← Book details Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 106

Sashe 103

Ruwa Cikin Cokali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk duniya babu wanda ya isa ya hanani aura masa tun da ƴata ce tun da ai ba a ce in ta aure shi ta koma kafirci ba kuma shi ma ya ce babu ruwansa da addininta kowa ya yi addininsa kin ga kuwa babu gudu babu ja da baya, tun da kaf unguwar nan babu wanda ya zaɓe ta sai shi kuma ba zan aurar da sauran ƴan uwanta ba ita ta zauna mini a gida domin haka babu gudu babu ja da baya!"

MAMY

Rai a matuƙar ɓace ta ce

"Dakata Zalika!. Kar ki raina min hankali mana, kenhar kin isa ki yinwasa da hankalina Zalika? Ita ƙawar taki ta rasa inda za ta yi ajiya sai a jakar ki, ta rasa mai za ta ajiye a jakar ki sai ƙwayoyin hana ɗaukan ciki?"
Zalika ganin Mamy ta rikice mata tana son janyo mata ruwa sai ta marairaice ta ce

"Wallahi Mamy ki yarda da ni ba ƙarya na miki ba, ko kaɗan ba da wata manufa ta ajiye ba, yanzu Mamy ni kika zargi da shan wannan maganin ko kuwa?"

Mamy a harzuƙe ta ce

"Dole ne na zarge ki Zakika saboda kin yi abin da za a zarge kin, shin idan babu rami mai ya kawo rami? Tun yaushe kika sauya Zalika mai zai sa na ƙi zarginki ai wannan ba ma zargi ba ne na tabbatar"

Kuka Zalika ta fashe da shi ta ce

"Mamy ko da wani zai zargeni na ɗauka ke ce za ki shaideni, kuma wannan abu ne da baki da tabbaci a kansa, kuma ko a musulunce zargin zina fa lamari ne baba kuma mai girma da yake buƙatar tabbatarwa, saboda ita zina ko za a zargi mutum sai an tabbatar sai an ga mutum turmi da taɓarya sannan sai an tara shaidu mutum ɗaya ba ya wadatar da ganin mazinaci...

Hannu Mamy ta ɗaga mata alamar dakatarwa, domin a furucin Zalika duk inda ta ambaci kalmar zina ran Mamy zafi yake sannan sai gabanta ya faɗi, ita a rayuwa babu kalmar da take jin nauyin furtawa a harshenta sama da kalmar zina, ta tsani kunnuwanta su saurari kalmar saboda nauyinta da kuma ƙazantarta don zina abun ƙyama ce, mai yinta abun ƙyama ne kuma abin a nisanci mu,amala da shi ne saboda zina Allah cewa ya yi ko kusantarta kar a yi bare a aikata ta.

Mamy ta ce.

"Zalika ni na haifeki ina so ki sani duk wani lafazi naki a tafin hannuna yake, na fi ƙarfin ki rufe ni da murfin ƙarya da yaudara, ina so ki faɗa mini tsawin wane lokaci kika ɗauka kina wannan mummunar ɗabi,ar?"

Zalika ta É—aga idanu ta kalli Mamy ido cikin ido ta ce

"Mamy ki yarda da ni ban taɓa aikatawa ba idan kuma har kina kokwanton maganar ni zan kira wacce ta saka maganin ta zo har gida ta miki bayani" Ta faɗa tana kuka wiwi

Nannauyar ajiyar zuciya Mamy ta sauke tana jin wani zafi a zuciyarta ta ce

"Ba na buƙatarta duk bakinku ɗaya, kafin ta zo kun gama tsara yadda za ku faɗa mini ƙaryar da kuka shirya, za ki faɗa mini gaskiyar yaushe ne kika kai matsayin da har kika fara amdaninda ƙwayar hana ɗaukan ciki, ɗabi,ar da take lalata tarbiya ɗabi,ar da take lalata suna kina mace amma za ki lalata rayuwarki ki cuci kanki ki cucemu sannan ki bar wa ƴaƴanki baƙin fentin da har jikokinki sai abin ya shafa"

Baki Zalika ta buɗe za ta ci gaba da faɗin maganar da take alamta musu da zargin Mamy hakan ya sa zuciya ta ɗauki Mamy ta wanke fuskarta da ƙwararan maruka har biyu. Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Mamy da Zalika, Mamy tana hakin baƙinciki kamar wacce ta yi tseren gudu yayin da Zalika take dafe da kumatun ta.

Mamy ta ci gaba da faÉ—in
"Abin da kika yi irin na iyaye masu sakaci da tarbiyar ƴaƴansu ne duk da a lokuta da dama idan ƙaddara ta zo gifta maka babu yadda ka iya wajen kauce mata, amma na yi iya ƙoƙarina don baki tarbiya sannan ina komai naki kafin komai ya sauya"

Zalika ta ci gaba da kuka wiwi tana son yin wasa da hankalin Mamy, kallon ta Mamy ta yi tana rayawa a ranta cewa sai ta nunawa Zalika akwai bambanci tsakanin tunanin yaro da na babba.

Taku ɗaya biyu Mamy ta yi hannuqanra biyu suna goye a bayanta ta tsaya tarw da ɗaga kanta sama tana kallon silin hawaye suka wanke fuskarta masu matuƙar zafi, a hankali ta sauke kanta daga kallon saman silin ɗin ta juyo tana kallon Zalika da ita ma tuni nata idanun sun rine da saboda kukan da take yi don wasa da hankalin Mamy.

