi a tashi fatawar ƴaƴa mata kawai da ɗakin miji suka dace domin mijin ne ya dace ya ɗauki ɗawainiyar mace, shi ya sa yake ta fafutukar ya ga ya aurar da su sun bar gabansa, babu tunanin samun nagartaccen miji. Komai sai dai uwa ta ciru ta ƙullu ta nemawa ƴarta ko su ƴaƴan su nema shi abu ɗaya yake da buri kuma yake fata shi ne ya haifi ɗa namiji, a ganinsa idan namiji ne zai taya shi ɗaukan ɗawainiya amma mace yana ganin ita sai dai ya nemo ya basu ba ya tunanin haƙƙi ne Allah ya ɗora masa.

Aisha cike da jin nauyin mahaifinta kuma tana jin kunya sai ta kasa faɗa masa dalilin kukan nata, ƙara zaburowa ya yi yana kumfar baki sai ga Mama Bilki ta fito daga ɗaki ta ce

"Wai mene ne kike neman mayarwa da mutane gidan makoki, ke ga mai arahar hawaye?" Jin tsawar da Mama Bilki ta mata da kuma wacce Baban ya yi sai ta sunkuyar da kai hawayen yana zuba ta ce

"Wai don na ɓaci shi ne ƴan ajinmu suke min dariya" Ta faɗa tana jin ɗacin abin a ranta, sai lokacin ƴanmatan kowacce ta mayar da kallonta jikin Aisha, domin sun fahimci matsalar shi kuma Baba bai ma gane inda maganar ta dosa ba hakan ya sa ya ce

"Ba dole suke miki dariya ba tun da sun ga sakarya, ke da girmanki amma kuka ba ya miki wahala" Mama Talatu cike da tausayin Aishar ta ce

"Haba Aisha ai da kin saka ƙunzugu a jikin ki, amma kya tafi cikin mutane a haka kuma kin san dai ƙawaye da sheƙiyanci" Wani kallo Mama Bilki ta jefawa Mama Talatu ta ce

"Sai aka ce miki bata saka tsumma ba, to ta saka, zo ki wuce ki je ki gyara jikin ki" Mama Bilki ta faɗa rai a ɓace saboda gabaɗaya haushi ta ji an tsinka ƴarta, Aisha tana fara tafiya kowa ya juya ya bi bayanta fa kallo, ashe ta saka wani ɗankwalin atamfa ta ɗaura a ƙugunta hakan ya sa ba a ganin ɓacin da jikin nata ya yi.

Mama Bilki cike da takaici ta ce

"Ai wallahi sha'anin gidan nan sai a hankali wallahi, a ce wai sunan yara suna da uba amma kamar marayu, a ce ubansu yana da hali amma ba zai É—auki É—awainiyarsu ba sai dai ya ce kowacce ta É—auki É—awainiyar kanta, to ko namiji ne aka ce ya É—auki É—awainiyar kansa ai an buÉ—e masa hanyar yin abin da ya ga dama varw kuma Æ´a mace da ake son killace ta a yi takatsantsan da rayuwar ...

Kafin ta kai aya Baba ya tari nunfashin ta da faÉ—in

"Sannu uwar kinibibi, yanzu saboda rashin godiyar Allah sai aka ce komai sai uba ya yi wa yara? Ita uwarsu mene ne amfaninta? Kun mata kun É—auki namiji kamar bawa komai shi zai yi a gida ba za ku taimaka ba, in banda son kai yanzu audugar wata-wata ma ni zan saya musu?" Mama Talatu ta ce

"Malam ai ba a ce wai lallai sai ka saya auduga ba amma akwai wasu ɗawainiyoyin da dan har ka ɗauke musu to zai zamana kuɗin da za su yi ɗawainiyar sai su sayi audugar da ƙananun abubuwan, amma a ce mace budurwa ita za ta yi wa kanta komai, hatta omon wanki da sabulu mai na shafawa ita za ta yi kai hatta ciyar da kanta ita za ta yi haba malam Allah ne fa ya ɗora maka nauyin iyalinka daga kan ƴaƴa da mata...

Wata harara da yakr jifanta da ita ya sa ta yi shiru ya ce

"Wato in mutu da ɗawainiya ni kullum in ƙare a tsaye? Ai shi ya sa da a ce maza na haifa da tuni ina ɗaki ina bacci da munshari su kuma suna can suna nema, in za ku kama sana,a kowa tashi ta fishshe shi.