Ƙure ta da ido Mamy ta yi kamar mai tuna wani abu sai kuma ta fara magana cike da kaushin murya ta ce

"Zalika tun da har kin ƙi faɗa mini gaskiya kina wasa da hankalina zan yi abin da zai cire zargi da kokwanto a tsakanina da ke game da wannan maganar " Zalika ta ci gaba da yi wa Mamy kallon tsoro don ba ta san abin da za ta faɗa ba.

Mamy ta ce

"Zan duba ki Zalika, idan har kin taɓa sanin ɗa namiji ma daga na duba zan gane domin akwai bambanci da tazara mai tarin yawa tsakanin macen da ta taɓa sanin namiji da kuma wacce budurwa ce dal a led"
Zalika ta yi matuƙar razana da kalaman Mamy domin ta san an zo wajen da wayo da dabarar ta ba za su yi amfanin komai ba, matuƙar Mamy ta duba matantakar ta za ta san ta mu,amalanci namiji sai dai ta fara tunanin wace hanya za ta bi domin kaucewa wannan ƙudurin na Mamy shin Mamyn za ta yarda da wani wasa da hankalin kuwa anya?.

JIDDA

Zaman lafiya mai wanzar da nutsuwa suke yi tsakaninsu kasancewar ba ta mugun nufi ga kowa a rayuwa ahi ya sa ba ta taɓa kawowa cewa wani ɗan adam zai nufi rayuwarta da sharri, ɗan adam ɗinma wanda suka kasance na kisa da zuciyarta wato Aliya da kuma wacce take ganin ita ce ta maye mata gurbin uwa wanda ta rasa!. Sai dai kash rashin sani ya fi dare dunu domin zaton da take ba haka ba ne, saboda ta bar kashi ranar kwasa!.
Tun ran gini rana zane duk abin da bawa ya ƙaddara masa to sai ya faru da shi daɗi ko akasin haka, kyakkawa ko mummuna, wannan kaɗai ta saka a ranta take rayuwa hankali kwance ba tare da ta yi tunanin ta bar wani giɓi ba wanda ya kamata ta cike shi. Soyayya da ƙauna haɗe da kukawa da ba su da iyaka ko kuma hanyar misaltawa su ne abubuwan da ta yi amanna tana samun su daga Ibrahim sai dai ita ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba tana ba shi kulawa daidai gwargwado domin matsayjnta na matarsa iya ma abubuwa da dama da ya shafe sa aun rataya a wiyanta.

Daga Umma har Aliya babu wansa ya saduda ko kuma yin da na sani ko kuma zuciyarsu ta rusuna game da mugun ƙudurinsu a kan Jidda wacce ba ta taka ko ta zubar musu ba. Suna nan suna ta shiri a kan yadda za su samu kuɗin da za su tafi ga mataki na gaba domin sun ci alwashin sai sun cika mugun burinsu banu gudu babu ja da baya. Sun yi ta buga buga inda za su samu kuɗi abin ya fassakara hakan ya sa suka yi dogon nazarin ganin inda ya dace au sosa, saboda Umma ta ce kar su tamabayi Jidda ba lallai ne ta basu kuɗi ba yun da ita tana ganin ba za ta iya ɗakko musu daloli a kuɗin mijin nata ba.

Umma ce zaune tare da Aliya su biyu a gidan sun haÉ—a kai suna shirya yadda za su samu kuÉ—i Umma ta ce

"Aliya sai kin yj taka tsantsan wajen yin abin da ya dace, kin dii ga yatinyar nan mai mugun hali matsawar za mu jira sai mun samu daga wajenta to tabbas za mu ci gaba da dawwama a talauci tun da ita sahegen sanabe ya sa ta je tana riƙon amana ni ban ga amfanin ta ba"

Aliya cike da sheƙiyanci ta ce

"To Umma ko a danganta ta da barzahu?" Ta faÉ—a.cike da ingilanci

Umma tana zare ido ta aika mata saƙon harara ta ce

"Baki da hankali Aloya, ai maƙiyi ka bar shi yake ganin ci gabanka, sai baƙinciki ya so halaka shi, bare mu ai tuggunmu na gaba a kan Jidda shi ne wulaƙanci daman ɗan hakin da ka raina.. "

Alia ta ce

"Watarana shi zai tsokane maka idanu"

Jinjina mata Umma ta yi suka ci gaba da tsara komai Aliya ta ce

"Umma ko dai set guda za a sato?" Umma ta yi saurin dafe ƙirji tana dogon wiya alamar babu wanda yake jinsu ta sassauta murya ta ce

"Haba Aliya ke baki iya sirri ba yanzu idan akwai wani a laɓe ai shikenan ya gama jinmu, sai asirinmu ya tonu, sannan kuma idan kika je kika kwaso set ai ganewa za a yi kawai dai ki samu ko ɗan zobe ne ki ɗakko na san za mu samu biyan buƙata a iya zoben ma"

Murmushi Alia ta yi ta ce

"Shi ya sa nake son ki Umma ke mikiya ce mai hangen nesa"
Chapter 103 · 0% Book details