Mama Sa'ade ce ta fito daga É—aki tana hamma ta ce

"Ai lamarin gidan nan sai addu'a amma dai kam ana fama"

Baba kallon Æ´anmatan da suke gabansa ya yi ya ce

"Kai ku tashi ku bani waje kowacce ta bar wajen nan, kuma maganin da kuka sha na farin jini duk wacce ta amayar min shi wallahi sai ranta ya ɓaci, mu ga zuwa gobe ko maganin zai yi aiki a fara min kayin neman aurenku" Ya faɗa yana miƙewa tsaye ya gyara rigarsa ya juya ya nufi hanyar ɗakinsa yana ta ƙananan maganganu da babu wanda ya ji mai yake cewa amma da alama faɗa ne yake.

Mama Talatu ce ta É—an matsa kusa da Mama Bilki ta ce

"Bilki don Allah yarinyar nan ki saya mata audugar mata, wallahi babu daɗi jinin al'ada yake kunyata mace kaima babba da yaya bare kuma yaro duk sai mutum ya ji ya tozarta duk ya rasa sukuni, in har baka kintsa kanka ba sai kake ta tsarguwa ko ka ɓaci... Kafin ta ƙarasa Mama Bilki ta ɗaga mata hannu tana faɗin

"Talatu bana son iyayi, idan ba za ta saka tsumma ba to ta zauna a haka, ita ba shegen girman kai ba idan aka ce ta fita waje ta soya awara ta siyar sai ta ƙi wai bata son talla, waye ubanta? Uban nata da ba ya iya ɗaukan ɗawainiyarta tun da ba za ta zage ta nema ba ai ta yi ta ganin takaici" Tana faɗar haka ta juya ta kama hanyar ɗakinta.

Mama Sa'ade baki ta taɓe ta juya ta shige nata ɗakin, Mama Takatu a zuciyarta ta ce

'Wannan rayuwa ban san ina za ta je da mu ba, duk wanda ya ce Æ´a mace ta É—auki É—awainiyar kanta ai hanyar lalacewa ya nuna mata, yanzu a ce uwa ba za ta siyawa Æ´arta mace auduga ba, idan ba wata sana'a yarinya take yi ba ina za ta samu kuÉ—in siyan auduga duk wata? Wata ma sau biyu take yi a wata É—aya, gaskiya akwai sake a lamarin gidan nan, a ce mutum ya É—auki É—awainiyar kansa Allah kyauta' Ta faÉ—a a zuciyarta tana nufar É—akinta

Mama Talatu tana shiga ɗakin ta sai ta samu Sadiya tana zaune ɗanta Kalifa ɗan shekara biyu yana kan cinyarta, abin mamaki kuma Sadiyar kuka take. Sai dai da alama shigowar Mamar ya yi wa Sadiyar bazata saboda saurin kawar da fuska gefe ta yi tana sharar ƙwalla da alama bata ma son Mama ta ga hawayen nata. Gaban Mama ne ya faɗi, zuciyarta ta tsinke tana fatan dai ba wata matsalar gidan auren Sadiyar ba ne ya saka take kuka, ta rasa wane irin aure ne wannan aka yi wa yarinyar nan wanda koyaushe cikin ƙunci take, da damuwa dama ta lura tun shigowarta kamar ma fuskarta a kumbure sannan kana ganinta ka ga waccr take cikin damuwa kuma babu alamar nutsuwa a tare da ita!.

MAMAN AFRAH
09025576222
[10/11, 9:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/IQU3wL7NUTCCqrbtxkJaaz?mode=ems_wa_t

*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*

BOOK 1

PAGE 2️⃣

*MAMA TALATU*

Zuciyarta sai ta mata nauyi da ganin halin da ƴarta take ciki, a hankali ta ƙarasa shigowa falon ta zauna a ƙasa kusa da Sadiya, tana mai sauke wata nannuyar ajiyar zuciya, ranta duk babu daɗi duk da wani lokacin tana jin farinciki cewa ƴarta ita ce wacce take da aure, amma dai auren wannan wani lokacin ma da shi da babu duk uwar ubansu ɗaya, dama ta san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, mijin Sadiya dama irin mazan nan ne da basu san darajar mace ba, shi ya sa yake wulaƙantata uwa uba kuma yadda aka yi auren, daga ganin Sadiya ya ce yana so a ranar farko da ya fara zuwa ƙofar gidansu, a ranar ne mahaifinta ya ce ya turo manyansa babu wani bincike da yake dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Haka aka yi biki babu wata fahimtar juna, babu bincikar halayensa gashi nan yanzu an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo.

Hannu Mama ta kai ta dafa kafaÉ—ar Sadiya ta ce

"Halima kukan mene ne kike yi?" Ta tambaya tana jin tsoron furucin da Sadiyar ,a ta yi a gefe É—aya tana fatan cewa Sadiyar ta faÉ—a mata wani abu daban amma ba matsalar gidan auren ta ba, ita burinta bai wuce Sadiyar ta zauna a É—akinta duk wuya duk runtsi.
Chapter 2 · 0% Book details